SU WAYE FIQAHA'US SAHABAH?
********************************
Wasu Sahabbai ne manya wadanda suka shahara a fagen ilimi da fahimtar addini. Kuma mafiya yawansu sun dauki zamani mai tsawo suna tare da Manzon Allah (saww).
Masu kokari ne wajen Ilmantarwa da karantarwa tun azamanin Manzon Allah (saww) da kuma bayansa. Wadanda daga irin fatawoyinsu ne aka gina fahimtoci na manyan Mazhabobin nan na Maluman Fiqhu.
Mafiya shahara daga cikin Fiqaha'us Sahabah sun hada da :
- Sayyiduna Abubakrin bn Abi Quhafah (Assiddeeq).
- Sayyiduna Umar bn Al-Khattab (Al Faruq).
- Sayyiduna Uthman bn Affan (Dhun Nurayn).
- Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib (Abul Hasanaini).
- Abdullahi bn Mas'ud.
- Zaidu bn Thabit.
- Abu Musal Ash'ariy.
- Mu'az bn Jabal.
- Ubayyu bn Ka'ab.
- Abud Darda'i.
Sai kuma Ummul Mumineen, Nana A'ishah bintu Abibakrin (Allah shi yarda dasu baki dayansu).
Sannan acikin kashi na biyu kuma akwai wadanda ake kira "AL- ABADALAH". Wato dukkansu sunayensu Abdullahi ne. Kuma dukkansu 'ya'yan Sahabbai ne kuma sun riski lokacin rayuwar Manzon Allah (saww). Kuma sun tattaro Ilimai masu yawa wadanda kusan sun shiga kowanne fanni na ilimin addini. Gasu nan kamar haka :
- Abdullahi bn Abbas.
- Abdullahi bn Umar.
- Abdullahi bn Zubayr bn Awwam.
- Abdullahi bn Amru bn Al-As.
Allah shi yarda dasu baki dayansu.
Dukkansu baki daya kowanne yana da manyan abubuwan da ya kebantu dasu na falala da fifiko acikin sauran Sahabbai.
Muhammad 'dan Sahlu dan Abu Khaysamah ya karbo daga Babansa yana cewa :
"Wadanda suka kasance suna bayar da fatawa azamanin Manzon Allah (saww) mutum uku ne daga Muhajirun, uku kuma daga mutanen Madeenah.
Umar da Uthman da Aliyu da Ubayyu bn Ka'ab da Mu'azu bn Jabal da Zaidu bn Thabit. Shi kuwa Abdullahi bn Abbas ya kasance idan an tambayeshi game da wani abu, in dai babu acikkn littafin Allah da Sunnar Annabinsa (saww) to yana yin furuci ne da Qaulin Abubakar (ra) idan kuma babu to yakan yi fatawa da maganar Umar (Allah shi yarda dasu baki dayansu. Ameen.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (17/10/2017 27-01-1439).

0 comments:
Post a Comment