ZIYARAR DA SHAITAN YAKAI MA ANNABI NOUHU (AS).
Abul Faraj Ibnul Jawzee ya ruwaito tare da isnadinsa daga Abdullahi 'dan Umar 'dan Khattab (ra) yana cewa:
Alokacin da Annabi Nouhu (as) ya hau Jirginsa, sai yaga wani tsoho wanda bai san dashi ba. (Ashe Iblis ne La'ananne). Sai Annabi Nouhu (as) yace masa: "MENENE YA SHIGO DAKAI?".
Sai yace : "Na shigo ne domin in kama Zukatan Mutanenka. Har ya zama zukatansu suna tare dani, Jikkunansu kuma suna wajenka".
Sai Annabi Nouhu (as) yace masa "FITA, YA KAI MAQIYIN ALLAH!!!".
Sai yace: "Abubuwa guda biyar dasu nake hallakar da mutane. Zan baka labarin guda uku daga ciki, amma ba zan gaya maka sauran biyun ba".
Nan take sai Allah (SWT) yayi wahayi zuwa ga Annabi Nouhu (as) cewa: "BAKA DA BUKATAR JIN WADANNAN GUDA UKUN, GARA KA UMURCESHI YA GAYA MAKA GUDA BIYUN".
Da ya gaya masa hakan sai La'anannen yace : "(abubuwan nan guda biyu) dasu ne nake saurin hallakar da mutane, sune : HASSADA DA KUMA KWADAYI".
"Ita hassada ta dalilinta ne aka Tsine mun albarka, kuma aka mayar dani na zama Shaitani abin korewa daga rahamar Allah".
"Shi kuma KWADAYI, ta dalilinsa ne na samu biyan bukata-ta akan Annabi Aadamu (as) duk da cewa an halatta masa Aljannah baki dayanta. (Amma kwadayi yajashi zuwa ga cin bishiyar nan guda daya rak wacce aka hanashi yaci)".
ZAUREN FIQHU : 'Yan uwa mu guji wadannan Miyagun halaye guda biyu. Wallahi duk wanda yake aikata wadannan halayen sai ya Qaskanta awajen Allah da bayinsa.
Mafiya yawan husumar dake faruwa acikin gidajenmu da Unguwanninmu, HASSADA ce asalinsu.
Mafiya yawan laifukan da suka fi lalata al'ummah, kwadayi ne asalinsu. Kamar irin su Zina, Sata, Luwadi, madigo, Zamba, Ha'inci, Cin hanci, Zalunci, etc.
Allah shi kiyayemu don Qarfin ikonsa.
Wannan Nasiha tana zuwa ne daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP - 1 (22-09-2015).
Kayi sharing zuwa ga Contacts dinka amma DON ALLAH kada ka chanza koda harafi guda daga wannan Sakon. Masu cin amanar Ilimi kuji tsoron Allah ku dena.

0 comments:
Post a Comment