Sahabbai manyan bayin Allah ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Thursday, 28 September 2017

Sahabbai manyan bayin Allah

*SAHABBAI MANYAN BAYIN ALLAH*

✍🏼 Rubutawa:
*_Malam Misbahu Saminu Madabo_*
26/09/2017.

Sune Qur'aani yake sauka ga Manzon Allah(saw) suna tare dashi.

 Idan basu fahimci hukunci ba,su tambaye shi ya basu amsa.

Idan Allah zai magana dasu ko magana akan su,sai yace dasu:

"ياايها الذين ءامنوا".

Suna zama da Annabi(saw) suci  Abinci,su sha abin sha tare,su Aura su kuma Aurar masa,suka kuma je dukkan Yaqi tare dashi,yana jagorantar su a Sallah da sauran ayyuka.

Kawai kai saboda kasa baqaqen kaya kana yawon banza a tituna,ko cikakkiyar magana ta minti 3 ba zaka iya ba da harshen Qur'aani(Larabci),sai iskanci da Mata da sunan Mut'ah.

Amma a hakan Shaidan yayi maka Khudubar wai kafi wa'yancan Imani da tsoron Allah,har ma kana Zagin su kana tsine musu.

Ke kuma qazama,kina wari saboda bin tituna ba wanka,amma a haka kike ganin wai kinfi Matan Manzon Allah(saw) da Matan Sahabbai(ra) imani da son Allah da Manzon sa(saw),saboda kawai Maza sun rarake ki da sunan Mut'ah.

Allah ka raba mu da shirme,iskanci da rashin mutunci da rashin hankali na Shi'a da 'yan Shi'a.

Allah ka kare mu ka kare imanin mu dana Zuriyar mu daga 6ata da ta6ewa!!!!!

Daga: *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support