Tambayoyi da amsa daga margayi Sheikh abubakar gumi (Rahimahullah) ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Friday 13 October 2017

Tambayoyi da amsa daga margayi Sheikh abubakar gumi (Rahimahullah)

41. TAMBAYA : – Idan mutum zai yi ramuwar sallar Asuba. Nafila zai fara yi ko farilla..?
AMSA : – Sallar farilla (Asuba) zai fara yi domin it ace wajibi ya rama ta, nan da nan. In kuma lokaci bai wuce ba, (ba a kai lokacin, zawal ba), yana iya rama RAKA’ATAINIL-FIJIR din da bai samu ya yi ba.
42. TAMBAYA : – Ko mai yin sallolin Nafiloli yana iya yin karatun FATIHA kawai, ga ko wacce Raka’a, ba tare da karatun sura ba? Kuma yin haka nan din ya isar masa.?
AMSA : – A’a karanta FATIHA kawai ba zai isar masa ba. Sai dai ya karanta FATIHA, sannan ya karanta sura, a inda ake karatun sura, in kuwa inda dama ba a yi ne (kamar RAKA’ATAINIL-FIJIR), shi ke nan.
43. TAMBAYA : – Muna son Mallam ya bayyana mana wurare goma sha daya (11), inda sallar Liman ke baci, amma ta Mabiya (MAMU) bat a baci ba.
AMSA : – To, matsaloli goma sha daya, inda sallar Liman ke baci amma ta mabiya ba ta baci ba, su ne:
Wuri na farko: idan Liman na cikin sallah (tare da Jama’a), sai HADISI ya kubce masa, watau ko ya yi RIHI (TUSA) : ko BAWALI (FITSARI) ya kubce masa; ko dai wani abu wanda zai warware Alwala; To, daga nan sai ya yanke sallar shi, ya jawo wani (daga cikin Mabiya; don ya ci gaba da sallar. To a nan sallar MABIYA na nan, amma ta shi (LIMAN) ta baci.
Wuri na biyu: Inda yake Limami ya yi sallah bai da Alwala, bai san bai da Alwala ba, sai bayan da ya kare sallar sannan ya tuna bai da Alwala. To, sallar shi, shi kadai t abaci, amma sallar MABIYAN shi na nan (ba ta baci ba).
Wuri na uku: Idan yana cikin sallah (tare da Jama’a) sai ya manta sallah yake yi, sai ya yi dariya, ko kuma dariyar ta rinjaye shi, har ya yi. To, a nan sallar shi kadai t abaci, amma na MABIYA, wadanda bas u yi dariyar ba, sallarsu na nan (ba ta baci ba). Sai su karasa, daga inda ya yi dariyar.
Wuri na hudu : Haka nan idan kana bin Limami, sai ka ga Najsa a jikin shi, ko ga tufafin shi (Liman din). To,daga lokacin da ka ga Najasar, sai ka kwace (ka bar bin Liman din). To, sallar shi (Liman) ta baci, domin kai ma ka dauki Najasar ken an, saboda haka kai ma sallarka ta baci. Domin wanda ya dauki Najasa, a cikin sallah, sallar shi t abaci. Saboda haka, abinda za ka yi shi ne ka wabce. In kuma kuna da yawa ne (wadanda suka ga Najasar) sai duk ku wabce, wani ya zama Khalifan Liman din, daga cikinku. Watau wani ya zamar maku Liman, a karashe sallar.
Wuri na biyar: – Watau ana cikin sallah sai suturar (watau kaya jikin Liman) Liman ta fadi. To, kai kuma mabiyi (MAMU), ba ka dubi al’aurar shi LIman ba. To, sallar shi (Liman) ta baci, shi kadai, amma kai sallarka na nan, sai ka ci gaba. Amma har in kai ma (MAMU), ka ga al’aurar Liman din, to kai ma sallarka ta baci. Domin wanda ya ga al’aaurar Limaminshi, sallar shi ta baci, saboda haka mai yin sallah da riga kawai (babu wando); idan ya duka wajen Ruku’u, har ya bari ya hango al’aurarshi, sallar shi t abaci watau in ya ga al’aurar shi, babu sallah.
