*HUKUNCIN MIKEWA MALAMI KO SHUGABA DON GIRMAMAWA*
*Tambaya :*
Assalamau alaikum Malam. Ina teaching practice ne yanzu, kuma idan na je aji yara suna mikewa damin gaishe ni, mal. na barsu su cigaba ko na dakatar da su ?
*Amsa :*
Wa alaikum assalam To dan'uwa akwai malaman da suka ta fi akan cewa makaruhi ne a mikewa malami, akwai kuma wadanda suka haramta, akwai wadanda kuma suka halatta.
Saidai maganar da ta fi ita ce bai hallata malami ya nemi a mike masa ba, saboda fadin Annabi s.a.w. " Duk wanda ya so mutane su mike masa to ya tanaji wurin zamansa a wuta" kamar yadda tirmizi ya rawaito shi kuma ya kyautata shi a hadisi mai lamba ta : 2755, Albani kuma ya inganta shi a silsilatussahihah lamba ta : 5957.
Amma idan aka mikewa malami ba tare da ya nema ba, to wannan babu laifi ga wanda ya mike da wanda aka mike saboda shi, domin ya zo a hadisi cewa : Annabi s.a.w. ya nemi mutanen Madina su mikewa Sa'ad, lokacin da ya gabato" kamar yadda Bukari ya rawaito a hadisi mai lamba ta :2878, wannan sai yake nuna halaccin mikewa ga mutane masu falala kamar malamai da manyan mutane, lokacin da suka gabato .
Don neman karin bayani, duba : Alminhaj na Nawawy 12/440, da Mirkataul mafaatiih sharhu mishkatil-masaabiih shafi na : 2972 BABU ALKIYAM . .
Allah ne mafi sani
*Amsawa*✍🏻
*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
24\11\2014
Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*
Shiga nan
www.duniyarfatawa.com.ng

0 comments:
Post a Comment