Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Thursday, 9 November 2017

Jinazah Ba Guri Ba Ne Na Gabatar DaHuduba Ko Yi Wa Jama'a Wa'azi Har Kullum :Dr Ibrahim Jalo Jalingo

1. Sunnah ce lokaci zuwa lokaci a sami wani wanda zai fadakar da wadanda suka halarci binne mamaci, amma ba zai dace da Sunnah ba a maida wa'azin tamkar wata lacca, ko a riki yin wa'azin a matsayin wani al'amari raatibi wanda sai an yi shi cikin ko wace jinazah.

2. Akwai hadithai biyu da suka tabbatar da cewa har sau biyu ne Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya yi wa Sahabbai jawabai na wa'azi -ba bisa siffar huduba ba- a inda ake binne wani mamaci. Hadithin farko shi ne wanda Aliyyu Bin Abi Dalib ya ruwaito kamar yadda ya zo cikin Sahihul Bukhariy Hadithi na 1362, da Sahihi Muslim Hadithi na 2647. Hadithi na biyu shi ne wanda Baraa Bin A'azib ya ruwaito kamar yadda ya zo cikin Musnad Ahmad Hadithi na 18534.

3. Kyamatar maida gurin binne mamata wurin yin jawabai masu kama da lacca, da kuma maida hakan al'amari raatibi da ake maimaitawa a duk lokacin da aka zo binne wani mamaci tabbas shi ne yake dacewa da abinda Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya zo da shi, shi ne kuma fahimtar da yawa daga cikin Malamanmu na Sunnah; kamar Sheikh Muhammad Bin Salihil Uthaimeen da wasunsa.
Allah Ya taimake mu Ya dora mu a kan yin daidai har kullum. Ameen.
Share:

Wednesday, 8 November 2017

Maganar Annabi Ta Yi Hannun Riga Da Maganar 'Yan Shi'ah Game Da Aisha Dr Ibrahim Jalo Jalingo


Maganar Manzon Allah mai tsira da amincin Allah game da Matarsa Nana A'isha Allah Ya kara mata yarda ta yi hannun riga da maganar 'yan Shi'ah masu muzanta ta da cin mutuncinta; wannan shi ne ya sa a lokacin da su batattun 'yan Shi'ah suke kafirta ta, suke la'antar ta, a lokacin ne kuma ita Shari'ar Musulunci ta bakin da ba ya karya watau Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ke siffanta ta da cewa ita Ahlul Baiti ce!

Imamul Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 2637, da Imamu Muslim hadithin na 2770, da Imam Ahmad Hadithi na 25,664, da Imamul Baihaqiy Hadithi na 20,386 cewa: A lokacin da Jama'ar da  suka yi wa Nana A'isha kazafi da sharrin cewa ta yi zina, sai Manzon Allah mai tsira da amincin Allah:-
((فدعا عليا واسامة حين استلبث الوحي يستامرهما في فراق أهله، فاما اسامة فقال: اهلك ولا نعلم الا خيرا. وقالت بريرة: ان رأيت عليها أمرا اغمصه اكثر من انها جارية حديثة السن تنام عن عجين اَهلها فتاتي الداجن فتأكله. فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: من يعذرنا من رجل بلغني أذاه في اهل بيتي! فوالله ما علمت من اهلي الا خيرا، ولقد ذكروا رجلا ماعلمت عليه الا خيرا)).
Ma'ana: ((Ya kira Aliyyu da Usamah a lokacin da Wahayi ya yi jinkiin zuwa yana mai neman shawararsu game da rabuwa da iyalinsa; amma shi Usamah sai ya ce: iyalinka ce ita, kuma ba mu san wani abu ba in banda alheri. Bareerah kuwa sai ta ce: babu wani abu na nakasa da nake gani tare da ita in banda kasancewarta wata yarinya mai karancin shekaru wacce take barci ta bar kullun garin gurasa har awakin gida su rika zuwa suna cin sa. Sai Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: Wane ne zai gamsar da mu har mu karbi uzurin mutumin nan da labarin cutarwarsa ga Ahlu baitina ya zo mini! Wallahi ni ban san wani abu ba game da iyalina in banda alheri. Tabbas sun ambaci wani mutum ni dai babu abin da na sani game shi in ba alheri)).

Allah Ya taimake mu har kullum. Ameen.

Share:

SANYA HAKORIN MAKKA A MA'AUNIN SHARIA?? Dr.jamilu yusuf zarewa

*SANYA HAKORIN MAKKA A MA'AUNIN SHARIA ?*


*Tambaya*


Assalamu Alaikum Dr, dafatar ka tashi lafiya
Alagafarta malam ina neman karin bayani game da Hauren makka da alhazzai suke sakawa akan cewa shima yana haddasa lum'a a lokacin da mutum ya zo kuskurar baki ruwa ba za su taba ainihin Hauren da Allah ya halicci mutum da shi ba?


*Amsa*
Wa alaikum assalam,

a zahiri sanya Haure bayan aikin hajji ba matsala ba ne ta fuskar Lam'a tun da kurkure baki sunna ne a wajan da yawa daga  malamai, wannan yasa rashin shafar ruwan ga hakori daya ba zai yi tasiri ba.

