Shin mecece mutuwa ?? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Thursday, 5 October 2017

Shin mecece mutuwa ??

SHIN MECECE MUTUWA? (01)
******************************
Mutuwa ita ce rabuwar ruhi da jiki. Wato da zarar ruhinka ya fita daga jikinka to ka mutu kenan. Mutuwa ita ce fitarka daga wani halin zuwa ga wani.. Kuma ita ce fita daga wannan gidan (duniya) zuwa ga wani gidan (lahira).

Allah da kansa yace Mutuwa Musibah ce.. Acikin littafinsa mai girma inda yake cewa :

"IDAN KUNA TAFIYA A DORON QASA SAI MUSIBAR MUTUWA TA SAMEKU...".

Hakika lallai mutuwa Musibah ce. Amma musibar da tafi ta girma ita ce : GAFALA (WATO RAFKANA) DAGA BARIN AMBATONTA..  Wato Mantawa da tunanin mutuwar. Da kuma rashin yin kyakkyawan tanadin guzuri saboda ranar zuwanta.

Hakika guzuri ya kamaci mai tafiya. Shi yasa Annabinmu (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya wa'azantar damu da irin wa'azin nan mai saurin tsinka zukata, Mai sanya mutum yayi ma kansa hisabi. Kuma yace : "KU YAWAITA AMBATON MAI YANKE JIN-DADI". WATO MUTUWA.

Mutuwa tana zuwa ne babu zato babu tsammani (Bagtatan). Dani mai rubutun, da ku masu karatun nan babu wanda yasan yaushe zai, mutu ? A wanne waje zai, mutu? Da yaya zai mutu?  Kuma menene ajalinsa?.

Wannan ita ce babbar tambayar da bata da amsa.. Kuma babu wani daga cikin mutane wanda ya santa balle ya gaya maka.. Shima bai san tasa ba, balle yasan ta wani.


Allah yana cewa : "ALLAH AWAJENSA NE SANIN ALQIYAMAH YAKE, KUMA SHI KE SAUKAR DA GIZA-GIZAI KUMA YASAN ABINDA KE CIKIN MAHAIFA.

"BABU WATA RAI WACCE TASAN ABINDA ZATA TSUWURWURTA GOBE, KUMA BABU WATA RAI DA TASAN AWACCE QASA NE ZATA MUTU".

Hakika mantuwa ko rafkanuwa daga tunanin Mutuwa da 'dacin nan nata, da Kwanciyar Qabari da duhun nan nasa, Da tambayoyin nan na Mala'iku da tsananinta, da ranar Alqiyamah da Tashin hankalin nan nata, da hawan siradi da kaifin nan nasa, Mantuwa daga ambato ko tunanin wadannan yakan sanya zuciya ta bushe har ma alfasha da 'barna su bayyana acikin doron Qasa da teku..

Kai sani cewar idan kai mai tuna mutuwa ne, to zaka kasance mai tanadin guzuri domin zuwanta..

Shin yaya sallarka take? Shin kana yinta akan lokacinta, tare da Ikhlasi da tsoron Allah? Shin kana da ilimin sanin tsarki da alwala da hukunce-hukuncen Salla?. In baka dashi mai ya hanaka ka nema?? -- Neman duniya ko?

Yaya azuminka yake? Shin kana tsaftace idanunka da harshenka ayayin da kake azumi? Shin kana kiyayesu daga kallon haramun, ko furta kalmomon haramun? Ko tunanin aikata sa'bon Allah??.

Shin yaya bin iyayenka yake? Shin kana basu hakkinsu kamar yadda ya dace? Baka 'bata musu rai, baka yi musu tairin kai da girman kai? Shin baka fifita matarka ko abokanka akansu?.

Yaya sadar da zumuncinka yake? Shin kana hakuri da wautar 'yan uwanka? Shin kana basu hakkinsu? Kana kyautata musu? Kana ziyartarsu?. Ko ko ka biye ma zuciya kana rama mugunta da mugunta?.

Yaya Mu'amalarka da mutane take? Shin kana sakin fuska ga dukkan Musulmai? Shin kana girmama kowa, kana zaman lafiya da kowa? Shin kana kwatanta adalci da gaskiya da rikon amana acikin kowacce harka ta cikin gidanka da wajen aikinka ko kasuwarka?.

Yaya dukiyarka take? Yaya abincinka da abin shanka yake? Ka tabbatar kan cin halal dinka kana kiyayewa daga haram?.

Idan akwai matsala yi kokari ka gyara.. Domin mutuwa tana daf da kai.. Mala'ikan mutuwa kullum yana shafa kanka sau saba'in.. Zai iya chafke ruhinka duk sanda aka umurceshi..

NASIHA CE DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 {04/10/2017  14/01/1439}.


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support