Yaduwar bin bokaye!!? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Tuesday, 7 November 2017

Yaduwar bin bokaye!!?

```YADUWAR BIN BOKAYE```
~~~~~~~~~~~~~~~~


_Godiya ta tabbata ga Allah, kuma tsira da amincin Allah su tabbata ga manzon Allah da mutanen gidansa, da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsa._
.
.
_Bayan haka wani abun takaici dake faruwa shine yadda zaka ga da yawa daga cikin matayen arewacin Nigeria sun jefa kansu a cikin mummunar hallaka ta sanadiyyar bakin kishi akan kishiya. Wasu mata saboda tsabar bin bokaye da 'yan duba da 'yan bori har su kansu ma sun zama matsafa qarfi da yaji, wasu kuma sun zama mazinata, suna zuwa suna zina da bokaye domin samun biyan miyagun bukatunsu._

_Akwai wasu Qawaye masu bin bokaye da faɗa ya tashi a tsakaninsu, suna yiwa juna gori sai wata tace ma ɗayar, ai yaron da kike goye dashi kema kin san ba ɗan mijinki ba ne, ɗan gidan boka wane ne. Haka dai suka rika tona ma juna asiri._

_Wasu kuma sun talauce su lalace, duk abun hannunsu ya qare saboda bin bokaye, wasu kuma addinin na su da imaninsu ma duk sun lalata, sun fi imani da maganar bokaye fiye da maganar Ubangijin su._

_Amma sai naga mafi yawan masu tofa albarkacin sunfi alaqanta abun da jahilci, ko duhun kai, alhali kuma gaskiya abun ba haka bane_

_A yanzu zaka tarar da mafiya yawan masu bin bokaye din nan, mataye ne wayayyu, 'yan boko masu aji, waɗanda ake ganin kamar kansu yaji gishiri. Kuma zaka tarar mafiya yawansu suna zuwa Islamiyyan ballantana ace basu san haramcin abun bane._

_Kuma matsalar tafi aukuwa a tsananin matayen Attajirai, 'yan siyasa da masu mulki, da sauran masu hannu da shuni. Amma yawancin matan talakawa suna fama da abin da zasu ci, koda suna son bin bokaye basu da bayarwa._

_Irin wannan harkar ta bokanci da tsafe-tsafe ta shigo har cikin kafofin sadarwa na yanar gizo wato (social media) kamar su whatsapp da Facebook. Yanzu haka akwai groups da pages da suke tallata wani abu wai shi *(Goron Tula)* wai wani abu ne wanda idan mace tayi amfani da shi, mijinta zai rikice wajen kaunarta har sai ya rabu da dukkan matansa, wai har kyautuka zai rika yi mata don dolensa!.._

_Dasu turaren jan hankali maza, da na korar kishiya da dai sauran su. Kuma matan dake wannan Sana'a r kullum sai kara yawa sukayi, kuma basu 6oye ma kowa abin da sukayi.._

_Abinda muke so mata su gane shine: bokanci ko harka da boka, ko amfani da kayan bokanci, duk haramun ne, kum hukuncin masu yinsa shine kafirci._

_Idan kikaje wajen boka kuma kika gaskatashi kin kafirce kenan, kuma ba zaki gane cewa ke kafira bace sai lokacin mutuwarki (sanda bubu lokacin tuba)_.

_Idan kika je lahira babu imani, to fa babu wata alfarmar da zaki samu a wajen Allah. Babu ceto gare ki, babu fita daga wuta, babu shiga Aljannah, babu shan ruwan Alkausara._

_kuma maganin mallakar miji ba zai mallaka miki tsarkakakkiyar soyayyarsa ba, kuma ba zai janyo miki samun soyayyar Allah ba, balle cikawa da imani._

_Duk wulakanci ko bambancin da kike gani agidan mijinki, to kiyi hakuri kiyi addu'a shine mafita, Allah ne yake juya al'amura ba boka ko malamin duba ba._

_Imaninki shine babban jarinki Aduniya da lahira, idan kika rasashi kin afka cikin talaucin da ba zaki sake yin arziki ba. Har abada. Allah ya tsare mana imaninmu._
=
=
Allah Ta'ala yasa mudace.
=
=
```DAN UWANKU HAR KULLUM ```:
IBrahim Abubakar Hamza




Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support