MU NISANCI TSINUWA DA LA'ANTAR YAN UWANMU
*Darasi na farko-1*
Abinda ake nufi da la'anta ko tsinuwa shine:-
*"Addua da fatan Allah ya nisantar da mutum daga rahamarsa,da fatan halaka da masifa a gareshi tare da fatan fishin Allah ya tabbata a gareshi"*.
Duk lokacin da ka ce Allah ka la'anci kaza ko wane,ko Allah ka tsinewa wane albarka,kana nufin Allah ya nisantar da shiga daga Rahamarsa ya kuma tabbatar da shi acikin Halaka da mafisa tare da haramta masa rahaam.
Wannan yasa Manzon Allah s.a.w yake gargadin mu da munisanci la'anta da yin tsinuwa ga yan uwanmu da dukkan sauran halittun Allah baki daya.
*DAGA CIKIN ILLOLIN LA'ANTA DA TSINUWA*
Manzon Allah s.a.w ya fadi illa da la'anta da tsinuwa suke janyowa mutum,ga kadan daga cikinsu;-
1-ILLA TA FARKO
*"La'antar abu da tsine masa,kamar kisan sane*
Manzon Allah صلى الله عليه وسلم yana cewa;
*(.......Kuma dukkan wanda yake La'antar mai Imani,kamar kisansane)*.
@صحيح الإمام البخاري - ٥٧٠٠ ،صحيح الإمام مسلم -
Ma'anar kamar kisansane shine;
"La'antarsa kamar yana yi masa adduane da halaka da tabewa".
@فتح الباري - ١٠/٤٨٢ ) ].
2-ILLA TA BIYU
*"Mai yawan La'anta baya zama daga cikin masu bada Shaida da kuma masu ceto a gobe alqiyma*.

*(Lallai masu yawan la'anta da tsinuwa,basu cikin masu bada shaida kuma basu cikin masu yin ceto a gobe alqiyama)*
@صحيح الإمام مسلم - ٥٧٠٠
3-ILLA TA UKKU
*Yawan la'anta da tsinuwa yana cikin abubuwan da suke saurin kai mutum shiga wuta*.

*(Yaa ku taron mata, Lallai ku yawaita yin Sadaka domin naga mafi yawa daga cikin ku acikin wuta)*,"sai suka tambaye shi saboda me,sai yace;
*(Saboda kuna yawan la'anta da tsinuwa kuma kuma kafircewa mazajen auranku....)*
@صحيح الإمام البخاري - ٣٠٤ ، وأخرجه الإمام مسلم في صحيحه بنحوه من حديث ابن عمر رضي الله عنهما - ٨٠ ].
4-ILLA TA HUDU
*La'anta da tsinuwa laifine babba daga cikin manyan zunubai*
Daga Salmatu bnul Akwa'i رضي الله عنه yana cewa;
*"Mu sahabbai mun kasance idan muka ga mutum yana la'antar dan uwansa to muna ganinsa ya bude wata kofa daga cikin kofofin manyan zunubai"*
@المعجم الأوسط - 6849 ، وإسناده جيد.
5-ILLA TA BIYAR
*La'anta da tsinuwa haramunne*.
Imam Nawawy Allah yayi masa Rahama yana cewa;
*"Malamai sun hadu akan la'anta da tsinuwa haramunne"*.
@شرحه على مسلم - ١/٢٥٠
6-ILLA TA SHIDA
*Yawan la'anta baya cikin siffar mai Imani*

*(Mai Imani baya sukar dan uwansa kuma baya la'anta da tsinewa dan uwansa,kuma mai Imani baya alfasha kuma baya mugunta)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ ﻋﻦ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﻦ ﻣﺴﻌﻮﺩ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ ــ ﻛﺘﺎﺏ ﺍﻟﺒﺮ ﻭﺍﻟﺼﻠﺔ ﺑﺮﻗﻢ 1900 ( ﺻﺤﻴﺢ )ﺍﻧﻈﺮ ﺣﺪﻳﺚ ﺭﻗﻢ : 5381 ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ
7-ILLA TA BAKWAI
*Mai la'anta da tsinuwa bai kiyeye wasiyyar Manzon Allah ba*.
Daga Sahabi Jurmuzal Hajimy R.A yana cewa,nace Ya Manzon Allah kayi min Wasiyya,sai yace;
*(Ina yi maka wasiyyar kada kazama mai La'anta)*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ ــ ﻣﺴﻨﺪ ﺍﻟﺒﺼﺮﻳﻴﻦ ﺑﺮﻗﻢ 19757 ﺻﺤﻴﺢ ) ﺍﻧﻈﺮ ﺣﺪﻳﺚ ﺭﻗﻢ : 2542 ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ
Allah ne mafi sani.
Mu hadu a Darasi na gaba insha Allah.

0 comments:
Post a Comment