```★★★ILLOLIN GULMA★★★```
~~~~~~~~~~5~~~~~~~~~~
*Zauren SA'ADATUL-MUSLIM*
.
_Muna bayani akan Illolin Gulma Zamu cigaba in Allah ya yarda_
.
_Lallai dan uwa wajibi ne ka dika kiyaye harshen ka wajen fadin alkhairi Imamu Dabarānī ya ruwaito hadisi daga Aswad dan Asram Al-mahāribī yace ni kuwa sai nace ya manzon Allah kayi min wasiyyah, sai Annabi saw yace "Shin ka kiyaye harshen ka?" Ni kuma sai na bashi amsa cewa " Ni kuwa mai zan kiyaye idan har ban kiyaye harshe na ba ya Annabin Allah? Sai Annabi yace "Shin ka kiyaye hannuwan ka? Ni kuwa sai na amsa da cewa "Me zan kiyaye idan ban kiyaye hannuwa na ba? Sai Annabi yace "Kada ka kuskura kafadi wata magana da harshen ka sai dai abu mai kyau na alkhari kuma kada ka kuskura ka shimfida hannuwan ka sai dai zuwa ga aikin Alkhairi" wannan hadisi ne Hasan Haisamī ya kawo shi acikin Maj'moo' mujalladi na 10 shafi na 303 hadisi ne ingantacce, 'yan uwa kunga wannan hadisin kai tsaye ya nuna mana haramcin gulma!_
.
_Kai wallahi ina sanar daku illar gulma, cewa imanin dayanku baya inganta har sai mutum ya kiyaye harshen sa, 'yan uwa kada kuga kamar maganar tayi girma, akwai hadīsī acikin Musnad na Imam Ahmad duk da wasu malaman Hadīsai sun raunata Hadīsin, hadisi ne na Anas Allah ya kara masa yarda yace Annabi Saw yace "Imanin bawa baya dai-dai tuwa har sai ya dai-daita zúciyar sa, to amma fa kusani zúciyar bawa bata dai-dai tuwa dole sai ya kiyaye harshen sa" akwai wani hadisi wanda ya inganta Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya kira magulmata da cewa "Yaku wadanda sukayi Imani da Harshen su alhali zuciyar su batayi Imani ba? Sai Annabi yace sune wadanda suke yin Gulmar 'yan uwa, kuma suke wulakanta su_
.
_'Yar uwa kinji fa wadanda sukayi Imani da harshen su amma Zuciyoyin su basuyi imani ba sune magulmata! To mu yanzu yaya muka dauki gulma, kamar yanda na fada maku cewa wallahi hatta wadanda suka siffantu da Ilimi acikin mālamai akan samu magulmata acikin su, 'yan uwa sai daifa mu nemi tsarin Allah, wallahi gulma tana da hatsari, kai wallahi bari kuji aljannah dakan ta ta'allaqa ne ga masu kiyaye harshe akwai Hadīsai acikin Bukhari da Muslim Annabi saw yace "Na lamince Aljannah ga duk wanda ya kiyaye harshen sa da kuma abinda yake a tsakanin cinyoyin sa (wato Al'aura)" kunji kenan idan muka dauki wannan hadisin zamu fahimci cewa ashe ita kanta Aljannah mutum bazai sameta ba har sai ya kiyaye harshen sa,_
.
_' Yan uwa ga wani hadisi mai tsoratarwa da yazo acikin Sahīhul Bukhari Hadīsi na 6477 da kuma Muslim Hadīsī na 2988 hadisin Abu-Hurairah Allah ya kara masa yarda yace Manzon Allah saw yace "Lallai mutum zaiyi tayin wata magana da wata kalma wacce baisan hatsarin dake cikin ta ba, bazai gushe ba sai wannan kalmar tayi sanadin shi na shiga wutar jahannama yana mai dawwama acikin ta wacce tsawon inda za'a saka shi yakai nīsan da yake tsakanin gabas da yamma" wannan hadisin yana cikin littafin Jāmi'ul-Ulūm Wal-Hikam shafi na 217 karkashin sharhin hadīsī na 15, to 'yar uwata yaya matsayin gulmar abokiyar zaman mu da muke yi bayan mun sani Allah ya haramta gulma!?_
.
_Sannan Akwai wani Hadīsi da Imam Tirmidī ya ruwaito acikin Sunan a babin Zuhdu hadisi na 2314 Annabi saw yace "Lallai mutum zaiyi tayin magana da wata kalma shi a wajenshi wannan maganar da yake yi babu wani abu na laifi, a haka yake daukar kalmar ta sanadin wannan kalmar sai a jefashi acikin wuta wacce nīsan ta yakai tsawon shekara saba'in 70" hadisi ne ingantacce daga Abu-Hurairah, don haka nefa Annabi yace koda ace laifin dan uwanka ne ka ambata to kayi gulma,!_
.
_Zamu dakata anan sai mun hadu a darasi na gaba_
.
*Hussaini Ibnu Taimiyyah Kuriga*
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp

0 comments:
Post a Comment