Ba'a Barin Ingantaccen Hadithi Saboda Ya Sabawa Wata Nazhaba Dr Ibrahim Jalo Jalingo ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Tuesday 17 October 2017

Ba'a Barin Ingantaccen Hadithi Saboda Ya Sabawa Wata Nazhaba Dr Ibrahim Jalo Jalingo


1. Matafiyar Annabi mai tsira da amincin Allah ita ce sama da dukkan wata matafiya (mazhaba), sannan fiqhunsa  shi ne sama da dukkan wani fiqhu.

2. Bin mazhabar (matafiyar) wani malami daga cikin Malaman Musulunci ba laifi ba ne matukar dai hakan bai kai mutum ga barin yin aiki da wani ingantaccen hadithin manzon Allah mai tsira da amincin Allah ba, in kuma ya kai shi ga barin yin aiki da wani ingantaccen nassin hadithin Annabi to lalle hakan ya haramta a bisa ittifakin dukkan Magabata na kwarai; saboda Annabi Muhammadu ne kawai Allah Ya aiko wa wannan Al'umma, duk kuma wani wanda ba shi ba to mabiyi yake a gare shi, kuma maganarsa shi Annabi Muhammadu tana sama da maganarsa.

3. To amma in aka sami wata mas'ala da babu nassin Annabi mai tsira da amincin Allah a kanta to a nan dukkan wani malami mai ikon yin ijtihadi sai ya yi ijtihadinsa  kuma duk hukuncin da ya samu kaiwa gare shi cikin ijtihadin nasa to da shi ne zai bauta wa Allah Ubangijinsa. Sannan kuma shi aammiy mara ikon yin ijtihadin Ilmi sai ya yi koyi da wanda zuciyarsa ta fi kwanciya da shi cikin mujtahidan da suka yi ijtihadin Ilmi a cikin wannan mas'ala wacce babu ingantaccen nassin Manzon Allah mai tsira da amincin Allah a cikinta.

4. Ke nan wajibi ne a kan ko wane musulmi ya gina addininsa a kan sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah; saboda duk wanda ya bar yin aiki da ingantaccen hadithin Annabi mai tsira da amincin Allah cikin wata mas'ala daga cikin mas'aloli kuma cikin zabinsa da jin dadinsa a bisa hujjar cewa: mazhabarsa ta saba wa hadithin, ko wata darika tasa ta Sufaye ta saba wa hadithin, ko wani tsari na kungiyarsa ya saba wa hadithin, ko wani tsari na duniyarsa ya saba wa hadithin to lalle wannan ya bace ya bar hanyar Muminai, ya bar fikhun Sahabbai da Tabi'ai da Tabi'ut Tabi'in, Wannan shi ne abin da nassoshin Alkur'ani mai girma da Sunnah mai daraja ke tabbatarwa. Shaikhul Islam Ibnu Taimiyah ya ce cikin Majmuu'ul Fataawaa 24/202:-
((واما من تبينت له السنة فظن ان غيرها خير منها فهو ضال مبتدع بل كافر)).
Ma'ana: ((Amma wannan da Sunnah ta bayyana gare shi, sannan ya yi zaton cewa waninta ya fi ta alheri, to shi dan'bidi'ah ne, kai kafiri ne ma)).
Ya kuma ce cikin littafin 27/125:-
((ومن ترك النقل المصدق عن القائل المعصوم واتبع نقلا غير مصدق عن قائل غير معصوم فقد ضل ضلالا بعيدا)).
Ma'ana: ((Wanda ya bar nakalin da aka gaskata daga mai fada wanda yake ma'asuu'mi, sannan ya bi nakalin da ba a gaskata ba daga mai fadan da ba ma'asuu'mi ba, hakika ya bace bata mai nisa)).

Allah Ya taimake mu Ya dora mu a kan daidai har kullum. Ameen.
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support