***************006*******************
MEYE YA HARAMTA GA MAI JININ HAILA DA KUMA JININ HAIHUWA?
***************************************
Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, 'yan uwa barkan mu da wannan lokaci tare da fatan kuna cikin koshin lafiya, a yau cikin wannan rubutu da zauren SA'ADATUL-MUSLIM yake gabatar wa in shaa Allah acikin wannan fitowa ta shida din zaiyi mana bayani ne akan ababen da suka zama haramun ga mace wacce ta kasance tana yin jinin haila da kuma mace wacce ta haihu wato jinin biiqi, Allah ta'ala muke roko ya taimake mu kuma ya kar6a mana kuma ya bamu ikon rubuta dai dai kuma ya taimake mu wajen yin riko da gaskiya, Allah yasa Mudace,
.
1 SALLAH DA AZUMI:- Bai halatta ba ga mace wacce take acikin kwanakin jinin haila (wato tana yin jinin haila) ko kuma wacce take acikin kwanakin jinin haihuwa (wato tana yin jinin biiqi) su dika yin sallah ko kuma su dika yin azumi saboda hadisin da Bukhari da Muslim suka ruwaito daga Abiy-Sa'eed Al-Khudriy Allah ya kara masa yarda yace, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace, "Ashe baku san idan mata suna yin jinin haila basu yin sallah kuma basu yin azumi ba?" Muslim hadisi na 79 Bulughul-Maram shafi na 71 hadisi na 158, Fiqhul-Muyassir na Sa'ad Yusuf shafi na 55,
.
Amma idan suka samu tsarki daga jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) to bazasu rama sallah ba amma dai zasu rama azumi domin kuwa hadisi yazo acikin Bukhari da Muslim daga A'isha Allah ya kara mata yarda tace "Lallai mu mun kasance muna yin jinin haila a zamanin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi kuma ya kasance Annabi yana yi mana umarni cewa mu rama azumi, amma kuma baya umartan mu cewa mu rama sallah" (duba Fiqhul-Muyassir shafin da mukayi ishara dazu)
.
2 `DAWAFI A DAKIN KA'ABA:- Baya halatta ga mai jinin haila ko jinin biiqi tayi d'awafi a dakin ka'aba saboda hadisin da Bukhari da Muslim suka ruwaito daga Uwar Muminai A'isha Allah ya kara mata yarda tace "Lokacin da muka isa Sarifa sai haila ta sameni, sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace "Ki aikata dukkanin abinda mai aikin hajji yake aikatawa sai dai banda d'awafi ga dakin ka'aba har sai kinyi tsarki" Muslim hadisi na 1211 duba Bulughul-Maram hadisi na 159 duba Fiqhul-Muyassir shafin da mukayi ishara dazu,
.
3 SADUWA DA ITA (TA FARJI):- Haramun ne saduwa da mace alhali tana yin jinin haila ko jinin biiqi (haihuwa) kuma Gaskiya dalilai akan haramcin haka suna da yawa amma dai in shaa Allah a fitowa ta 007 zamuyi bayani ne akan wannan matsalar ta 3 tare da maganganun malamai da hujjoji daga Al-Qur'ani mai girma don haka 'yan uwa a saurare mu a rubutu na gaba, Assalamu Alaikum warahmatullahi wabarakatuh,
.
Hussaini Haruna Ibn Taimiyyah Abu-Nabeelah Kuriga
.
**16/10/1438**
.
→ A yanzu haka zaku iya bibiyar zauren SA'ADATUL MUSLIM ta shafin sada zumunta dake Facebook ta cikin wannan link din
https://free.facebook.com/Saadatul-Muslim-Islamic-Group-Chat-1017855871594468/?ref=opera_speed_dial_freefb
.
→ Ga masu sha'awar shiga zauren SA'ADATUL MUSLIM sai su aiko da cikakken Suna da adreshi izuwa ga numbar mu +2348052975857 ta whatsapp
0 comments:
Post a Comment