GA WASU HANYOYI GUDA SHIDA WADANDA ZAKA IYA BINSU DON GYARA HALAYENKA ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Saturday, 23 September 2017

GA WASU HANYOYI GUDA SHIDA WADANDA ZAKA IYA BINSU DON GYARA HALAYENKA

GA WASU HANYOYI GUDA SHIDA WADANDA ZAKA IYA BINSU DON GYARA HALAYENKA :

1. Cikakken imani na gaskiya tare da yawaita neman kusanci da Allah ta hanyar aikata dukkan abinda zai janyo kusancinka dashi. Ta hanyar kwatanta yin haka ne zuciya take samun kaifi, Kuma mutum yake samun saukin suluki (tafiya) bisa hanyar neman yardar Ubangijinsa.

2. - Zama tare da kulla abota da mutanen kirki masu kyawawan halaye. Domin kuwa abokai suna taka muhimmiyar rawa acikin tarbiyyar abokansu ta fuskar Mu'amala da kuma zama yau da kullum.

Shi yasa malamai suka ce ''Shi aboki mai jan abokinsa ne. Idan shi na kirki ne zai jashi zuwa alkhairi. Idan kuma shi na banza ne, to zai ja abokinsa ne zuwa ga sharri.

Wani Malami ya fa'da acikin waqa : "Kar ka tambaya game da halin mutum, Kai dai ka tambayi su waye abokansa?. Domin kowanne aboki yana koyi ne da abokansa".

3. Hanya ta uku ita ce : Ka rika yiwa kanka hisabi domin ita zuciya bisa hakikanin gaskiya an halicceta ne bisa dabi'ar yin umurni da munanan abubuwa. Kuma ita zuciya kullum kokarinta shine ta jaka zuwa ga sharri.

Don haka ka rika tuhumar zuciyarka kana yi mata hisabi kuma kana janta zuwa ga alkhairi. Kar ka zama mai binta duk inda ta jaka kamar jela, tana janka zuwa ga bin son ranta.

Imam Busiriy yace "Ita zuciya kamar Jariri take. Domin shi jariri idan ka kyaleshi kaci gaba da shayar dashi, sai ya girma bai dena son shan nono ba. Amma idan ka yayeshi shikenan sai ya yayu".

4. Na hudu shine : Ka yawaita jarraba aiki da kyawawan halaye madaukaka irin su Hakuri, juriya, Tawadhu'u, kyauta, biyayya, gaskiya, amana, sakin fuska, etc.

Alokaci guda kuma ka rika kokarin kauce ma miyagun halaye irin su Qarya, girman kai, rowa, ha'inci, taurin kai, riko, gaaba, hassada, etc.

Shi yasa Manzon Allah (saww) yace : "SHI ILIMI ANA SAMUNSA NE DA NEMAN ILIMI. SHI KUMA HAKURI DA HAKURKURTAR DA RAI".

5. Hanya ta biyar ita ce: Ka rika karanta tarihin magabata na kwarai kana jin yadda sukayi rayuwarsu cikin neman yardar Allah da guje ma sa'ba masa.

Domin karanta tarihinsu wata babbar hanya ce muhimmiya ta gyaran halaye domin zaka ji labari daga manyan Maluma wanda acikinsa zaka ji yadda halayensu da ladubansu yake.

6. Hanya ta shida ita ce: ka rika rokon Allah cewa ya baka kyawawan halaye, kuma ya rabaka da miyagun halayen dake tare da kai.

Yin wannan yana daga cikin manyan hanyoyin da zasu kaika zuwa ga kyautatuwar halaye.

Daga cikin addu'o'in da Manzon Allah (saww) yake yi akwai wacce yake cewa:

"YA ALLAH KA SHIRYAR DANI ZUWA GA MAFI KYAWUN HALAYE. DOMIN BABU MAI SHIRYARWA ZUWA GA MAFI KYAWUNTA SAI DAI KAI.

"KUMA KA JUYAR DA MAFIYA MUNINTA DAGA GARENI. DOMIN BABU MAI JUYARWA DAGA MAFI MUNINTA SAI DAI KAI".

Ya Allah muna Tawassuli da mafi kyawun halaye da dabi'u acikin bayinka don alfarmarsa ka kyautata halayenmu. Ka kiyayemu daga miyagun halaye.

DAGA ZAUREN FIQHU (06-08-2016).


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support