Wuri na Shida : – Liman ya yi HOBO. To, abinda zai yi shi ne ya fita, ya sa wani cikin mabiyan ya ci gaba da yin sallar; shi kuwa ya fita, ya je ya wanke. In ya wanke sai ya zo ya zama mabiya (MAMU), (watau ken an ko da an tsere mishi da wasu raka’o’I zai dai iya dorawa a kan wadda ya riga ya yi kamin Habon ya same shi. Sai dai idan an gama sallar sai ya rama wadda bai samu ba, lokacin day a tafi wajen wanke jinin). To, cikin tafiya wajen wanke jinin, sai y ayi Magana da mantuwa, ko dai maganar da gangan; ko dai ya yi wani abinda ke bata sallah, to shi tashi sallar t abaci, amma ta mabiya (MAMU) ba ta baci ba.
Wuri na Bakwai : – Shi ne idan Liman ya manta, bai yi SUJADA guda daya (a wata Raka’a) ba, misali, ga Raka’ar farko sai Liman ya yi SUJADA daya, ya manata da dayar. To, a nan abinda za a yi masa, sai a ce
mishi “SUBHANALLAHI”, domin ya komo ga SUJADA ta biyun. In Liman ya ki (komawa don yin SUJADAR) yana tsammanin ya yi (ya cika). To, tunda su MABIYA ne, in suna jin tsoron kada ya mike har ya sake ruku’u ga raka’a ta biyu, sai su tashi su bi shi. Idan ya yi raka’a ta biyun, in ya zauna (shi Liman) sub a za su jira shi ba, domin kun san raka’a ta uku tare da su; to su (Mabiya), raka’a biyu ce a wajensu, amma shi (Liman) ta uku ce a wajen shi. Saboda haka shi ba zai zauna ba. Su ma (Mabiya) va za su zauna ba, (ko da yake wajen zaunawa ne, a wajensu); sai su bi shi. Idan ya yiwo raka’a ta hudu tare da su; to sub a za su zauna ba, (sai su sake mikewa; kamar dai raka’a ta biyar ce za su kawo); shi kuwa zai zauna, ya yi TAHIYA, ya yi sallama. Lokacin day a sallame, y ace ‘ASSLAMU ALAIKUM’, to su kuma sai su cika sallah, watau ku kawo raka’a dayan nan ta farko. To, idan sun yi haka nan, sallar shi (Liman) ta baci, amma tasu sallar ta yi kyau. Sannan su kuma (Mabiyan), idan sun kare sallah sai su yi KABLIYYA (sujada biyu, kamin sallama), domin Liman ya sa sun bar zaman farko, (zaman da ake yi bayan Raka’a biyu), domin an bar TAHIYA, da zaman TAHIYAR, da KABBARAR zaman (duk saboda rahsin yin zaman), shi ya sa za ku yi KABLI, saboda haka (a cikinsu, mabiyan) wanda ya manta bai yi KABLIYYA ba, said a ya sallame sallar, to in nan da nan ne ya tuna bai yi ba, sai ya yi BA’ADIYYA, (sujada biyu bayan sallama).
Wanda ya manta bai yi ba, har lokaci ya yi tsawo, to shi ma sallar shi ta baci . sai dai wata sabuwa. To, ga wannan kuma akwai wani KABLI (na fadar malamai) da ke cewa: Idan mabiyan, sun yi wa Liman ‘SUBUHANNALLAHI’, domin ya dawo ya yi sujadar ta biyu; amma ya ki dawowa, to a nan sai su mabiya su kyale Liman din, su yi sujadar, su kadai, sannan su yi sauri su tarar da Liman, tun bai gama karatu har ya yi ruku’u ba, a ci gaba da sallar da su, har a gama, a sallame da su baki daya. A nan (idan su yi haka nan), sallar Liman ta baci, amma tasu kuma ta yi kyau.
Wuri na Takwas : – Watau kamar KABLIYYA ta sunna UKU ta sami Liman tare da ku, zaman farko ba a yi ba, sia aka tashi. To, kun ga gun zaman, akwai kabbarar yin zaman, sannan akwai TAHIYA, da zaman TAHIYAR, sannan da kabbarar tashi daga zaman, (watau sunnoni hdu ma ke nan), to an yi kabbarar tshi, saboda haka an bar sunnoni uku ken an, ba a yi ba (an manta). To, in an manta, ba a yi wannan KABLIYYAR ba, har aka sallame sallar, to nan da nan in an tuna sai a yi BA’ADIYYA. In aka manta ba a yi BA’ADIYYA ba, har abu ya yi nisa, sallah ta baci ken an (gaba daya). To, amma idan Liman ne bai yi BA’ADIYYA ba, kai mabiyi, ka yi; to sallar Liman ta baci, amma kai taka sallar ba ta baci ba.