Amma zai iya zama matsala saboda yana iya janyo riya, tun da galibi wanda zai sanya yana yi ne saboda yaje hajji ko dan ace masa Alhaji, hakan ya sa barinsa shi ne ya fi.

Idan ya kasance an yi hauren ne da zinare to haramun ne namiji ya sanya saboda Annabi S.A.W. ya ce: (An haramta zinare ga mazajen Al'umata, amma an halatta ga matayansu)

Allah ne mafi sani.

*Dr, Jamilu Zarewa*

1/11/2017

Ga dukkan mai son shiga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH* sai ya yi saving wannan number +2348122248585  sannan ya tura da sunansa da adireshinsa ta whatApp. Duk abun da mutum ya turo matukar ba suna ba ne ba za a kula shi ba.
Share:

Tuesday, 7 November 2017

Yaduwar bin bokaye!!?

```YADUWAR BIN BOKAYE```
~~~~~~~~~~~~~~~~


_Godiya ta tabbata ga Allah, kuma tsira da amincin Allah su tabbata ga manzon Allah da mutanen gidansa, da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsa._
.
.
_Bayan haka wani abun takaici dake faruwa shine yadda zaka ga da yawa daga cikin matayen arewacin Nigeria sun jefa kansu a cikin mummunar hallaka ta sanadiyyar bakin kishi akan kishiya. Wasu mata saboda tsabar bin bokaye da 'yan duba da 'yan bori har su kansu ma sun zama matsafa qarfi da yaji, wasu kuma sun zama mazinata, suna zuwa suna zina da bokaye domin samun biyan miyagun bukatunsu._

_Akwai wasu Qawaye masu bin bokaye da faɗa ya tashi a tsakaninsu, suna yiwa juna gori sai wata tace ma ɗayar, ai yaron da kike goye dashi kema kin san ba ɗan mijinki ba ne, ɗan gidan boka wane ne. Haka dai suka rika tona ma juna asiri._

_Wasu kuma sun talauce su lalace, duk abun hannunsu ya qare saboda bin bokaye, wasu kuma addinin na su da imaninsu ma duk sun lalata, sun fi imani da maganar bokaye fiye da maganar Ubangijin su._

_Amma sai naga mafi yawan masu tofa albarkacin sunfi alaqanta abun da jahilci, ko duhun kai, alhali kuma gaskiya abun ba haka bane_

_A yanzu zaka tarar da mafiya yawan masu bin bokaye din nan, mataye ne wayayyu, 'yan boko masu aji, waɗanda ake ganin kamar kansu yaji gishiri. Kuma zaka tarar mafiya yawansu suna zuwa Islamiyyan ballantana ace basu san haramcin abun bane._

_Kuma matsalar tafi aukuwa a tsananin matayen Attajirai, 'yan siyasa da masu mulki, da sauran masu hannu da shuni. Amma yawancin matan talakawa suna fama da abin da zasu ci, koda suna son bin bokaye basu da bayarwa._

_Irin wannan harkar ta bokanci da tsafe-tsafe ta shigo har cikin kafofin sadarwa na yanar gizo wato (social media) kamar su whatsapp da Facebook. Yanzu haka akwai groups da pages da suke tallata wani abu wai shi *(Goron Tula)* wai wani abu ne wanda idan mace tayi amfani da shi, mijinta zai rikice wajen kaunarta har sai ya rabu da dukkan matansa, wai har kyautuka zai rika yi mata don dolensa!.._

_Dasu turaren jan hankali maza, da na korar kishiya da dai sauran su. Kuma matan dake wannan Sana'a r kullum sai kara yawa sukayi, kuma basu 6oye ma kowa abin da sukayi.._

_Abinda muke so mata su gane shine: bokanci ko harka da boka, ko amfani da kayan bokanci, duk haramun ne, kum hukuncin masu yinsa shine kafirci._

_Idan kikaje wajen boka kuma kika gaskatashi kin kafirce kenan, kuma ba zaki gane cewa ke kafira bace sai lokacin mutuwarki (sanda bubu lokacin tuba)_.

_Idan kika je lahira babu imani, to fa babu wata alfarmar da zaki samu a wajen Allah. Babu ceto gare ki, babu fita daga wuta, babu shiga Aljannah, babu shan ruwan Alkausara._

_kuma maganin mallakar miji ba zai mallaka miki tsarkakakkiyar soyayyarsa ba, kuma ba zai janyo miki samun soyayyar Allah ba, balle cikawa da imani._

_Duk wulakanci ko bambancin da kike gani agidan mijinki, to kiyi hakuri kiyi addu'a shine mafita, Allah ne yake juya al'amura ba boka ko malamin duba ba._

