ZAN IYA HULDA DA MAI KUDIN LUKUDU ? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Saturday 16 September 2017

ZAN IYA HULDA DA MAI KUDIN LUKUDU ?

*ZAN IYA HULDA DA MAI KUDIN LUKUDU ?*

*Tambaya*

Assalama alaikum. Malam dan Allah
Ina aiki ne  akarkashi wani Alhaji Amman a nazargin sa da wai  kudisa bana halal bane wasu suce dan  luwadi ne  wasu  kuma suce kudin lukudu ne ina  so insan  yadace nacigaba damai aiki ko inbari Allah y kara lpy da ilimi da kafin basira ameen

*Amsa*

Wa alaikum assalam, Ya wajaba ka tabbatar da hakan kafin ka yanke hukunci.
Ba'a gina hukunci a musulunci akan shakka ko zato mara rinjaye, saboda wani sashen zaton zunubi ne kamar yadda aya ta (12) a cikin suratul Hujraat ta tabbatar da hakan.

Idan wani bangare na kasuwacinsa halal ne wani kuma Haram ne za ka iya hulda da shi, saboda Annabi S.a.w. ya yi mu'amala da yahudawa kuma a cikin dukiyarsu akwai halal akwai kuma haram.

Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
16/09/2017


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support