FUSKOKIN 'YAN WUTA
************************
'Yan wuta, Fusakunsu baqi-qirin suke kaurara.. Kamar sauran sassan jikinsu. Baqaqe ne wuluk babu alamar haske balle Murmushi garesu.
Muryoyinsu kamar muryar bijimin da aka yanka.. Babu da'din ji, balle saurare. Da ache za'a jiyar da duniya irin Gunjin da 'yan wuta keyi, da kowa sai ya Mace dan tsoro..
Da ache 'dan wuta zai leko da fuskarsa duniya, da sai 'doyin fuskar ya kashe dukkan abinda ke doron Qasa.
Sayyiduna Abu Hurairah (ra) ya ruwaito daga Manzon Allah (saww) yana cewa :
"Hakika (Su 'yan Wuta) za'a rika Kwarara musu ruwan zafi akansu, Ruwan zai shiga cikin jikinsu har cikin cikinsu.. Sai kayan cikinsu ya rika Zagwanyewa har sai ya biyo ta jikin Sawayensu.. Sannan a mayar dasu kamar yadda suke".
(Tirmidhiy da Baihaqiy ne suka ruwaito)
Acikin wata riwayar da aka karbo ta hanyar Sayyiduna Abu Sa'eed Alkhudriy (rta) Manzon Allah (saww) cewa yayi :
"WUTA ZATA SOYA 'DAN WUTA HAR SAI LEƁENSA NA SAMA YA LANƘWASHE ZUWA TSAKIYAR KANSA. LE'BENSA NA QASA KUMA ZAI ZAGWANYE YAYI QAS, HAR YANA BUGUN CIBIYARSA".
(Imam Tirmidhiy ne ya ruwaito acikin sunanu hadithi na 2587).
Sa'eed bn Jubayr (rah) yace "Idan 'Yan wuta suka ji yunwa (Wata irin yunwa ce ta bala'i) zasuyi kururuwa (Suna neman agaji). Sai a agaza musu da bishiyar Zaqqum (Wata bishiya ce wacce ta Tsiro da chan Qasan Jahannama, idan ganyenta ya fa'do cikin wutar sai wutar ta rika Eehu saboda bala'insa. To shine abincin 'Yan wuta).
Idan suka ci daga gareta sai Fatar jikin fuskokinsu ta sa'bule (Allah ka kiyayemu).
Nan take sai a jarrabesu da wata irin Qishirwa.. Zasu rika eehu suna neman agaji. Sai a agaza musu da ruwan Hameem (Ruwan gyambo ne mai kauri, mai tsananin wari, ga tsananin Quna kamar narkakkiyar dalma).
Idan suka kusanto dashi zuwa ga bakunansu, Sai tsananin zafin bala'in ruwan zai Soye naman fuskokin nasu har sai naman fuskokin ya kwakkwabo acikin ruwan..
Shi yasa Allah ma bayan ya siffanta wannan ruwan sai yace : "TIR DA WANNAN ABIN SHAN, KUMA WANNAN MASAUKI (WATO GIDAN WUTA) YA MUNANA".
(Aduba Tafsirin Ibnu Katheer ayah ta 29 acikin Suratul Kahfi).
Ibnu Abi Hatam ya ruwaito ta hanyar Abu Hurairah (ra) daga Manzon Allah (saww) yana cewa :
"Hakika ita Jahannama idan aka Koro mata Mutanenta zuwa gareta, sai harshenta ya fara riskarsu. Zata lashesu lasa guda wacce babu sauran wani nama (tsoka) da zai ragu ajikinsu fache sai ya narke ya zube Qas akan sawayensu".
😭😭😭😭😭
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!!
Hakika dukkan bala'i yana cikin Wuta.. Duk wanda ya shiga wuta yayi asarar da babu fanshewa!!
Ya Allah ka kiyayemu daga wuta! Ya Allah ka kiyayemu daga wuta! Ya Allah ka kiyayemu daga wuta!!
AN GABATAR DA KARATUN A ZAUREN FIQHU WHATSAPP (20-09-2017 29-12-1438).

0 comments:
Post a Comment