Wuri na Tara : – Shi ne wurin yaki, kun san Liman yak an raba Jama’a kashi biyu, ya fara rabin sallar da wasu mutane, sannan ya yi sauran sallar da sauran mutane. To, misali kamar a sallar Azuhur, ko sallar La’asar, kun ga in kamar sallar zaman gida ne, zai yi Raka’a biyu da Jama’a farko, sannan ya bar su, su cika sallarsu, su sallame su kadai, su tafi wajen yaki. Sannan wadancan masu yaki, su taho, su kabbarta a bayan shi (Liman); a yi ragowar Raka’a biyun tare da su. In ya sallame, su kuma su cika sallar, sannan su ma su sallame. To, bayan ya saki Jama’ar farko, (sun bi shi ga yin Raka’a biyu na farko, sun cika, sun sallame, sun tafi). To, wadannan bangaren Jama’a na biyu, sun zo, ko bas u zo ba idan wani abinda ke bata sallah, ya sami kwacewar tusa, ko yin dariya; to su wadancan na farkon, abin bai shafe sub a. watau dai sallar su ta yi dai-dai, amma ta Liman ta baci.
Wuri na Goma : – Liman ne a cikin kuskure, kamar a cikin duhu, sai ya kaucewa Alkibla (Gabas); kamar ya dubu Arewa; su kuma mabiya suna fuskantar dai-dai Alkiblar (watau Gabas). Watau ke nan, shi Liman yana fuskantar Arewa (da kuskure), su kuwa suna fuskantar Gabas (Alkibla). Sai bayan da aka gama sallah, sai aka gane Liman bai fuskanci Alkibla ba, to, a nan shi (Liman), shi kadai n eke da laifi. Saboda haka sallarsu (mabiya) na nan, amma ta Liman kuwa, ta baci, sai ya sake tashi, shi kadai.
Wuri na Goma Sha Daya : – To, idan sallar Liman t abaci, saboda wani dalili, yak an jawo wani, ya sanya shi Khalifan shi (madadin shi), wanda zai ci gaba da jagorancin sallar. To, shi kuma wannan Liman din (wanda aka jawo aka sanya), sharadi ne, sai ya yi niyyar yin Limanci. In bai yi niyyar yhin Limancin ba, sannan kuma ya ja mutane haka nan, ba tare day a yi nityyar ba, to, shi kadai bai da sallah, amma wadanda suka bi shi (watau mabiya), su sallarsu na nan. To, wadannan sun e wurare goma sha daya, a inda sallar Liman ke baci, amma ta mabiya ba t abaci ba. Amma kuma, sharadin wannanhukunci duk sai ya zamo ga sallolin da haduwar mutane domin yin su, ba sharadi ban e. misali, in ga sallar Juma’a ne, dayan wadannan abubuwan ya abku, har sallar Liman ta baci, to, ta mabiya ma ta baci. Haka nan ga sallar LAILATUL MADRI (domin duk akwai sharadin taruwar). A nan ma idan sallar Liman ta baci, sallar mabiya ma ta baci. Haka nan ma ga sallar tsoro, (watau dai duk, sallolin da suke da sharadin taruwa a yi su); idan sallar Liman ta baci, to, ta Mamu (mabiya) ma ta baci. Amma ga sauran salloli, wadanda ba sharadi ba ne, sai an taru : kamar sallar Azuhur, La’asar, Magariba, da dai sauransu. To, su wadannan ana amfani da wannan hukuncin.
KASARU
44. TAMBAYA : – Kwana nawa aka kayyade wa mai yin KASARU, cewar ya yi KASARU?
AMSA : – A’a babu wani kayyadin lokacin, sai dai cewa aka yi idan ya je wani gari; y ace “Zan tsaya a nan, in yi kwana hudu,” to, sallar shi ta KASARU ta yanke daga wannan tunanin da ya yi.
