NA RABA GADONA KAFIN NA MUTU, KO YA INGANTA ?? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Wednesday 13 September 2017

NA RABA GADONA KAFIN NA MUTU, KO YA INGANTA ??

*NA RABA  GADONA KAFIN NA MUTU, KO YA INGANTA  ?*


*Tambaya*

Assalamu alaikum. malam don Allah ina da tambaya da fatan za'a amsamin, wai mutum zai iya rabawa iyalansa gadansa kafin yamutu wai hakandin ya halatta? nagode


*Amsa*
Wa'alaykumussalam,

To dan'uwa malamai suna cewa hakan bai inganta ba, saboda dalilai, ga wasu daga ciki :

1. Hakan yana daga cikin gaggauta abin da Allah ya jinkirta, saboda Allah ya sanya rabon gado ne, bayan mutuwa.

2.  Zai iya yiwuwa daya daga cikin  iyalan nasa ya mutu kafin shi, ka ga sai a samu kwan-gaba kwan-baya.

3. Yana iya jawo hassada saboda daya daga cikin magadan zai iya yin kasuwanci da gadon da aka ba shi ya samu riba mai yawa kafin magajinsa ya mutu, wanda hakan zai iya kawo hassada tsakanin magada, don za su ga da ba'a yi gaggawar rabawa ba da ya kasance daga cikin rabonsu.

4. Yana daga cikin sharudan gado tabbatar da mutuwar  wanda za'a gada .

Allah ne mafi sani

*Dr, Jamilu Zarewa*
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support