Haihuwar imamul hussain (RA) ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Thursday, 5 October 2017

Haihuwar imamul hussain (RA)

HAIHUWAR IMAMUL HUSAIN (RA)
**********************************
Ummul Fadhli bintul Harith (Matar Sayyiduna Abbas bn Abdil Muttalib) tayi wani mafarki wanda ya firgitata don haka ta tafi wajen Manzon Allah (saww) ta gaya masa tace :

"Hakika ni nayi wani mummunan Mafarki (Naga) kamar an yanke wani bangare daga jikinka, Kuma an ajiyeshi adakina.

Sai Manzon Allah (saww) yayi murmushi yace mata "ALKHAIRI KIKA GANI (A MAFARKINKI). DOMIN IN ALLAH YA YARDA FATIMATU ZATA HAIFI WANI YARO, KUMA ZAO KASANCE A DAKINKI".

Kwana ka'dan kuwa sai Nana Fatimah ta haifi wani kyakkyawan Jariri mai albarka nai haske, Wanda ba'a samu wani jaririn da ya fishi haske da Qamshi da tsarki da albarka a garin Madeenah ba..

Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) da kansa ya sanya masa suna AL-HUSAIN (alaihis salam) Kuma ya yanka masa Aqeeqah, ya rarraba naman ga Talakawa da Miskinai.

Anyi wannan haihuwa mai albarka aranar 3 ga watan Sha'aban shekara ta 4 bayan Hijirah, agarin Madeenah.

Kuma Imamul Husain ya rayu rayuwa mai albarka cikin ilimi da ibadah da tsoron Allah. Kuma yayi Shahadah ne aranar Ashura awani waje da ake kira Karbala' akan hanyarsa ta tafiya Kufa, Sojojin Ibnu Ziyadin suka tareshi tare da Jama'a masu yawa daga iyalan gidan Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

Daga cikin wadanda sukayi shahadah tare dashi akwai Qannensa da 'ya'yansa, da kuma 'Ya'yan Dan uwansa (Imamul Hasan).

Albaniy ya inganta Hadisin mafarkin nan acikin Silsilatus Sahihah, hadisi na 1227 da kuma Sahihul Jami'i hadisi na 3146.

Shahadah ta hanyar kisan gillah, hanya ce ta bayin Allah. Domin kuwa Sarkin Muminai Umar bn Al-Khattab da Sayyiduna Uthman bn Affan da Imamu Aliyu (Allah ya yarda dasu baki dayansu) duk kashesu akayi.

Ya Allah ka Qara mana son iyalan gidan Annabinka (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) mafifitan iyalai adoron Qasa.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (11-01-1439 02-10-2017).


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support