45. TAMBAYA : – Wai wannan yana tambayar; ko ana yin Kasaru ga sallar shafa’I da wutri?
AMSA : – A’a watau sai ga sallar farilla kawai; kuma ko a sallar farillar, sai mai raka’a hudu (4) kawai.
46. TAMBAYA : – Mutum ne ya yi tafiya; amma bai sami yin salloli ba, zai yi niyyar kasaru ne?
AMSA : – Sai ya rama su (sallolin) kamar kasaru; domin duk sallah, yadda mutum ya bar ta haka zai rama ta. In ta kasaru ce, sai a rama ta a kasaru; in ta zaman gida ce (ko da mutum na cikin tafiya ne) sai ya rama ta a irin ta zaman gida.
47. TAMBAYA : – Wannan yana tambayar cewar; yana tafiya a cikin Jirgin Sama har sallar Azuhur, da sallar La’asar da sallar Magariba suka same shi; bai sami dammar yinsu ba. To, sai ya isa da Isha’i. in zai rama sallolin, yaya zai yi? Watau zai yi KASARU ne ko kuwa zai cika sallar?
AMSA : – To, zai rama sallolin Azuhur da La’asar akan sallolin KASARU, domin ana yi musu KASARU, sannan kuma lokacinsu ya fita (domin an shiga lokacin sallar Isha’i). amma sallar Magariba; ko da yake lokacinta bai fita ba, dama salloli, wadanda suka kubce mishi, kuma su masu Raka’a hudu ne, to in lokacinsu ya fita, zai rama su a kan KASARU, yadda suke a lokacin yinsu.
JUMA’A
48. TAMBAYA : – Ina son Malam ya fahimtar da ni game da zaman da Liman kan yi cikin Hudubar Juma’a.
AMSA : – Wannan mustahabbi ne, ko kuma Sunna ne. watau in Liman ya yi huduba ta farko, ya zauna. Watau, kamin Liman ya fara Huduba sai ya dan zauna, don mutane su natsu. Sannan in ya yi Huduba ta farko, ya zauna don a sami bambanci tsakanin Hudba ta farko, da ta biyu. Ana son kuma lokacin da Liman ya zauna mutane su yi addu’a don ana fatan amsar addu’a a wannan lokacin.
49. TAMBAYA : – Ko mai ya sa ba a fassara Huduba ta ranar Juma’a (da Harshen Hausa); saboda mutane su fahimta?
AMSA : – To, yana yiwuwa a nan gaba in Allah ya so a fassara. Domin sharadin dai a yi Huduba? A yi da harshen Larabci. Abinda ya sa; domin kowanne masallaci na duniya ne gaba daya, ban a mutum guda ba; watau kun gad a Larabawa, da Turawa, da kowane irin yare; dam un zamo a masallaci guda, a wuri daya, duk namu ne masallacin. To, in ya zam Jam’iyya irin ta Musulunci, wadda ta tara mutane na duniya daban-daban, tilas ne kowa ya koye shi. To wane harshe ne ya kamata a rike? Shi ne harshen Kur’ani, watau Larabci. Saboda haka, tilas ne a yi HUDUBA da harshen Larabci. Bayan haka nan, yana yiwuwa ga Liman, bayan y agama Huduba, kamin ya kabbara sallah; domin lokacin nan ba a hana Magana bay a fassara wa mutane abinda ya ce. Ko kuma karanci, ya fada wa mutane cewar, ya ce, “Abu kaza da kaza”.
50. TAMBAYA : – Shin wai wankan da na yi a ranar Juma’a ya isar mani; ko kuwa sai na sake wani idan zan je masallaci?
AMSA : – To, ya danganta ga ra’ayin da ka bi. Idan ka bi ra’ayin Ashhab (mai cewar ana yin wankan ne domin ranar Juma’ar) to, shi ken an wankan da ka yi ya isar maka. Kuma kana iya yin wankan ko yaushe, matukar dai Alfijir na ranar Juma’ar ya fito. Sannan kuma kana iya dukkan aiyukan da kake son yi bayan ka yi wankan, ko da Jima’I ka yi da matarka, sai dai ka sake wankan Janaba kawai. Amma kuma in ka bi daya ra’ayin na IBN KASIM, mai cewar ana yin wankan ne don sallar Juma’a; to tilas ne da ka gama wankan, ka nufi masallci; don sallar Juma’ar, ko tsayawa ka yi, ka ci abinci, ko ka yi barci, sai ka sake wankan. Ga wannan ra’ayin kuma, sai wanda zuwa sallar Juma’ar take wajibi a kanshi, kuma za shi tafiyar din, sannan zai yi wankan. Amma ga wancan ra’ayin (na yin wankan saboda ranar), ba sai wanda ya zamo wajibi ya je sallar ba, zai iya yi. Saboda haka kamar matan aure, da bayi da yara, da matafiyi; duk suna yin wankan Juma’a domin ana yinsa ne domin ranar Juma’a kamar ranar Idi, ba domin sallah ba.