_Imaninki shine babban jarinki Aduniya da lahira, idan kika rasashi kin afka cikin talaucin da ba zaki sake yin arziki ba. Har abada. Allah ya tsare mana imaninmu._
=
=
Allah Ta'ala yasa mudace.
=
=
```DAN UWANKU HAR KULLUM ```:
IBrahim Abubakar Hamza




Share:

Audio:-Hakkin mata akan mazajensu - Dr.Abdullahi Usman g/kaya





HAKKIN MATA AKAN MAZAJENSU



Tare da:-

DR ABDALLAH USMAN G/KAYA


DOMIN SAUKO DA WANNAN AUDIO SAIKU SHIGA WANNAN BLUE RUBUTU DAKE KASA.


Ayi saurare lafiya.
Share:

Audio:-Adaidaita sahu 1-4 by Sheikh Muhammad adam albani Zaria (Rahimahullah)

MUHADARA MUHADARA

Mau taken:-
ADAIDAITA SAHU

Daga:-
Sheikh Muhammad adam albani Zaria (Rahimahullah)

DOMIN SAUKO DA WANNAN AUDIO SAIKU SHIGA WANNAN BLUE RUBUTU DAKE KASA.

001 Adaidaita sahu

Download now

002 Adaidaita sahu

Download now

003 Adaidaita sahu

Download now

004 Adaidaita sahu

Download now

Ayi saurare lafiya

Kucigaba da kasancewa da wannan shafin.
Share:

Menene Hukuncin lika Ayatul Kursiyyu Abango da Nufin neman kariya?

*Tambaya ta (219)*

*Menene Hukuncin lika Ayatul Kursiyyu Abango da Nufin neman kariya?*

الحمد لله واحد القهار.

*AMSA:*Lika Ayatul kursiyyu ko qananun alluna ajikin gida ko mota ko shago, ko makaranta ko wajan kasuwa, akwai barna mai yawa acikin hakan, bisa Abunda shari'a ta hana.

@ - Mafi Rinjaye Ana likawa ne dan Ado da gayu, wanda bango ana sanya masa launuka na fenti hakan saiya zama sababi na wulaqanta Alqur'ani.
Wannan yana daka cikin juyar da Alqur'ani daka manufar saukar dashi, daka shiriya da wa'azi kyakkyawa dakuma Ibada da tilawarsa dasauransu..

Alqur'ani Ba'a Saukar dashi danyiwa bango Ado dashi ba, an Saukar dashi dan shiriya ga Mutane, dakuma Bayani.

2- Wasu Suna likawa ne dan Neman tabarruki, Wannan Bidi'ane Tabarruki Mai kyau shine bauta da karanta Alqur'anin, Bawai likashi ajikin bango ko juyashi zuwa jikin Alluna masu Ado ba.

Sannan Yin hakan yasabawa Abunda Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yake akai, da khalifofinsa shiryayyu Allah yakara yarda dasu, dukkan Alkhairi yana cikin binsu, bawai wajan Saba musu ba,

Tarihi yanuna wannan dabi'a taliqa karamin Allo mai dauke da ayatul kursiyyu ko wani Bangare na Alqur'ani ajikin gida ko mota ko kasuwa, ba'a fara yinsa ba sai bayan shudewar  Nagartattun Musulmi sai lokacinda Musulmai suka zama masu rauni a'aqida da ilmi dariko da Addininsu.

Haka nan Lika irin wannan alluna dauke da Alqur'ani hanyace dazatakai Mutum ga shirka, domin Wasu suna qudurta cewa wadannan kananun Alluna da'ake likawa akasuwa ko mota ko gida kariyane ga gidan ko motar daka Wani Sharri, qudurce wannan kuma Shirkane.

Mai bada kariya na Hakika shine Allah, daka cikin dalilan da zaisa kuma yabawa Mutum kariya shine tilawar Alqur'ani ka yin zikirori wadanda Sukazo acikin hadisai Ingantattu, bawai likashi abangon gida ko mota ba.

Adunqule dai bai halatta rubuta ayar Alqur'ani abangon gida ko sanya karamin Allo ajikin mota ko shago ba, koda abangon masallacine bai halatta ba, bidi'ane.

Sanyawa kuma tareda qudurce bayar da wata kariya ga Mutum wannan kam Shirkane.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك نشهد أن لا إله إلا أنت نستغفرك ونتوب إليك.

🖊 *Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai*
*+2347033406106.*
*+2348140925493.*
Share:

Menene hukuncin mutumin da yake take wandonsa, shin ya halatta a bi shi salla?

*TAMBAYA DA AMSA DAGA SHEIKH MUHAMMAD BELLO AHMAD AL-ADAMAWIY, RAHIMAHULLAH*

*001*

*TAMBAYA*
Assalamu alaikum, Mene ne hukuncin mutumin da yake take wandonsa, shin ya halatta a bi shi salla?

*AMSA*
