Daga Rabi'u Maiwaya Limawa
1. SHAHADA: Ya yi Shahada iri daya da ta Sayyidina Umar (R.A)
2. Ya rasu ranar Juma'a: Rasuwar Ranar Juma'a alama ce da ake kyautata wa Mutum zato ya samu dacewa.
3. Mahaddacin Alkur'ani ne: Ana kyautata zaton duk wanda ya haddace Alkur'ani Mai Girma ya kuma kiyaye shi ya yada shi. Zai samu rabauta ranar Lahira.
4. Kisan Gilla: Duk Muminin da aka yi wa kisan gilla ana sa ran laifukan sa sun rataya a wuyan wanda ya kashe shi.
5. Ya cika da kalmar SHAHADA: Kafin rasuwar sa an ji shi ya na maimaita kalmar La ila ha illallah Muhammadur Rasulullah
6. Dandazon Mutanen da suka halarci jana'izarsa: Ana kyautata zaton duk mamacin da mutane 40 suka halarci jana'izarsa wadanda ba sa shirka zai samu dacewa.
7. Ya rasu ya na Sallar Asuba. Sallar Asuba na daya daga cikin Sallah mai madaukakiyar daraja.
8. Limami ne shi: Jagorancin Sallah wata babbar baiwa ce da ke kusanta Bawa zuwa ga Allah.
9. Ya Karanta Suratul MA'ARIJ: Kafin a kai ga kashe shi ya karanta sura daga cikin Alkur'ani Mai Girma.
9. Ya Karanta Suratul MA'ARIJ: Kafin a kai ga kashe shi ya karanta sura daga cikin Alkur'ani Mai Girma.
10. Ya Dago Daga SUJADA: Sai bayan da ya dago daga sujada sannan makisan sa suka fara harbin sa.
11.Ya Nemi Gafarar Mutane Kafin Rayuwar sa. (Duk wanda na yi wa ba daidai ba don Allah ya yafe min).
Ya Allah Ka amshi shahadar Malam Mu kuma Allah Ya azurta mu da yin shahada.
0 comments:
Post a Comment