TSOHUWA BATA SHIGA ALJANNAH! Zauren fiqhu ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Monday, 18 September 2017

TSOHUWA BATA SHIGA ALJANNAH! Zauren fiqhu

TSOHUWA BATA SHIGA ALJANNAH!
**************************************
Imamut Tirmidhiy ya ruwaito hadisi Mursal ta hanyar Imam Hasanul Basariy (rah) cewa :

"Watarana Wata Tsohuwa tazo wajen Manzon Allah (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) tace : "Ya Ma'aikin Allah Ka roki Allah ya shigar dani Aljannah".

Sai Manzon Allah (saww) yace mata "YA KE MAHAIFIYAR WANE, HAKIKA ITA (ALJANNAH) TSOHUWA BATA SHIGARTA".

Daga jin haka sai tsohuwar nan ta juya ta koma tana Kuka. Sai Manzon Allah (saww) yace "KU BATA LABARI CEWA BA ZATA SHIGA ALJANNAH ALHALI TANA TSOHUWA BA. YA KARANTO WASU AYOYIN DAKE NUNA CEWA ANA MAYAR DASU 'YAN MATA NE (WATO SAI AN MAYAR DA ITA BUDURWA KAFIN A SHIGAR DA ITA ALJANNAH).

Allahu Akbar! Annabi (saww) ya kasance yana yin Kakaci da Sahabbansa amma ba ya furta wata kalma fache ta gaskiya.

Mafi girman Salatai da sallamomi su tabbata bisa mafi girman darajar halittu awajen Ubangijinsa, Shugabanmu Annabi Muhammadu tare da iyalan gidansa da dukkan Sahabbansa acikin kowacce Qiftawar ido Gwargwadon adadin motsawar halittu da numfashinsu baki daya. albarkacin Salatin nan Ya Allah ka dawwamar mana da Soyayyarsa da Jin nauyinsa da tabbatuwa bisa tafarkinsa Madaidaici har zuwa karshen numfashinmu. Ameeen.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (18/09/2017 27-12-1438).
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support