Take wanda a Musulunci haramun ne domin hadisai masu yawa sun zo suna hani akan haka, kuma ba lallai sai wando ba.

Manzon Allah, sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce:

 *"مَا أَسْفَلَ مِنْ الْكَعْبَيْنِ مِنْ الْإِزَارِ فَفِي النَّارِ"* رواه البخاري (5787).

Duk abun da ya wuce idon sawu (na tufafi), to yana wuta. Bukhari ne ya ruwaito hadisi na 5787.

Malamai suka ce tun da har Allah Ta'ala Ya yi barazana da wuta, to wannan ya nuna babban laifi ne.

Dangane da batun bin shi salla matukar babu najasa a jikin tufan shi za a bi shi salla, domin laifin mai laifi bai hana a karɓa sallansa matukar ya yi ta yanda shari'a ta koyar kamar yadda Abdullahi Bn Umar ya yi salla a bayan Hajjaj Bn Yusuf al-Thaqafee.

Wallahu A'alam.

✍🏼Tattarawa:
*_Umar Shehu Zaria_*
Share:

Sunday, 5 November 2017

JAN HANKALI:- Idan kana aikata abubuwa 3 imaninka zai karu

JAN HANKALI

IDAN KANA AIKATA ABUBUWA UKU IMANINKA ZAI KARU:

1- Tilawal Al-Qur'ani.
2- Kiyamul-laili.
3- Azkhar.

ZAKA FUSKANCI MATSALA A KABARINKA IDAN KA MUTU DA ABU UKU:

1- Hakkin Wani
2- Dabi'ar Annamimanci
3- Hassada

ABUBUWA UKU SUNA KAUDA FUSHIN ALLAH AKAN BAWANSA:

1- Istigfari.
2- Tausayawa waninka
3- Sadaka

IDAN ALLAH YA BAKA ABU UKU TO KA GODEWA ALLAH:

1- Lafiya
2- Wadata
3- Basira

KADA KA YARDA KA AURI MACE MAI DABI'O'I GUDA UKU:

1- Mai yawan fushi.
2- Maras sirri
3- Marar tsafta (Kazamiya)

KA YI KOKARI KA GINA RAYUWARKA AKAN ABU UKU:

1- Son Allah da Manzonsa.
2- Gaskiya da Rikon Amana.
3- Hakuri da Jarrabawa a Rayuwa

ABUBUWA UKU KA ROKI ALLAH (S.W.T) YA TSARE KA DA AIKATA SU:

1- Yanke Zumunta.
2- Zagin Sahabbai.
3- Mutuwa da hakkin wani

MUTANE UKU KADA KA SAURARI MAGANARSU:

1- Makaryaci
2- Magulmaci
3- Malami mai kwadayi da son zuciya

MUTUM UKU KADA KA YARDA SU DINGA KUSANTARKA:
1- Munafiki
2- Mazinaci
3- Maras kunya

ABUBUWA UKU BA A SON JINKIRTA SU IDAN LOKACIN SU YA ZO:

1- Sallah
2- Aure
3- Jana'iza

ABUBUWA UKU RIKO DA SU YANA SAMAR DA RABO A LAHIRA:

1- Kokarin ibada
2- Kula da Nafila
3- Amfani da Halal a Rayuwa

ABUBUWA UKU SUNA HANA MUTUM TANADIN LAHIRA:

1- Dogon Buri.
2- Rashin karanta Alkur'ani
3- Nisantar sauraron Wa'azi.

MUTANE UKU SUNA SAMUN TAIMAKON ALLAH:

1- Mutumin da yake Neman aure Don ya kare mutuncin kansa
2- Mutumin da ya tafi jihadi, Domin daukaka kalmar Allah.
3- Bawa wanda aka dora masa fansar kansa.

ABUBUWA UKU NASA ZUCIYA TA GURBACE:
1- Rashin yarda da kaddara.
2- Aibata bayin Allah na kwarai
3- Wulakanta Iyaye

Ya Allah ka tsare mu daga sharrin Shaidan, ka shiryar da mu kan hanya madaidaiciya, amin.
MATA 10 WAINDA ALLAH YA
TSINE MUSU: -
ﺍﻟﻮﺍﺷﻤﺎﺕ
ﻭﺍﻟﻤﺴﺘﻮﺷﻤﺎﺕ
1. Mata masu
tsaga
fuskokinsu. -
ﺍﻟﻨﺎﻣﺼﺎﺕ
ﻭﺍﻟﻤﺘﻨﺼﻤﺎﺕ
2. Mata masu
aske gashin
gira. -
ﺍﻟﻤﺘﻔﻠﺠﺎﺕ
3. Mata masu
kankare hakori
(wushirya). -
ﺍﻟﻮﺍﺻﻠﺔ
ﻭﺍﻟﻤﺴﺘﻮﺻﻠﺔ
4. Mai 'karin
gashi da wadda
ake karamata
gashin. -
ﺍﻟﺘﻲ ﺳﺨﻂ ﻋﻠﻴﻬﺎ
ﺯﻭﺟﻬﺎ
5.Matar da
mijinta yayi
fushi da ita. -
ﺍﻟﻤﺘﺸﺒﻬﺎﺕ ﺑﺎﻟﺮﺟﺎﻝ
6. Mata masu
shigar maza. -
ﺯﻭﺍﺭﺍﺕ ﺍﻟﻘﺒﻮﺭ
7. Mata masu
yawan
ziyartar
kabur-bura
(makabarta).
- ﺍﻟﻨﺎﺋﺤﺎﺕ
8. Mata masu
kururuwa akan
mamaci. -
ﺍﻟﻤﺤﻠﻞ ﻟﻪ
9. Mata masu
auren kashe
wuta. -
ﻛﺎﺳﻴﺎﺕ ﻋﺎﺭﻳﺎﺕ
ﻣﺘﺒﺮﺟﺎﺕ
10. Mata masu
bayyana
tsiraicinsu.
Kada ku manta TSINUWA itace
nisanta daga
rahamar Allah!
ﻗﺎﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : " ﻳﺎ
ﻣﻌﺸﺮ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ
ﺗﺼﺪﻗﻦﻭﺃﻛﺜﺮﻥ ﻣﻦ
ﺍﻹﺳﺘﻐﻔﺎﺭﻓﺈﻧﻲ
ﺭﺃﻳﺘﻜﻦ ﺃﻛﺜﺮ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻨﺎﺭ " ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ
Manzon Allah (SAW)
ya ce: 'Yaku
taron mata! ku
yi sadaqa,
kuma ku yawaita neman
gafara.
(Istigfari)
domin lallai
ninagan ku
mafiya yawanku
'yanwuta
ne."Allah yakaremu. Send it to ur family n frndx

