HALAYEN MASU TSORON ALLAH (09) Zauren fiqhu ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Friday, 8 September 2017

HALAYEN MASU TSORON ALLAH (09) Zauren fiqhu

HALAYEN MASU TSORON ALLAH (09)
***************************************
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

Da sunan Allah rayayyen da ya raya dukkan rayayyu, Kuma rayayen dake dawwama bayan gushewar dukkan kasantattu.

Salati da aminci su tabbata bisa Annabin da Allah ya aikoshi domin raya zukatan da suka mace, Annabinmu Muhammadu tare da iyalan gidansa da dukkan Sahabbansa da mabiyansu har zuwa ranar sakamako.

Wannan shine Kashi na tara (09) acikin darasin Zauren Fiqhu mai taken "HALAYEN MASU TSORON ALLAH". Kuma acikinsa in sha Allahu zamu ci gaba da jin irin yadda magabata na kwarai suka tarbiyyantar da zukatansu wajen tsananin tsoron azabar Allah da kuma kwadayin rahamarsa.

Daga cikin Magabata akwai wadanda ko dariya basu yi arayuwarsu saboda tsananin tsoron azabar Allah.

Watarana Hajjaju bn Yusuf (wani azzalumin Gwamna ne) ya kira babban Malamin nan na garin Madeenah mai suna Sa'eed bn Jubayr yana tuhumarsa kamar yadda ya saba yiwa Maluma.. Yace masa "Na samu labarin cewa wai kai baka ta'ba yin dariya ba tunda kake?".

Sai Sa'eed bn Jubayr din yace masa "Ta yaya zan iya yin dariya alhali ga Jahannama chan an kunnata, ga turakun azaba nan an kafasu, ga kuma Zabaniyawa nan an tanadesu?".

Shi kuwa Gazwaan (rah) watarana anyi gobara agidan makwabtansa sai yaje domin kashe Wuta. Agarin haka sai wani garwashi ya Qona masa yatsansa. Da yaji zafi sai yace "Tunda har Wutar duniya ta Qonani naji zafi, to daga yau ba za'a Qara ganin dariyata ba har sai na san shin an tseratar dani daga azabar Allah ne ko A'a?".

'Yan uwa kunji fa masu yi da gaske.. Hakika daga cikin magabata akwai wadanda sukayi ma Allah alkawaein cewa mutukar suna raye ba za'a ta'ba ganin dariyarsu ba. Wato sai alahira bayan sun karbi sakamakonsu mai kyawu.

Daga cikinsu akwai Jum'atud Dusiy, Rabee'u bn Khuraash da Dan uwansa Rub'eey bn Khuraash, Aslam Al'ijly da Wuhaibu bn Alwardi, da shi kansa Sa'eed bn Jubayr da sauransu.

Yazeedur Raqqashiy ya ruwaito daga Sayyiduna Anas bn Malik (ra) cewa lokacin da Manzon Allah (saww) yaje Isra'i suna tare da Mala'ika Jibreelu (as) sai Manzon Allah (saww) yaji wata Qara mai tsanani..

Sai ya tambayi Mala'ika Jibreelu (as) "YA JIBREELU WANNAN WACCE IRIN QARA CE?"

Sai Mala'ika Jibreelu yace "WANI DUTSE NE ALLAH YA JEFOSHI DAGA GEFEN (GA'BAR) WUTAR JAHANNAMA,  DUTSEN YANA TA WULWULOWA TSAWON SHEKARU SABA'IN ACIKINTA. SAI YANZUN NAN YA KAI QARSHEN QASAN ZURFINTA".

Anas (ra) yace Tun daga nan Manzon Allah (saww) bai sake yin dariya ba, sai dai murmushi".

(Ibnu Abid dunya ne ya ruwaitoshi. Imam Tabaraniy ma ya ruwaito irinsa daga Sayyiduna Abu Sa'eed Alkhudriy (ra) shima akarshen hadisin yake cewa "Manzon Allah (saww) tun daga wannan ranar bai sake yin dariya ba, har Allah ya karbi ransa".

'Yan uwa kunji fa zurfin Jahannama.. An jefa dutse daga bakinta amma sai bayan shekaru saba'in kafin dutsen ya isa Qasanta!! (INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN).

Amma fa Ubangiji yayi rantsuwa cewa sai ya chika cikinta fal da Aljanu da Mutane!! SUBANHALLAH!!!

Sayyiduna Abu Dharr Algifariy (ra) yace "Nace Ya Manzon Allah (saww) shi menene acikin litattafan Annabi Musa (as)?

Sai yace "Ta kasance gaba dayanta Misalai ne gaba dayanta. :

- INA MAMAKIN WANDA YA TABBATAR DA CEWA MUTUWA GASKIYA CE. AMMA KUMA HAR YANA FARIN CIKI..

- KUMA INA MAMAKIN WANSA YA TABBATAR DA CEWA WUTA GASKIYA CE. ALHALI KUMA YANA DARIYA..

(Ibnu Hibban ne ya ruwaitoshi).

Lallai 'yan uwa akwai babban aiki agabanmu. Dole ne mu rika kokarin dawo da zukatanmu kan hanya, hanyar tunanin lahira. Mu dena shagaltuwa wajen gyara duniya ka'dai. Domin ita duniya ba matabbata bace.

Lallai wauta ta tabbata ga wanda ya tabbatar cewa Azabar Allah gaskiya ce amma bai gije mata ba..

Lallai Dimaucewa ta tabbata ga wanda ya tabbatar cewa duniyar nan ba matabbata bace, amma ya riketa ita ce abar nemansa koma-bayan lahirarsa.

Lallai rashin nutsuwa ta tabbata ga mutumin da yake jinkirta tuba alhali bai san yaushe ne mutuwarsa ba..

Ya Allah ka karbi tubanmu ka kyautata ayyukanmu, ka gyara zukatanmu ka Qara mana himma da kwazo wajen neman lahirarmu.

Anan zamu tsaya sai a darasi na gaba zamu dora daga inda muka tsaya. In sha Allahu.

Anan nake miko sakon Ta'aziyyah zuwa ga Daliban Zauren Fiqhu Whatsapp game da mutuwar daya daga cikin Dalibanmu wato Alhaji Bala Ali Kila (Bala Mai Ji) wanda Makobcina ne kuma Muna tare dashi tun lokaci mai tsawo.

Ya rasu ne aranar asabar din da ta gabata, Sakamakon jinyar Asthma dake tare dashi. Muna addu'a tare da fatan Alah ya jikansa ya gafarta masa, ya albarkaci zuriyar da ya bari. Mu kuma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da imani. Ameeen.

An gabatar da karatun a Zauren Fiqhu Whatsapp ranar (03-05-2017). Kuma an hada karatun tare da taceshi aranar 06-05-2017. 07064213990.


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support