Monday, 24 June 2019
Home »
» WACCE TA SHA MAGANIN HANA DAUKAR CIKI, IDDARTA JINI UKU CE!
WACCE TA SHA MAGANIN HANA DAUKAR CIKI, IDDARTA JINI UKU CE!
Tambaya
Assalamu alaikum, don Allah mal. mace ce aka saketa ta yi tsarki sai ta sha maganin hana daukan ciki sai ya zama wata uku(3) ba jini, shin da wata za ta yi iddah ko da jini?
*Amsa*
Wa alaikum assalam, Za ta jira jini uku, ko da kuwa za ta yi shekara goma ne, kamar yadda Allah ya fada a aya ta (228) a suratul Bakara.
Allah ne mafi sani
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
18/06/2019
0 comments:
Post a Comment