Assalamu alaikum. Manzon Allah (S.A.W) yace:kuyi kokarin danne abubuwa uku:

(1) fushi (2) Sha'awa (3) Maganganunku.

Ku himmatu danyin abubuwa 2:
(1) Ayyukan Alkhairi (2) Abokai nagari.

Kuci moriyar abubuwa 2:
(1) Lokaci (2) Karfi.

Ku nemi abubuwa 3:
(1) Gafaran Allah (2) ilmi (3) Hikima.

YA ALLAH KABAMU IKON KIYAYEWA.

Ba'a gajiya da aikin alkhairi. Daure turawa 'yan uwa musulmi domin samun lada.

Share:

Saturday, 4 November 2017

AKWAI GADO GA DAN DA MACE TA SHAYAR DA IYAYEN SHI ?

*_AKWAI GADO GA DAN DA MACE TA SHAYAR DA IYAYEN SHI ?_*


*_Tambaya_*

Assalamu alaikum malamaina don Allah ga wata tambaya kamar haka : idan aka haifi yaro sai daga baya aka samu cewa da babanshi da mamarshi duk mace guda ta shayar dasu to wai wannan yaron yana da gadansu koko?


*_Amsa_*
Wa'alaykumussalam.

 A na gado da takaba a auren da a ka gano rashin ingancinsa, kuma a na danganta yaro ga mahaifinsa. [AL-MUGNY; 8/590]

Wallahu A'alam.

*_MALAM: NURUDDEEN MUHAMMAD (MUJAHEED)_*

25/10/2017

Ga dukkan mai son shiga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH* sai ya yi saving wannan number +2348122248585  sannan ya tura da sunansa da adireshinsa ta whatApp. Duk abun da mutum ya turo matukar ba suna ba ne ba za a kula shi ba.

Share:

Friday, 3 November 2017

FALALAR KARANTA WASU SURORI LOKACIN KWANCIYA BARCI?!

*FALALAR KARANTA WASU SURORI LOKACIN KWANCIYA BARCI*


*1-Karanta AYATUL KURSIYYU*

Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Idan kazo kwanciya a shimfidarka to ka karanta AYATUL KURSIYYU,Wato*
*﴿اللّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ﴾ bazaka gushe ba kana tare da mai kariya daga Allah,Kuma shaidan bazai kusance ka ba har sai ka wayi gari)*
@صحيح البخاري-رقم (3275).

*2-Karanta QUL YÃ AYYUHAL KAFITUN*

Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Idan kazo kwanciya shimfidarka acikin dare,to ka karanta QUL YA AYYUHAL KAFIRUN,"قُلْ يَا أيُّهَا الْكَافِرُونَ"sannan sai ka kwanta barci alokacin da ka gama karantata,Domin ita kubutace daga Shirka)*
@حسنه الألباني في صحيح الجامع -رقم :(292).


*3-Karanta QUL HUWALLAHU da FALAQI da NASI*

Daga Nana A'isha رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا,tana cewa,Manzon Allah ﷺ ya kasance,idan yazo kwanciya a shimfidarsa a kowane dare,yana hada tafikan hannuwansa,Sannan sai yayi tofi acikinsu,
sai ya karanta,QULHUWA FALAQI da NASI)*
﴿قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ﴾وَ﴿قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ﴾وَ﴿ قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ ﴾،
*Sannan sai ya shafi abinda ya sauwaqa daga jikinasa,yana farawane daga shafar kai,da abinda yayi saura na jikinsa,yana yin haka har sau ukku)*
@صحيح البخاري-رقم : (5017)


*4-Karanta suratul ISRA'I da ZUMAR*

Daga Nana A'isha رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا,tace,Manzon Allah ﷺ ya kasance baya kwanciya barci har sai ya karanta *SURATUL ISRA'I da SURATUL ZUMAR*.
@صححه الألباني في صحيح الترمذي -رقم:(2920)

*5-Karanta Suratul MULK wato TABARA*


 Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Lallai akwai wata Sura ta Alqurani mai ayoyi guda Talatin,tana neman ceton bawa har sai an gafarta masa,itace Suratul TABARA.....)*

Daga Abdillahi bn Mas'ud R.A yana cewa;-
"Wanda ya karanta Suratul TABARA
{تباركَ الذي بيدِه الملكُ}
A kowane dare,Allah zai kare shi da ita daga Azabar Qabari,Mun kasance a lokacin Manzon Allah ﷺ muna kiranra mai tseratarwa.....".
@صحيح الترغيب 1475 صحيح ابن ماجه 3068 صحيح الترمذي 2891 صحيح أبي داود 1400 الألباني

Manzon Allah ﷺ ya kasance yana karanta Suratul TABARA  da Suratul
SAJADA,akowane dare"
