Illolin gulma 04 ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Saturday, 30 September 2017

Illolin gulma 04

```★★★ILLOLIN GULMA★★★```
~~~~~~~~~~4~~~~~~~~~~
*Zauren SA'ADATUL-MUSLIM*
.
_Muna bayani akan gulma kuma mun fadi yanda Annabi saw ya fassara mana cikakkiyar kalmar gulma_
.
_Kunga kenan mu sai dai muce Allah ta'ala ya tsare mu, domin kuwa yanda muke yin mu'amala da gulma ya subhanallah,  'yar uwa ta dan uwa na Annabi ne fa ya fassara mana ma'anar kalmar gulma cewa, magana ce wacce zaka fada akan dan uwanka gashi kuma aikin sa ne fa kafada amma idan yana wajen ransa bazaiji dadi ba, to ida kuwa haka ne su waye yanzu basuyin gulma yaku ja'ama?  Mutum ne zaka sameshi gashi da siffa ta mutanen kirki amma kuma sai kasameshi da siffa ta magulmata,  kamar yanda mata suke mu'amalar 'yan uwansu a wannan bangaren har idan aka samu wata tana kokarin yi masu nasiha sai suce ai akinta ne da batayi ba da baza'a fada ba, 'yar uwa wallahi wannan Gulma ne Allah ya hana, domin kuwa Allah cewa yayi  "Kada sashin ku yayi gulmar sashi" don haka kalar wannan gulmar haramun ne inji Annabi Muhammad saw,_
.
_Lallai idan muka dauki wannan fassara ta Annabi saw akan gulma to ashe kunga kenan wajibi ne mu tsaya mu kiyaye harshen mu domin kuwa kada balā'i ya sauka akan mu, muna neman tsarin Allah_
.
_Al-Imam Al-Hasanul-Basary babban tabi'ī daga cikin tabi'ai Allah yayi masa rahama yana cewa  "Yin magana akan wannan matsal kala uku ce, wanda kuma kakaf dinsu harāmun ne abu na farko shine ita kanta Gība din wato Gulma!  Na biyu kuma Kazafi abu na uku itace Karya,"  wato labari ne yazo ya sameka cewa wanefa yana aikata kaza, kai kuma sai kadauki wannan labarin kana yadawa, to wallahi wadannan kakaf dinsu harāmun,  'yan uwa ayi hakuri zamu ambaci dalīlai kadan da suke tabbatar mana da haramcin wadannan abubuwa in shaa Allahu,_
.
 _Abu na farko da zamu fara ambata shine wani hadisi swahīhī wanda kowwannen mu yasan wannan hadisin wanda Imam Bukhari ya ruwaito hadisin mai lamba 6018 a babin Ladubba, shi kuma Imam Muslim a Babin Imāni hadisi na 47  shi kuma Imam Tirmidhī acikin Sunan Babin da yake magana akan Qiyāma hadisi na 2500 hadīsin Abdirrahman Ibn Sakhr wato Abu-Hurairah Allah ya kara masa yarda, yace lallai Annabi saw yace  "Duk wanda yayi Imāni da Allah da rana ta karshe  to ya fadi Alkhairi ko yayi shiru"   kunga kenan a karkashin wannan hadisin zamu fahimci cewa magulmata Imānin su da Allah ta'ala akwai saura ba cikakken Imani suke dashi baga Allah domin Annabi ne ya fada,  'yan uwa gulma fa tana da hadari, kawai dai mu nemi tsarin Allah Madaukaki,_
.
_Zamu dakata anan sai mun hadu a darasi na gaba_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp ‬

Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support