DUK LOKACIN DA KA SHIGA CIKIN TSANANIN WAHALA DA KUMA DAMUWA, KAR KA MANTA DA ABUBUWAN NAN GUDA BAKWAI ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Thursday 14 September 2017

DUK LOKACIN DA KA SHIGA CIKIN TSANANIN WAHALA DA KUMA DAMUWA, KAR KA MANTA DA ABUBUWAN NAN GUDA BAKWAI

DUK LOKACIN DA KA SHIGA CIKIN TSANANIN WAHALA DA KUMA DAMUWA, KAR KA MANTA DA ABUBUWAN NAN GUDA BAKWAI:
******************************

Rubutawa: *Sheik Aliyu Said Gamawa (Hafizahullah)*

1⃣. Ka tuna cewa Jarrabawa ce daga Ubangininka, wanda yafi kowa Sonka da Kaunarka.

2⃣. Ka tuna cewa Ubangijinka yayi maka haka ne don ya Kankare maka
Zunubanka, ko kuma ya daukaka maka darajarka.

3⃣. Ka tuna cewa an jarrabi Annabawa da Manzanni da Salihan bayin Allah wadanda suka zo kafin ka.

4⃣. Ka tuna cewa Tun kana cikin mahaifiyarka kafin ta haifeka an riga an rubuta maka duk abinda zaka samu aduniya, da kuma dukkan abinda zai sameka. Mai dadi ko Kishiyarsa.

5⃣. Ka tuna cewar rungumar Qaddara kowacce iri, yana daga cikin Ginshikan Imaninka. Gwargwadon yadda kake rungumar Qaddara, gwargwadon haka imaninka yake.

6⃣. Ka tuna cewar kowanne tsanani yana tare da sauki guda biyu. (Ga lada, ga kuma yayewar tsananin).

7⃣. Ka tuna cewar Allah shine ARHAMUR RAHIMEEN (MAFI TAUSAYIN MASU TAUSAYI) kuma yafi komai kusa dakai, Kuma yafi kowa tausayinka. Kuma zai amsa
dukkan rokonka.

Ya Allah ka yaye mana dukkan Tsanani don Rahamar nan taka wacce ta yalwaci dukkan halittunka.

Ameen summa amin.

Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support