AKWAI MASU CEWA ALLAH YANA KO INA, SUNA HUJJA DA FADINSA ( WA HUWA MA'AKUM AINAMA KUNTUM) DA DAI WASU AYOYIN, YAYA ABUN YAKE? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Tuesday, 12 September 2017

AKWAI MASU CEWA ALLAH YANA KO INA, SUNA HUJJA DA FADINSA ( WA HUWA MA'AKUM AINAMA KUNTUM) DA DAI WASU AYOYIN, YAYA ABUN YAKE?

*AKWAI MASU CEWA ALLAH YANA KO INA, SUNA HUJJA DA FADINSA ( WA HUWA MA'AKUM AINAMA KUNTUM) DA DAI WASU AYOYIN, YAYA ABUN YAKE?*

الحمد لله.

*AMSA:* Allah madaukakin Sarki yana Saman Al'arshi, saman Dukkan halittu, a wajan Ahlussunnah Wal-jama'a, Haka dukkan manzanni sukazo da Wannan aqidar, Allah yana Saman Al'arshi.

Kamar Yanda ya fada a cikin Ayoyi maban-banta Masu yawa acikin Alqur'ani mai girma.

Allah ya bayyana Qarara ya dai-daita a saman Al'arshinsa, dai-daituwar da ta dace da girmansa da Daukakarsa, Ba Wani Abun Halitta da yai Kama dashi wajan yanda ya dai-daita.

Babu Wanda yai kama da Allah, ko yake kama dashi,,

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya Tambayi Wata baiwa a ina Allah yake? Tace yana Sama, Yace Ni Wanene tace: Manzan Allah, sai ya cewa: Uban gidanta ka 'yantata tabbas Ita Muminace. Muslim ya ruwaito.

Wannan ya Nuna Allah yana Sama can Saman Bakwai Saman Al'arshi sama madaukakiya.

ISahabbai sun hadu kamar yanda Manzanni Suka hadu, akan Allah yana Sama, Saman Al'arshi.

Duk Wanda yace Allah yana Kowanne waje, ko baya Sama, shi kafirine, Mai Qaryata Allah da Manzansa, da qaryata Ijma'in Ahlussunnah Wal-jama'a, Kamar dariqun bidi'a irinsu *Jahamiyyah da Mu'utazilawa,* da Makamantansu, Wadannan suna cikin Wadanda sukafi kowa kafirci cikin Mutane, saboda Inkarin sunayen Allah da Siffofinsa.

Fadin Allah madaukakin Sarki acikin Suratul Mujadala aya ta (7).

ألم ترى أن الله يعلم مافي السماوات وما في الأرض ما يكون من نجوى ثلاثة إلا هو رابعهم ولا خمسة إلا هو سادسهم، ولا أدنى من ذلك ولا أكثر إلا هو معهم أين ما كانوا، ثم ينبئهم بما عملوا يوم القيامة، إن الله بكل شي ء عليم.

Bata Nufin Irin yanda batattu da 'yan bidi'a suke fassara ta, da yanda suke jefa shubuha da rudu a zuqatan Masu qaramin Sani.

Abunda Ake nufi acikin Ayar shine, Babu wasu mutum uku da zasu zauna suyi zance ko tattaunawa aboye asirri face sai Allah ya zama Na hudunsu, idan Su biyarne ko Qasa da Haka ko sama da haka face Sai Allah ya Zama yana tare dasu, da Ilminsa da Buwayarsa, a duk inda Suka kasance, Babu Abunda zai boyu agareshi na Al'amarinsu, Sannan ranar Alqiyama Ya basu labari akan Abunda Suka aikata, na Alkhairi ko sharri, Sannan yai Musu sakayya dashi, Tabbas Allah Masanine Akan Komai.

Wannan shine Abunda ayar da Ire irenta suke nufi, Bata cin karo da Ayoyi da Ingantattun Hadisan da suka nunar da Allah yana Sama a saman Al'arshi, babu Abunda yake buya agareshi Na ayyukan bayi aduk inda suka aikata Wani abu, yana tare dasu da Ilminsa da Buwayarsa.

Duk Wanda kaji yana jidali da hayaniya akan Abunda ayoyi da Hadisan dai-duwar Allah a saman Al'arshi suka tabbatar, inma tantirin jahile wanda ya gaji bidi'a a nonon uwarsa, ko kuma zindiqine Batacce wanda Allah ya Wulaqantar dashi ta hanyar aukawa wannan bata.

Mai Son Qarin bayani saiya duba Litattafan tafsiri musamman Tafsirin ibnu kaseer qar-qashin wannan aya da Makamantanta, da Kuma litattafan Aqida da Tauhidi.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت، أستغفرك وأتوب إليك.

*🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai*
*WhatsApp Group*
*2348123432272*
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support