MATAN ZAMANI - Zauren fiqhu ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Tuesday 10 October 2017

MATAN ZAMANI - Zauren fiqhu

MATAN ZAMANI
***********************************
* Babban kuskure ne gareki amatsayinki na 'Ya mace ki rika nuna ma saurayi kwadayin kudinsa afili. Kina kawo masa bukatunki,ya saya miki wannan, ya saya miki wancan, ya baki kudin dinki, kudin anko, kudin party, etc.. Da zarar
saurayi ya biya miki bukatarki ta kudi, to shi kuma zai fara kwadayin kema DOLE ki biya masa bukatar sha'awarsa..

* HARAMUN NE, BAI HALATTA BA, ku rika zama daga ke sai saurayinki.. Komai Ustazancinsa, komai yawan soyayyar dake tsakaninku,
Shaitan ne zai zama na ukunku.. Zai shiga zuciyarsa ya rika Qawata masa cewa yayi zina dake.. kema
haka..

* TSINUWAR ALLAH DATA MALA'IKUNSA ta tabbata bisa duk budurwar da zata sanya kaya matsatsu masu nuna siffar Nononta ko bayanta, Sannan ta
fesa turare ta tafi wajen saurayi... Annabi (saww) ya tsine ma mataye masu irin wannan shigar..Kuma
yace ba zasuji koda Qamshin aljannah ba!!!

* AZABA MAI RADADI DA WULAKANTARWA ta tabbata bisa budurwar da take SEX-CHAT (chatting na batsa) da wani saurayi.. koda kuwa ya kai mata sadaki..
Allah zai kwashe albarka gareshi
shi da ita...

* Kunyar duniya da kuma FALLASA ARANAR TSAIWA ta tabbata bisa dukkan budurwar da ta bama saurayi jikinta yana ta'bawa, ko kuma ta bashi dama yayi zina da ita..
Daga wannan ranar taci amanar Allah da Manzonsa da amanar iyayenta da danginta..
Kuma ta fidda kanta daga layin mutane masu albarka masu
Qima awajen Allah.

Addu'ar ZAUREN FIQHU ita ce: Allah yasa wannan rubutun ya zama sanadiyyar shiryuwar bayin Allah wadanda suka afka cikin wannan
babbar hallaka..
Wadanda basuyi kuma, Allah ya
kiyayemu baki daya. Kuyi share Wanda kadamu dasu Allah zaibiyaka ranan gobe.

DAGA:
       ZAUREN FIQHU.


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support