Alqur'ani ya bamu labarin cewa Alqiyamah zata tashi ne ba tare da tsammani ba. Wato zata zo ne "baghtatan". Alokacin da mutane suna cikin rafkanuwarsu ba tare da anyi musu shelar zuwanta ba. Zata tarar dasu kowa yana cikin sha'aninsa.
🔹Alqiyamah zata tashi ne abisa mafiya sharrin mutane adoron Qasa. Mutanen da basu san komai ba dangane da aikin gaskiya ko na imani. Kamar yadda Allah madaukakin Sarki ya riga ya hukunta cewar Alqiyamah ba zata tashi alhali aduniya akwai mumini ba.
🔸Bari dai zata tashi ne alokacin da zub da jini ya zama ba komai ba. Rayukan mutane da rayukan dabbobi sun zama kamar abu guda. 'Ya'ya zasu iya kashe iyayensu, ko kuma mutum ya kashe 'dansa ko 'dan uwansa ko abokinsa ba tare da jin komai aransa ba. Kuma babu abinda zai faru.
🔸Lokaci ne zai zo wanda Mataye zasu yi yawa aduniya. Sai ya zama adadinsu ya ninka na mazaje fiye da sau hamsin. Har sai ya kasance Namiji guda shi ke jibintar Mata guda hamsin (50) ko fiye da haka.
🔸Zina zata yawaita aduniya. Har sai ya zamanto an dena buya don yinta. Mutum zai yi zina da 'yarsa, yayi da Mahaifiyarsa, yayi da Qanwarsa ko yayarsa. Su zai mayar tamkar matansa har ya hayayyafa dasu.
🔸Har sai ya zamanto ana yin zina afili Qarara, agefen hanyoyi da tituna. Har sai ya zamanto anyi wasu shekaru masu yawa babu sauran 'Ya'yan halal aduniya sai dai 'ya'yan zina.
đź”»Mutanen zamanin, wasu irin mutane ne wadanda basu hana junansu aikata sa'bon Allah, kuma basu umurnin junansu da aikin alkhairi.
đź”»Shi yasa Manzon Allah (saww) yace "ALKIYAMAH BA ZATA TASHI BA, FACHE ABISA MAFIYA SHARRIN HALITTU".
Acikin wani hadisin kuma yace "ALKIYAMAH BA ZATA TASHI BA, HAR SAI YA ZAMANTO ADORON QASA BA'A CEWA "ALLAH! ALLAH!".
Acikin riwayar Imamu Ahmad kuma, "HAR SAI YA ZAMANTO ADORON QASA BABU MASU CEWA LA ILAHA ILLAL LAAH!".
Hadisai Ingantattu sun tabbatar da cewar Alqiyamah zata tashi alokacin wani mutum ya tatsi nonon rakumarsa, ya cira kwaryar kafin ya kai bakinsa sai Alqiyamah ta tashi.
Wasu mutanen kuwa suna tsakiyar cinikayya atsakaninsu, wannan ya saya wannan ya sayar masa.. Nan take sai Alqiyamah ta tashi. Wani kuma yana wanka acikin kududdufi kafin ya fito daga kududdufin Alqiyamah ta riskeshi ya mutu nan take.
Wasu kuma suna tsakiyar aikata "MA-SHA'A" alokacin da za'a busa Qahon tashin Alqiyamah. Haka zata riskesu su koma zuwa ga Sarkin Sarauta (SWT).
Watarana Manzon Allah (saww) ya fito sai Sahabbansa suka ga alamar kamar hankalinsa atashe. Da suka tambayeshi dalili sai yace musu :
"TA YAYA ZAN SAKI JIKI, ALHALI GA MA'ABOCIN QAHO NAN (WATO MALA'IKA ISRAFEEL) YA SANYA QAHONSA ACIKIN BAKINSA, YA SUNKUYAR DA GOSHINSA, YA YI SHURU DA KUNNENSA YANA JIRAN A UMURCESHI DA BUSAWA SAI YA BUSA".
Sai Sahabbai suka ce "To Ya Rasulallahi me zamu ce?"
Sai yace "Kuce HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKEEL. WA TAWAKKALNA 'ALAL LAHI RABBINA".
Allahu Akbar! 'Yan uwa kunji yadda al'amarin fa yake. Acikin wani hadisin kuma, Manzon Allah (saww) yace: "Hakika idanuwan Mala'ikan nan Ma'abocin Qaho abude suke tunda aka wakilta masa (wannan Qahon). Yana kallon wajen Al'arshi. Yana tsoron kar a umurceshi kafin ya kifta idanunsa. Idanuwansa tamkar wasu taurari ne masu haske guda biyu".
Muma Zauren Fiqhu mun ce HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKEEL. Ya Allah kasa mu cika da Imani. Allah ka kyautata karshenmu. Ameeen.
DAGA ZAUREN FIQHU

0 comments:
Post a Comment