JANA’IZA
51. TAMBAYA : – Ko ana saw a kabari sumunti?
AMSA : – A’a laka kadai ake iya kwabawa a sanya, domin kada kasa ta rufe shi. Amma sanya sumunti makarufi ne. sannan kuma, sanya itatuwa, ya fi sanya tukwane. Domin sanya tukwane zai hana wata rana a sanya wani a wurin saboda za a yi ta ganin kushewar kabarin, na da, domin tukunya bat a lalacewa. Amma itace na da saurin rubewa, ya lalace (ya bace fiye da sauri) akan tukunya.
52. TAMBAYA : – Ko ya halatta idan wani mutum ya mutu, a rubuta wani abu na Kur’ani ko Hadisi, a rataya masa?
AMSA : – Ba dai-dai ba ne, domin yana kai ga a sanya Kur’ani a cikin Najasa. Domin kasusuwan mamaci a cikin kabari Najasa ne. Koda yake akwai wasu Malamai da ke cewar “Musulmi bai zama Najasa”, amma dai rashin yi ya fi. Bai dai halatta ba, a takaice.
53. TAMBAYA : – Wannan yana tambayar cewar: Limaminsu ya zo yi wa wani yaro dan kwana uku da haihuwa Jana’iza, (Bayan yaron ya rasu); sai ya rike shi a hannu; lokacin da ake yi masa sallar (Jana’iza). Yin haka ba komai? Ko kuwa dole sai an aje shi a kasa?
AMSA : – A’a Ajiyewa ake yi a kasa, ba cewa ake I a rinka rikewa a hannu ba. Watau ajiye shi ake yi a kasa kamar kowa; matukar dai ya yi kuka lokacin da aka haife shi. Watau bai fado matacce ba. Haka nan za a yi masa wanka da Likkafani.
54. TAMBAYA : – Ina hukncin wanda ya hana a wuce da Gawa ta kofar gidansa; alhali kuwa shi makwabcin makabarta ne?
AMSA : – To, wannan bay a da hankali. Yana da ikon ya ce, “Ba a bi ta kofar gidana.” Amma kuma abin da ake biyowa da ita nan (watau Gawar), ya kamata ya yi tawali’u idan ya gan ta.
55. TAMBAYA : – An ce: wankan Gawa, iri uku ne, yaya suke?
AMSA : – Ni dai wanka iri daya na sani, shi ne ana wanke gawa kamar yadda ake wankan JANABA. Sai dai ana son a bar shi kwance, ya fi a zaunar da shi wajen wankan. Amma kuma in mai tambayar, yana nufin a yi wankan (a maimaita) har sau uku, to wannan ana yin haka nan. To, amma kuma wannan ai duk dai wankan iri daya ne; sai dai an maimaita shi har sau uku kawai. Amma in an ce “Iri uku”, ai ya zama daban-daban ken an. To, said a kuma, ko ga wannan inda bambancin yake (idan za a maimaita wankan har sau uku din), a wajen wankan karshe, ana son a sa Magarya da itace Kafur. Domin yin haka na sanya jiki ya yi karfi.
56. TAMBAYA : – To, Allah ya gafarta Malam; yaya hukuncin bayan an gina masallaci a dauki mutum (Mamaci) a binne shi a ciki? Kamar yadda aka yi wa Abdul-Nasir (na kasar Masar)?
AMSA : – To, yin haka nan bay a da kyau. Sai a kai shi (Mamacin), wajen da ake binne sauran musulmi. Amma ba a binne mutane a cikin masallaci. Ga Mas’habar Malik ma, ko a ce a dauko mamaci, a kawo shi cikin masallaci domin a yi mishi sallah ba a yi; balle ma a ce a shigo da shi a binne a ciki. Watau kabarin ma Annabi (S.A.W.)da ke cikin masallcin Madina; ainihinsa ba cikin masallacin yake ba; masallacin ne ya yi fadi, har ya kai ga inda yake.