@صحيح الجامع  ٤/٢٥٥ الألباني
*6-Karanta Ayoyi guda biyu na karshen Suratul BAQARA*

Manzon Allah ﷺ yana cewa;-

*(Dukkan wanda ya karanta ayoyi guda biyu na karshen suratul BAQARA a kowane dare ta isar masa)*
@البخاري مع الفتح، ٩/ ٩٤، برقم ٤٠٠٨، ومسلم،١/ ٥٥٤، برقم ٨٠٧، والآيتان من سورة البقرة، ٢٨٥-٢٨٦.

*﴿آمَنَ الرَّسُولُ بِمَا أُنْزِلَ إِلَيْهِ مِنْ رَبِّهِ وَالْمُؤْمِنُونَ كُلٌّ آمَنَ بِاللَّهِ وَمَلائِكَتِهِ وَكُتُبِهِ وَرُسُلِهِ لا نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِنْ رُسُلِهِ وَقَالُوا سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا غُفْرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيْكَ الْمَصِيرُ*

*لا يُكَلِّفُ اللَّهُ نَفْسًا إِلا وُسْعَهَا لَهَا مَا كَسَبَتْ وَعَلَيْهَا مَا اكْتَسَبَتْ رَبَّنَا لا تُؤَاخِذْنَا إِنْ نَسِينَا أَوْ أَخْطَأْنَا رَبَّنَا وَلا تَحْمِلْ عَلَيْنَا إِصْرًا كَمَا حَمَلْتَهُ عَلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِنَا رَبَّنَا وَلا تُحَمِّلْنَا مَا لا طَاقَةَ لَنَا بِهِ وَاعْفُ عَنَّا وَاغْفِرْ لَنَا وَارْحَمْنَا أَنْتَ مَوْلانَا فَانْصُرْنَا عَلَى الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ﴾*.


Allah ne mafi sani



*Allah ka bamu ikon da Manzon Allah ﷺ a dukkan rayuwa baki daya*.
Share:

MENENE HUKUNCIN WANDA YAYI SALLAH ALHALI YASAN YANA CIKIN JANABA??

*MENENE HUKUNCIN WANDA YAYI SALLAH ALHALI YASAN YANA CIKIN JANABA??*

الحمد لله رب العالمين.

Amsa: Abune sananne awajan musulmi cewa tsarkin  hadasi babba ko karami, wajibine, kuma sharadine na ingancin sallah, duk wanda yai sallah bashi da tsarki da gangan koda mantuwa sallarsa batacciyace bataiba, saiya sake, idan daganganci yayi hakika ya aikata babban laifi cikin manyan laifuka dakuma zunubi mai girma.

Shaikul islam ibnu taimiyyah rahimahullah yace:

"Musulmi kada yayi sallah a inda ba alkibla bane, kada yayi sallah batare da alwala ko ruku'u ko sujjada ba, wanda ya aikata haka yacancanci zargi da uquba,
Min hajussunnah (5/204).

Hakika gargadi mai tsanani yazo gawanda ya aikata haka;

Hadisi daga Abdullahi dan mas'ud yardar Allah takara tabbata agareshi daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam yace: (Anyi Umarni ayiwa wani bawa daka cikin bayin Allah bulala dari acikin kabarinsa, bai gusheba yana tambayar dalilin bulalar dakuma rokon asassauta masa harsaida ya rage saura bulala daya, sai aka karasa masa dayar, aka cika kabarinsa da wuta, lokacin da'aka dauke masa azabar bayan yafarfado sai yace kusanar dani sabo dame akaimin bulala? sai akace dashi kayi sallah ne sau daya batare da tsarki ba, kawuce tawajan azzalumi kuma baka taimakeshiba) Addahawi yaruwaitoshi acikin mushkilil Ãàsaar Albani ya hassanashi acikin silsila saheeha (2774).

Malamai sunyi ittifaqi akan duk wanda yai sallah batare da tsarki ba yana mai halatta hakan, ko saboda isgili, hakika yakafirta, za'a nemi yatuba, idan bai tubaba za'a kasheshi.

Amma idan mutum yai sallah batare da alwala kawai dan wulakanta sallah, bai halatta hakan ba kuma ba izgili yakeba,  Imamu Ahmad yatafi akan cewa mutum yakafirta, jamhurdin malamai kuma sukace: bai kafirta ba, saidai abunda yayi babban laifine cikin manyan laifuka.

Imamun nawawi rahimahulla yace:

Idan mutum yasan yanada hadasi kuma yasan sallah batsarki haramunne, abunda yayi laifine babba cikin manyana laifuka, baya kafirta awajanmu, saidai idan yahalatta sallah batsarki ne, Abu hanifa yace yakafirta saboda izgilinsa.

Abunda yake wajibi akan wanda yai sallah babu tsarki shine yatuba, yayi istigfari, yakuma kuduri niyyar bazai sake aikata hakan ba, sannan saiya sake sallar daya sallata batare da alwala ba, Allah madaukakin sarki yana karbar tuban wanda yatuba yakoma gareshi.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.

