```★★★ILLOLIN GULMA★★★```
~~~~~~~~~~6~~~~~~~~~~
*Zauren SA'ADATUL-MUSLIM*
.
_Cigaba_
.
_Akwai wani hadisi da Annabi saw yake bayar da labari akan abinda zai faru a ranar Alqiyāmah, yake cewe "Mutum ne za'azo dashi ranar tashin Al'qiyamah gashi yayi sallah cikakka kuma yayi azumi cikakke kuma ya bayar da dukiyar sa a hanyar Allah, wata kīla ma yaje aikin hajji, gashi a filin qiyamah ayyuka na kwarai Alhamdulillah, to amma dai matsalar sa itace ya zagi wannan sai a dibi ladarsa a baiwa wanda ya zaga, haka kuma kuma yayi ma wani Qazafi shima nan sai a dībi ladarsa a baiwa wanda yayi ma Qazafin, haka kuma yaci dukiyar wani shima nan a debi ladan sa a baiwa wanda yaci dukiyar sa, haka kuma yayi gulmar wani shima anan a debi ladarsa a baiwa wanda yayi gulmar, haka kuma ya zubar da jinin wani shima nan sai a debi ladarsa a baiwa wanda ya zubar da jinin sa, haka kuma ya bugi wani shima a debi ladansa a baiwa wadanda ya zalunta, a haka malā'iku zasuyi ta dībar ladansa ana rarrabarwa amma bai isa ya hana ba, sai a samu gashi da yana da lada amma fa sun kare saboda zaluncin daya aikata yau gashi ya koma ziro, Annabi yace wannan mutumi shine fallasashshe wanda asirinsa ya gama tonuwa kai karshen Al'amari dai makomar sa itace wutar jahannama!" Allah ya tsare mu_
.
_'Yar uwa kamar yadda muka fada a baya cewa Allah ta'āla ya haramta gulma, to ga wani hadisi mai tsoratarwa wanda Abū-Hurairah ya jiyoshi daga Annabi saw, Lallai Annabi saw yace "Lallai mutum zaiyi tayin magana da wata kalma wacce Allah ya yarda da ita, ba tare da yasani ba ko yanaga ba komai bane to kuma saboda wanban kalmar da yake furtawa sai Allah ya ta'ala ya daukaka darajarsa da ita wannan kalmar, sannan kuma yace lallai wani bawan Allah, wato wani mutum zaiyi tayin wata magana da wata kalma wacce take acikin abinda Allah ya hana wato Allah bayason kalmar kuma shi da yake amfani da wannan kalmar a tunanin sa ba komai bane amma a haka ita wannan kalmar sai ta zama sanadin sa na shiga wutar jahannama!" Wannan hadisi ne ingantacce yana cikin Sahīhul Bukhāri hadīsí na 6478 sannan yana cikin Musnad da Imām Ahmad mujalladi na 2 shafi na 334, wallahi 'yan uwa daga cikin kalmomin da Allah bayaso Gulma tana cikinsu,_
.
_Lallai dan uwa na da kuma ke 'yar uwa ta ku karkade kunnuwan ku kuji abinda zan sanar daku, wannan abin da zan fada yanzu shi yakamata mutane su dika fadawa 'yan uwansu idan sunzo masu da labari sannan zamu doshi kadan daga magabata muji abinda suka nuna mana dangane da illar harshe da kuma musībar gulma, ku kasance kuna fada ma 'yan uwanku cewa *Dukkan mu ko ni kaina ko kai ko ke dukkan mu kakaf dinmu duk wanda yasan idan zaiyi magana acikin mu amma kuma yasan ba alkhairi bace to kawai yayi shirū mu abinda mukafi so kenan domun tanan ne zamu samu kāriya daga musība da take tattare da Gulma* An samu inganracciyar riwaya daga Ibn Umar yana cewa "Kashedin ku da yawan magana," haka kuma Imāmun-Nakha'ī yana cewa "Mafi yawan mutane sun hallaka saboda yawan dukiya da kuma yawan magana"_
.
_Har wayau an samu asar daga Imamu Annakha'i yake cewa "Lallai yawaita magana a wajen da babu wata bukatar hakan, yana sanya kekashewar zuciya," ida kika fito gidan wance ina zaki gidan wance! Wallahi idan ka bībiya babu abinda takeyi sai gulma, kawai ita ta zama uwar Gulma a gari bata anan bata acan ke kuwa!? An samu wata riwaya daga salman Allah ya kara masa yarda wani mutum yace ma Salmān kayi min wasiyya yakai Salmān, a lokacin da Salmān ya tashi bashi amsa sai yace masa "Kada ka kuskura ka dika yin magana! Sai wannan mutum yace to ni kuwa ya zanyi da jama'a dangane da bukatu na yau da kullum idan naqi nayi magana, yana fadar haka sai Salmān yace masa to kuwa kasani idan dai har zakayi magana to kayi magana da gaskiya, banda Gulma ko Annamīman ci ko karya aa kayi magana da gaskiya ko kuma kayi shiru inji Salmān Allah yayi masu rahamah_
.
_Zamu dakata anan sai mun hadu a darasi na gaba_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp

0 comments:
Post a Comment