57. TAMBAYA : – Tambayar da ake yi cikin KABARI, har kafurai da wadanda suka gabaci wannan al’ummar ana yi musu ita?
AMSA : – To, ya dai taho cewar wannan al’ummar (Al’umar Annabi Muhammadu (S.A.W.), ana yi musu wannan tambaya ta kabari. Sannan an yi kilafar, ko sauran al’umma ana yi musu, ko kuwa ba a yi musu? Abinda dai aka rinjayar bisa ga wannan matsala (ga mafi yawan malamai) shi ne ana yi musu.
58. TAMBAYA : – Wadansu malamai sun ce idan mutum ya mutu ana sake mayar da ranshi a Kabari, domin a yi masa tambayoyi. Wadansu kuma sun ce za a bar mutum cikin KABARIN ne har sai Ranar Tashin Kiyama; sannan a tayar da shi domin yi masa tambayoyi. To, wai yaya al’amarin yake?
AMSA : – To, wadannan maganganu da suka fada, duka haka ne. watau daga ran da mutum ya mutu, ya shiga BARZAHU kenan har ranar da za a tayar da shi, ranar kiyama. Wannan zama, duk zaman BARZAHU ken an. Watau shamaki tsakanin Duniya da Lahira. Kuma wannan shi ne zaman KABARI. Kuma ana mayar wa mutum da ran shi lokacin da aka sanya shi a KABARIN; har ma ana cewa, yana jin saurin tafiyar wadanda suka binne shi; lokacin da suke komowa. Watau wanda Allah ya sa zai amsa wadannan tambayoyi da sauki; zai ce “Allah ne Ubangiji na; Annabi Muhammadu (S.A.W.) Manzon Allah ne, kuma Alkur’ani shi ne littafi na”. Bayan haka sai a ce masa, “Ka yi barci, babu jin tsoro”. To, kun ga watau jikinsa zai zauna a nan cikin bacci. Amma duk da haka ranshi, za a buda daga Kabarinsa a sa hanya tsakanin kabarinsa da Aljanna in da zai zauna. Saboda haka ran shi yana nan a cikin Ni’ima har randa tashin kiyama ya taho. In ya zamo ma cikin SHUHADA (wadanda suka mutu wajen Jihadi) ne, ba a ko barinsa, sai a sanya shi a HAYATULIL DHURAH a rataye shi a karkashin Al’arshi.
NAFILOLI
59. TAMBAYA : – Game da yin Raka’ainil Fijir; wasu sun ce, “Fatiha kawai ake karantawa; ban da sura” yaya hukuncin yake?
AMSA : – To, ga asalin kilafar (ka san Malamai, kullum dubi suke yi ga abinda aka Ruwaito daga Annabi (S.A.W.); kowa ya fadi abinda ya fahimta gwargwadon fahimtarshi). Aisha (RTA) ta ce, “Na ga Annabi (S.A.W.) na yin Raka’atainil Fijir da sauri kamar bai karanta sura ba.” Wannan Magana da ta yi, ita ce aka yi wa fassara. Wasu sun ce, “Tun da akwai wani Hadisin da ke cewar, “Babu sallar dab a a karanta Fatiha ba’ to ash eke nan karancin karatun day a yi, shi ne Fatiha.” Saboda haka a tsaye ga Fatiha dai. Wani ya ce “A’a ana karanta sura (bayan Fatiha); domin akwai wani Hadisi wanda yake cewa; wanda ya karanta KULYA AYYUHAL KAFIRUN da KULHUWALLAHU cikin sallar Rka’aitainil Fijir, ba zai yi ciwon hakora ba.’ Wannan ya nuna ana aza sura’. Wanda duk mutum ya dauka, dai-dai ne.
60. TAMBAYA : – Nafilar da ake yi bayan sallar Magariba; shin karatunta a asirce ne? ko a bayyane ne?
AMSA : – A bayyane ake yi, sai dai mutane in a cikin masallaci suke don kada wani ya rinka yi wa wani a bayyane (yan saurare), sai a yi a asirce.
Allah Ya Kara Fahimtar Damu ameen…..
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support