Tambayoyin musukunci
Watsapp group
Share:

Thursday, 2 November 2017

Audio:- Muhimmancin Sada Zumunci A Musulunci Sheikh Jabir Sani Maihula

KHUDUBAR JUMU'A (7-2-1439AH / 27-10-2017) Daga Masallachin Sultan Muh'd Sa'ad Abubakar III dake Tanki Guiwa Lowcost Sokoto.

Mai Taken: MUHIMMANCIN SADA ZUMUNCI A MUSULUNCI

Tare da: Sheikh Jabir Sani Maihula (Hapizahullah)

Download Audio Now
Share:

Video:-Maganin Ciwon Suga Da Hawan Jini By Dr.Abdullahi Usman Umar g/kaya Kano

Zaku Saurari Da Kuma kallo Fatawa Daga  ml Abdullahi Usman Umar Dake Jahar Kano State, Zakuji Yadda Yake Bayani Game Da Magungunnah Na Gargajiya.
Wa’yanda Sunka Hada Da Magance Ciwon Suga da Hawan jini Da Saurab Makamantan Su.
Haka Kuma Zaku Karu Da Wannan Fatawa Tashi Ta Fannin Abubuwa Dake Cike Da lora A Wannan Zamani Da Muke ciki Domin Malamin Allah Ya Bashi Basira Fiye Da Tinanin Jama’a.
Sai kuyi Download Ku kallah Ku saurari Malamin.
Watch After Download:-
Share:

Video:Wacece Mijinta Yafi ( Tare Da Mata ) - Sheikh Jafar Mahamud adam (Rahimahullah)



Allah jiqan malam da rahama allaha ka tsinewa dukkan masu hannu a wajen kisan malam ya Allab ka wargaza tanadinsu allah hadasu da masifa da bala i daga duniyarsu har lahira.
ya na daya ne daga cikin mafiya
shahara da kuma fitattun
Malaman Musulunci kuma
Jagorori a kan shiriya da miliyoyin al’ummar Musulmin Najeriya –
Musamman Arewacinta –
da kuma yammacin Afirika
su ka gani a farkon karni
na 15 bayan Hijrar Manzon
Allah (sallallahu ‘alaihi wa
alihi wa sallam) daga
Makkah zuwa Madina.
Ranar Juma’a 25 ga watan
Rabi’ul Awwal, 1428 A.H.
(13 April 2007, C.E.), wasu
‘yan ta’adda da kuma
bindiga dadin da har
yanzu ba a san ko su waye
ba, sun yiwa Malam Ja’afar
Kisan gilla lokacin da ya ke
jagorantar jama’a a sallar
Asuba a masallacin
Juma’arsa da ke unguwar
dorayi a birnin Kano,
Najeriya.
Hakikanin gaskiya, Malam
Ja’afar zai dade a zukatan
dukkanin Musulmi a
matsayin wata alama ta
masu riko da madarar
karantarwar addinin
Musulunci bisa
madaidaicin ra’ayi adalci
da kuma basira.
Don haka, bukatar samar
da website da sunansa ba
za ta misaltu ba. Wannan
website zai tattara tare da
yada gagaruman ayyukan
Shaikh Ja’afar ta dukkanin
hanyoyi, abun da mutane
da yawa a ko’ina cikin
kasa ke yunwar samu,
musamman saboda
Shehin malamin wata
alama ce ta malaman da
su ke kira zuwa ga akidar
Ahlus Sunnah wal Jama’ah.
Wannan website zai
taimaka wajen yada
ayyukan Shaikh Ja’afar na
alkhairi da taimakon
al’umma tare da bayar da
hadin kai don yada
kyawawan ayyuka da
ciyar da su gaba ta hanyar
tallafawa ilimi da harkokin
zamantakewa.
FATAN ZA’ACI GABA DA KASANCEWA TARE DAMU
Share:

Saturday, 28 October 2017

MUYI SALATI GA ANNABI SAW (DARAJOJI 40) Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Mal.Aminu Ibrahim Daurawa

MUYI SALATI GA ANNABI SAW (DARAJOJI 40)

Yin salati ga Annabi saw, yana jawo wa mai yi darajoji 40
Kamar yadda Ibnul Qayyim ya kawo a cikin littafin sa, da ya wallafa akan salati ga Annabi saw, mai suna Jala'ul afham.
Na 1, Yin salati Bin umarnin Allah ne.
Na 2 , Koyi da Allah swt, shima yana yiwa Annabi saw. salati
Na 3 , koyi da Mala'iku, suma suna salati ga Annabi saw .
Na 4 , Samun lada goma.
Na 5 , Samun daraja goma.
Na 6 , yafe laifi goma.
Na 7 , Amsa adduar wanda ya fara da salati.
Na 8 , samun ceton Annabi saw .
Na 9 , Gafarta zunubin mai yawan salati .
Na 10 , Allah zai yaye, masa abinda yake damunsa.
Na 11 , Zaiyi kusa da Annabi saw. Ranar Alkiyama
Na 12 , Wanda yayi salati ya sami ladan Sadaka.
Na 13 Salati sababi ne na biyan bukata.
Na 14 , Allah taala Zaiyi salati ga wanda ya yiwa Annabi saw, salati.
