*SHIN WATANNI NAWA MIJI ZAI IYA KAURACEWA MATARSA TA SUNNA ?*
*Tambaya:*
Assalamu alaikum Tambaya ita ce؛ shin Tsawon wani lokaci ne ya halatta miji ya kaurace wa matar shi ta sunna kuma wani Mataki ya dace ta dauka in har ya wuce period din da sharia ta halatta?.
*Amsa:*
Wa'alaykumussalam, Ya halatta ya kaurace mata tsawon watanni hudu kamar yadda Allah ya fadi a suratul Bakara aya ta: 226.
Bai halatta ya wuce hakan ba, in ya koma da kansa ya cigaba da saduwa da ita to Allah mai gafara ne game da abin da ya wuce, in har ba zai koma ba bayan watanni hudu sai ya sake ta kamar yadda aya ta 227 a cikin surar ta nuna hakan.
In ya ki komawa ya sadu da ita kuma ya ki saki sai taje wurin Alkali don ya bashi zabi tunda wata hudu ya cika ko ya dawo mata ko kuma ya sake.
Allah ne mafi Sani
✍🏼 *Amsawa:*
*_Dr Jamilu Yusuf Zarewa_*
10/02/2017
Daga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH*

0 comments:
Post a Comment