ABUBUWA GUDA 6 SUNA JANYO RASHIN ALBARKA ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Monday 16 October 2017

ABUBUWA GUDA 6 SUNA JANYO RASHIN ALBARKA

ABUBUWA GUDA 6 SUNA JANYO RASHIN ALBARKA



Albarka yana nufin alkhairi mai yawa mai dauwama,Albarka idan ta samu acikin dukiya sai dukiyar ta yawaita ta zama mai yawan amfani,haka idan ta samu acikin 'ya'ya sai su amfaneka duniya da lahira,idan kuma aka sameta a rayuwa sai rayuwar ta zama mai amfanu duniya da lahira mai tserarwa a duniya da lahira.

Allah Madaukakin sarki idan yana nufin bawansa da alkhairi sai ya sanya albarka acikin abinda ya basa,har sai an wayi gari abu kadan yazama mai yawan amfani,karami ya zama babba da izinin Allah.


Daga cikin abubuwan da suke janyo rashin albarka a rayuwa ga kadan daga cikinsu;-

1-Na farko
*"Rashin jin tsoran Allah da rashin kiyaye dokokinsa da umarninsa"*.

Allah ﷻ،yana cewa:
﴿ﻭﻟﻮ ﺃﻥ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻘﺮﻯ ﺁﻣﻨﻮﺍ ﻭﺍﺗﻘﻮﺍ ﻟﻔﺘﺤﻨﺎ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺑﺮﻛﺎﺕ ﻣﻦ ﺍﻟﺴﻤﺎﺀ ﻭﺍﻷﺭﺽ﴾.

Taqwa wato kiyaye dokokin Allah da bin uwarninsa da hanuwa da haninsa yana janyowa saukowar albarka daga sama da kasa,kuma ya yawaita albarka a tsakanin al'umma baki daya,amma rashin Taqwa da yawaita basa umarnin Allah da keta iyakokin Allah yana janyo rashin albarka da daukewar arziqi abayan kasa.

2-Na biyu
*"Gafala cikin rashin Addua da rokon Allah,da rashin kwadayi da neman abinda yake wajan Allah"*

Wata rana Manzon Allah ﷺ sai ya sami Sahabi Abaa Umama R.A shi kadai babu kowa,a tare da shi akwai alamar bakin ciki da damuwa,sai Manzon Allah ﷺ yace da shi;
*(Mi ya zaunar da kai acikin Masallaci yanzu a lokacin da ba lokacin sallah ba??)*sai yace Ya Manzon Allah ﷺ kuncin rayuwa ya sameni kuma ga bashi yayi mini yawa,sai Manzon Allah ﷺ yace;
*(shin bazan Koyarda kai ba abinda idan kafa Allah zai tafiyar maka da bakin cikin da kake cika ba?? Kuma ya biya maka dukkan bashin da yake tare da kai ba??)*sai yace;Eh ya Manzon Allah,sai yace da shi;
*(Idan ka wayi gari ko idan kayi yammaci sai kace:)*
"ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﺍﻟﻬﻢ ﻭﺍﻟﺤﺰﻥ،ﻭﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﺍﻟﻌﺠﺰ ﻭﺍﻟﻜﺴﻞ،ﻭﻣﻦ ﺍﻟﺠﺒﻦ ﻭﺍﻟﺒﺨﻞ، ﻭﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﻏﻠﺒﺔ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻭﻗﻬﺮ ﺍﻟﺮﺟﺎﻝ،"
Abu Umama yake cewa;
"Sai na riqa fadar wannan adduar sai Allah ya tafiyar min da dukkan damuwata kuma ya biyamin bashin dake kaina".

3-Na Ukku
*"Yanke zuminci yana janyo kuncin rayuwa da rashin albarka acikin rayuwa da arziqi"*

Manzon Allah ﷺ yana cewa;
*(Dukkan wanda yake son Allah ya yalwata arziqinsa kuma ya tsawaita rayuwarsa,to ya sadar da zumincinsa)*.
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭﻣﺴﻠﻢ.

Kyawawan halaye da sadar da zumici yana janyo albarka acikin rayuwa da arziqi da dukiya da 'ya'ya,haka kuma rajin sada zuminci yana janyo rashin albarka acikin su.

4-Na hudu
*"Rashin sadaka da ciyar da dukiya cikin daukaka kalmar Allah"*.

Hakika Allah ﷻ ya hukunta dukkan wanda ya ciyar da dukiya ko yayi sadaka ga masu buqata,to Allah zai yalwata masa kuma ya buda masa hanyar samu mai yawa,kuma ya sanya masa albarka acikin dukiyarsa.

Manzon Allah ﷺ yana Fada ga Asma'h R.A;-
*(Ki ciyar sai Allah ya ciyar dake)*
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﻣﺴﻠﻢ.
A kowane yini Akwai Mala'iku guda biyu suna cewa;
*(Ya Allah ka sanya albarka ka rubaiya duniyar wanda yake ciyarsa,ya Allah ka janye albarka acikin dukiyar wanda baya ciyarsa)*
@ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ ﻭﻣﺴﻠﻢ.

5-Abu na biyar
*"Kasala da barin aiki"*

Musulinci addini ne na aiki da addini bane na cima zamne ba,Manzon Allah ﷺ yana cewa;
*(Kuma an sanya aziqina a karkashin inuwar takobina)*
@ﺻﺤﺤﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ.

6-Na shida
*"Rashin dogaro ga Allah ingantacce tare da rashin neman arziqi a wajan Allah"*.

Manzon Allah ﷺ yana cewa;
*(Da dai zakuriqa yin dogaro ga Allah hakikanin dogaro,da Allah ya azurta ku kamar yanda yake azurta tsuntsu,yana fita da sassafe cikinsa babu koma,amma ya dawo da yamma cikinsa a cike)*
@ﺃﺧﺮﺟﻪ ﺃﺣﻤﺪ ﻭﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺀ ﻭﺍﺑﻦ ﻣﺎﺟﺔ ﻭﺍﺑﻦ ﺣﺒﺎﻥ ﻭﺍﻟﺤﺎﻛﻢ ، ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ :ﺣﺴﻦ ﺻﺤﻴﺢ.


Allah ne mafi sani.


ﺃﺳﺄﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻥ ﻳﻤﻦ ﻋﻠﻴﻨﺎ ﺟﻤﻴﻌﺎ ﺑﺎﻟﺘﻮﻓﻴﻖ ﻭﺍﻟﺮﺯﻕ ﻭﺍﻟﺒﺮﻛﺎﺕ ،،،
ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻭﺑﺎﺭﻙ ﻋﻠﻰ ﻧﺒﻴﻨﺎ ﻣﺤﻤﺪ



Shiga nan
www.duniyarfatawa.com.ng
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support