Shin wai idan Jinin-Al-ada ya ɗaukewa Mace kafin ketowar Al-fijr, dolene sai tayi Sallar Magriba da Isha'i? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Thursday 12 October 2017

Shin wai idan Jinin-Al-ada ya ɗaukewa Mace kafin ketowar Al-fijr, dolene sai tayi Sallar Magriba da Isha'i?

*Tambaya ta (378)*
:
_Shin wai idan *Jinin-Al-ada* ya ɗaukewa Mace kafin ketowar *Al-fijr,* dolene sai tayi *Sallar Magriba* da *Isha'i*?_
:
_*Amsa:*_
:
_Dangane da abinda Mālamai sukace akan wannan *Mas'ala* shine, idan mai *Jinin-Al-ada* tayi tsarki kafin *faɗuwar rana* kokuma tayi tsarki kafin *ketowar alfijr* to wajibine akanta tayi *Sallolin Magriba da Ishā'i* kokuma *Azahar da La'asar*, saboda tsarki ya zomata acikin lokutan waɗannan Salloli, sannan kuma zata haɗesune alokaci ɗaya ta Sallacesu wato zatayi jam'insune, saidai idan lokacinne yaƙure tayadda bazaiyiwu ta sallacesu gaba ɗayaba, to shikenan sai tasallaci taƙarshen, kuma wannan itace fatawar da wani sashe na *Mαиzoи Aʟʟαн(ﷺ)* suke bayarwa, sannan kuma mafi yawa daga cikin *Mālamai* suma akan haka sukatafi, saidai wasu daga cikin *Mālamai* sukace a'a iyakar Sallar da tasamu tsarki acikin lokacintane kaɗai zata *Sallata:*_
:
_Amma idan tsarki yazowa Mace bayan *Sallar Asubahi* ko *Sallar Azahar* kokuma bayan *Sallar Magriba* to kawai zata Sallaci waɗannan *Salloline* ɗaiɗaikunsu tunda dama ba'ayin jam'i atsakaninsu,_
:
_Saidai *Mālamai sunyi Saɓani* gameda cewa idan *Jinin-Al-ada* yazowa Mace alokacin *Sallah* kuma batariga tayi wannan *Sallarba* Shin idan tayi tsarki dolene sai tarama wannan *Sallar* kokuma bazata ramaba? Mazhabin *Shāfi'iyya* dakuma *Hanābila* suntafine cewa dole sai tarama, amma Mazhabin *Mālikiyya* da *Hanafiyya* sukace a'a bazata ramaba tunda bawai sakaci tayiba na *ƙin yin Sallar* akan lokacinta, danhaka sukace bazata ramaba, danhaka dai Mālaman da suka tafi akan *Ƙaulin* cewa bazata ramaba *Alal-Haƙiƙa*  maganarsu tafi Dalilai dakuma Hujjoji masu *Ƙarfi,*_
:
*_※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※_*
:
*_ωαηαη sнιηε gωαяgωαdoη ɗαη αвιηdα ιʟιмιη мυ dαкυмα вιηcιкεηмυ үαкαι zυωα gαяεsнι, dαηнαкα ιdαη αηgα ωαηι кυsкυяε αcιкιη αвιηdα мυкα яυвυтα тo αηα'ιүα ғαɗαкαя dαмυ мυgүαяα, тαяεdα кαωo нυננα мαι ƙαяғι:_*
:
*_Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:_*
                 *_↓↓↓_*
:
*"المجموع للنووي"(2/562)*
:
*"المغني لإبن قدامة" (1/238)*
*_"""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
              *Daga Zaυren*
             *Fιƙ-нυl-Iвadaт*
*_"""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
              *_→AMSAWA←_*
           *Mυѕтαρнα Uѕмαи*
              *08032531505*
*_"""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
_*Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾*_
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support