Jinin haila:Abubuwanda da suka halatta ga mace a lokacin da take jinin haila! ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Tuesday, 10 October 2017

Jinin haila:Abubuwanda da suka halatta ga mace a lokacin da take jinin haila!

HUKUNCE-HUKUNCEN JININ HAILA
***************009*******************
ABUBUWAN DA SUKA HALATTA GA MACE A LOKACIN DA TAKE JININ HAILA!
***************************************
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu mai rahama mai jin qai, tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Swallallahu-Alayhi-Wasallam da ahlin gidansa yardaddun Allah da wadanda suka biyo bayan su da kyautata wa har yazuwa ranar sakamako, 'yan uwa da ikon Allah ta'ala yau ga bayanin mu da mukace zamuyi maku akan wadansu abubuwa da suka halatta ga mace mai jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) ta aikata su da kuma tabbatar da cewa acikin LittĂŁfin Allah babu inda ya hanasu su aikata, haka kuma acikin littafan musulunci (Hadisai) babu inda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya hanasu cewa kada su aikata, kuma da yardan Allah zamu takaita rubutun bazamu tsawaita shi ba, Allah ta'ala yayi mana jagoranci,
.
1:-  YA HALATTA (Mace mai jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) ko kuma mace mai janaba ko namiji mai janaba, matar aure ko budurwa, Mai mata ko gwauro, ta hanyar Jima'ei ko kuma mafarki, kakaf dinsu ya halatta su dauki Al-Qur'ani da hannuwan su kuma su karanta Al-Qur'ani din matukar bukatar hakan ya taso, inaso kusani acikin LittĂŁfin Allah (Al-Qur'ani) ko kuma Hadisi kakaf babu inda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ko kuma Allah ta'ala ya hana mace ko namiji don Suna acikin wannan halin cewa wai kada su dauki Al-Qur'ani, Wallahi ina yi maku rantsuwa da Allah babu wannan wajen, ya halatta kiji na sanar dake da kuma kai wanda kake da janaba ajikin ka ku karkad'e kunnuwan ku kuji ya halatta ku dauki Al-Qur'ani ku karanta matukar bukatar hakan ya taso, domin babu inda akace kada ku dauka, don haka  'yan uwa kusani wannan tilawar Al-Qur'ani din babu hani akan sa, (Asha karatu lafiya 'yan uwa na),
.
Hadisi ya tabbata acikin Sahihu Muslim Daga Ummuna Aysha Allah ya kara mata yarda tace,  "Lallai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kasance yana ambaton Allah a kowwane hali" ( Duba Fiqhul-Muyassir shafi na 56)          ..  Imam Muhammad Nasirud-Deen Al-Albany Rahimahullah yace  "Acikin wannan hadisin akwai halaccin karanta Al-Qur'ani ga mai Janaba, domin kuwa lallai karatun Al-Qur'ani zikiri ne (ambato) kenan zai shiga acikin maganar ta cewa (Yana ambaton Allah) (Duba Fiqhul-Muyassir shafin da mukayi ishara dazu)      ...    Amma abinda yafi shine mutum ya  karanta Al-Qur'ani acikin tsarki, wato ya karanta shi yana tsarki domin kuwa ya tabbata acikin Hadisi na Sunan Abiy-Dawuda a lõkacin da akayi wa Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi sallamah, to a lõkacin bashi da tsarki sai yayi taimama sannan ya amsa, daga nan yace  "Lallai ni an karhanta min ambaton Allah, sai dai idan ina da tsarki"   (Ku nemi wannan hadisin acikin Sahih Sunan Abiy-Dawuda mujalladi na farko shafi na 763, ko kuma a Duba Fiqhul-Muyassir shafin da mukayi ishara dazu)
.
Sheikh Swalihul-Othaymeen Allah ta'ala yayi masa rahama yace  "Babu wani hani ga mace wacce take jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) su dauki Al-Qur'ani su karanta idan bukatar haka ya taso kamar matar ta kasance malama ce (mai koyar da karatu acikin makaranta ya halatta ta dauki Al-Qur'ani ta karantar dasu) ko kuma Daliba ce (Wacce take zuwa makaranta koyon karatu ya halatta ta dauki Al-Qur'ani taje makaranta a koyar da ita) ko kuma wadanda suke zaune acikin gida (Gashi kuma suna yin jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) to ya halatta su dauki Al-Qur'ani suyi tilawa idan suka bukaci hakan"   (Wannan fataawa ta Swalihul-Othaymeen Rahimahullah tana acikin littafin fatawoyin sa mai suna  *SU'ALAN-AN-AHKAAMUL-HAIDH* fatawa ta 52 shafi na 16)
.
2:-   YA HALATTA (Mace tabi duk hanyar da zatabi ta biya wa mijin ta bukata alhali tana yin jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) amma dai banda saduwa wato banda kwanciyar aure kamar yanda bayani ya gabata acikin rubutun mu daya gabata
.
3:-    YA HALATTA (Mace alhali tana yin jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) ko kuma mai Janaba su shiga masallaci domin jin wa'azi ko kuma daukan karatu, kada kudamu da hadisin da yazo acikin Sunan na Abiy-Dawuda hadisi na 232 wai daga Ummuna Aysha Allah ya kara mata yarda tace, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace  "Lallai ni ban halatta wa mace mai jinin haila ko kuma mai Janaba shiga masallaci ba"    (Wannan hadisi karya akayi wa Annabi bai tabbata ba)   ya halatta kushiga cikin masallaci Kuyi zaman ku in shaa Allah Imam Muhammad Nasirud-Deen Al-Albany Rahimahullah yace  "Babu wani ingantaccen hadisi kai tsaye da yazo yake nuni da cewa an hana mace mai jinin haila ta shiga masallaci"   (Duba Fataawa-Muhimmah Lin-Nisaa'il-Ummah 55, ko Fiqhul-Muyassir na Sa'ad Yusuf shafi na 57)    don haka dai  'yan uwa na babu wanda ya hanaku, Allah ta'ala yasa kun fahimce ni, Allah yasa Mudace
.
Alhamdulillah anan zan dakata in shaa Allah, sai ajira mu a fai-fai na 010 kuma in shaa Allah shine zai zama rubutu na karshe akan wannan matsalar ta jinin haila, wanda kuma taken wannan rubutun shine FAA'IDOJIN MU ACIKIN WANNAN LECTURE, Allah ta'ala yayi mana jagoranci, Allah yasa Mudace, Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuh
.
Hussaini Haruna Ibn Taimiyyah Abu-Nabeelah Kuriga
.
                **24/Shawwal/1438**
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support