Hanyoyin samun shiga Aljannah ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Thursday, 5 October 2017

Hanyoyin samun shiga Aljannah

HANYOYIN SAMUN SHIGA ALJANNAH (78)

KIYAYE GABOBI BIYU
*********************
Hadeethi daga Abdurrahman dan Thawbanu (rta) daga Sayyiduna Abu Hurairah (ra) daga Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) yace :

"WANDA YA KIYAYE ABINDA KE TSAKANIN GEMUNSA GUDA BIYU {WATO HARSHE} DA KUMA ABINDA KE TSAKANIN QAFAFUNSA (WATO AL'AURA) ZAI SHIGA ALJANNAH".

Imamul Hakim ne ya ruwaito hadisin acikin Mustadrak juzu'i na 4 shafi na 397 kuma ya inganta isnadinsa.

BAYANI
********
Kiyaye harshe ba abu ne sassauka ba. Kasancewarsa gaba mafi yawan motsawa ajikin Bil Adama alhali kuma shine mafi hatsari.

Wajibi ne mutum ya kiyaye harshensa daga zagin musulmi ko aibantasu ko cin zarafinsu ko yin Qarya, gulma, annamimanci, batsa, da sauransu.

KIYAYE AL'AURA: Wajibi ne mutum ya kiyaye al'aurarsa daga zina madigo, luwadi,da sauransu.

Wannan ya ha'da har da Istimna'i (Masturbation) kasancewar mafiya rinjayen Malamai sun tafi akan haramcinsa, ga kuma chutarwa jiki da zuciya da yakeyi.

Allah yasa mu dace da samun rahamarsa da yardarsa ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU (29-09-2017 08/01/4439).



Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support