*MU KYAUTATAWA JUNA ZATO*
*_WANI DAGA CIKIN SALAF (MAGABATAN FARKO NA KWARAI) YANA CEWA:_*
_*Idan naga ruwan giya suna zubowa daga gemun mutum, to zance giyar ta zubar masa ne*_ Wato abinda yake nufi anan tunda dai bai ganshi yana shan giyar ba a zahiri ba to lallai ba zaice ya ganshi yana shan giya ba.
*HAKA KUMA YA QARA DA CEWA:*
*_Haka kuma idan na ganshi a saman tsololuwar tsauni yana cewa_; " *NI NE UBANGIJINKU MAFI DAUKAKA* " ( *ANA RABBUKUMUL A'ALA* ). *_Anan kuma zance wannan yana karanta_* *AYA CE DAGA AL-QUR'ANI MAI GIRMA*
Kaji *swalihan* bayi kenan, duk fa wannan yana yine akan tsananin kyautatawa musulmi zato, yi masa uzuri da kuma gujewa yin shaidar zur.
Yanzu mutanen wannan zamanin wa zaiga giya na zuba daga gemun mutum yace wai ba giyar ce ya gama sha ba? Haka kuma wa zai ga mutum saman qololuwar tsauni yana kwala ihu yana fadar *_NI NE UBANGIJINKU MAFI DAUKAKA_* Har yace bawai kansa yake kira Allah ba, ai ayar qur'ani ce yake karantawa?
Kuma wannan itace dabi'ar da ake son musulmai su dabi'antu da ita ta kaucewa yin shaidar zur, kyautatawa juna zato da kuma gujewa munanawa musulmi zato kamar yanda dimbin ayoyin Al-qur'ani da ingantattun hadisai suka hore mu.
*Allah ya bamu ikon kyautatawa junanmu zato. Ameen*
*TAMBAYOYIN MUSULUNCI*

0 comments:
Post a Comment