```ASHURA DA TASU'A```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zauren SA'ADATUL-MUSLIM*
.
_Da sunan Allah mai rahama mai jinkai, ranar Ashura itace ranar 10 ga watan Al-Muharram wato watan farko na sabuwar shekarar Musulunci wanda ya inganta daga Annabi Saw cewa ya azumci wannan ranar kamar yadda bayanin ya gabata, to ita kuma Tasu'a fa? Ranar Tasu'a itace ranar 9 ga watan Al-Muharram wacce Annabi yayi nufin azumtar wannan ranar Amma Allah madaukaki bai kai Annabi Saw wannan lokaci ba, dalili kuwa hadisin Ibn Abbas wanda yake cewa "A lokacin da Annabi Saw yayi azumin Ashura kuma yayi umarni da cewa a azumci wannan ranar, sai mukace ya Manzon Allah lallai wannan rana ce wacce yahudawa da Nasara suke girmama ta, sai Annabi Saw yace, idan har shekara ta zagayo da yardan Allah zan azumci ranar 9 ga wata, (wato 9 ga watan Al-Muharram sannan ya azumci 10 ga watan) Ibn Abbas yace Allah madaukaki bai kaddari Annabi Saw yakai shekarar ba, sai mutuwa tazo ma Annabi Saw" Muslim da Abu-Dawuda ne suka ruwaito wannan hadisin, duba littafin Fiqhul-Muyassir na Sa'ad Yusuf shafi na 177,_
.
_'Yan uwa kunji inda azumtar 9 ga wannan wata na Al-Muharram ya samo asali wato ka azumci 9 da 10 ga wannan watan shi akafi so, amma ga wanda bashi da karfin yin azumi guda biyu a jere shi ko ita guda daya 1 rak kawai zata iya yi to tayi kokari tayi na 10 ga watan kada tace zatayi 9 tabar na 10 aa kawai mutum matukar shi guda 1 kawai zaiyi to yayi 10 ga watan wato Ashura shi yafi, sabanin 'yan sha-biyu da suke wasa da makami suna illata jikin su wannan ba koyarwar Musulunci bane da kuma Nawasib masu yin cika-ciki shima wannan babu shi a Musulunci abinda ya inganta shine yin wannan azumi guda biyu wato 9 da 10 ga wannan watan na Al-Muharram, wanda kuma a yanzu da nake wannan rubutun da safe yau Laraba wato Wednesday 7 ga watan Al-Muharram shekara ta 1439 wanda azumin Tasu'a zai kama ranar Juma'a shi kuma Ashura ranar Asabar, Allah ya bamu ikon yin Azumin don Allah, Allah yasa mudace_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp

0 comments:
Post a Comment