Na 15 ,Salati ga Annabi saw, yana tsarkake mai yawan yinsa.
Na 16 , Zai sami bushara da Aljannah.
Na 17 Tsira daga tsananin kiyama
Na 18 yiwa Annabi saw salati yana tuno maka abinda ka manta
Na 19 , salati yana cikin hakkokin Annabi saw.
Na 20 , Salati yana kamsasa majalisi.
Na 21, Salati yana korar talauci.
Na 22 Salati ga Annabi saw yana kore rowa .
Na 23 Bazaa durmaza hancin mai salati ba.
Na 24 Mai salati ya kama hanyar Aljannah.
Na 25 Idan akayi taro aka tashi babu salati, zaayi warin mushen jiki.
Na 26 , A fara magana da yabo ga Allah da salati ga Annabi saw.
Na 27 samun haske akan siradi ranar Alkiyama
Na 28 fita daga Jafa'i, na laifi, idan anyi salati.
Na 29 Mai yawan salati ga Annabi saw, yana samun yabo da girma.
Na 30 samun Rahma
Na 31 soyayyar Annabi saw, ga mai salati
Na 32 Annabi saw ya Nuna yana son mai masa salati.
Na 33 Samun shiriya da rayuwar zuciya .
Na 34 Duk mai yiwa Annabi saw salati, ana gayawa Annabi saw, sunan sa.
Na 35 Tabbata akan siradi ranar Alkiyama
Na 36 Yiwa Annabi saw, salati, rokon Allah, kuma ibada ne.
Na 37 Salati ga Annabi saw godiya ne ga Allah.
Na 38 salati ga Annabi saw zakka ne da tsarki g
Share:

MECECE DUNIYA?!

MECECE DUNIYA?
*******************
'Yan uwa wannan rayuwar ta duniya fa rudani ce da wasa, da yaudara mai dauke hankali.. Shaitan yana amfani da ababen cikinta wajen yaudarar da zukata da shagaltar da tunanin Bil Adama.

Rayuwar nan ta duniya Mafarki ne wanda ke cike da alkawura marassa tushe, Marassa makama.. Wanda yayi sammakon farkawa daga wannan mafarkin shine wanda ya rabauta.

Ita rayuwar duniya tamkar cin kasuwa ne. Lokutan da Ubangiji ya baka awannan rayuwar sune tamkar kudaden cin kasuwar.. Babu wanda ya rabauta sai wanda yayi amfani da kudinsa wajen sayen abubuwan da zasu amfaneshi idan ya koma gidansa na ainahi..

Wato yayi amfani da lokutansa wajen neman ilimin addini da kuma aiki dashi, Ko taimakon addini da jikinsa da Aljihunsa da basirarsa da dukiyarsa..

Yayi amfani da ranaikunsa da dararensa wajen nafilfili da Zikirin Allah da Karatun Alqur'ani da kira zuwa ga tafarkin Allah..

Amma wanda yayi amfani da lokutansa wajen Kallon abinda ya haramta, rawa da waqa, zaman gulmace-gulmace, cin mutuncin Musulmai, tafiya wajen sa'bon Allah, rushe tarbiyyar al'ummah, to wadannan sune asararru, sune wadanda basu ci ribar kasuwancinsu ba..

Ya kai 'Dan uwa!! Ko kasan cewa duk abinda kake gadara dashi awannan duniyar (Kudi, Mulki, daukaka, dukiya) sai da wasu suka sameshi kafinka?.

Kuma yanzu dolensu sun tafi sun barshi?. Suna Qarkashin Qasa suna girbar abinda suka shuka na alkhairi ko sharri??.

Yadda yanzu basu nan sai dai labarinsu, mafiya yawansu ma ko labarin nasu babu....  To hakanan kaima gobe sai dai labarinka... Jibi kuma ko labarin naka ma babu!!!.

Lahira ita ce gidanka na ainahi.. Gidanka matabbaci.. Yi Qokari ka tanadar ma kanka guzuri mai yawa ta hanyar Ibadah mafi saurin tseratarwa daga wuta. Wato Zikirin Allah safiya da maraice..

Yima guzurinka Stamp na Ikhlasi.. Kuma ka zubar da Miyagun kaya daga cikin guzurinka ta hanyar Istighfari..

Ka Qamsasa guzirin naka, ka Qara masa tsada ta hanyat Salati da Tasleemi ga Annabinka mafi daraja.. Alfaharin Banu Hashim, Farin cikin Halittu, Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata agareshi da iyalan gidansa tsarkaka da dukkan Sahabbansa yardaddu da mabiyansa har zuwa ranar sakamako. Ameeen.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (24/10/2017 05/02/1439).


Share:

SU WAYE FIQAHA'US SAHABAH?

SU WAYE FIQAHA'US SAHABAH?
********************************
Wasu Sahabbai ne manya wadanda suka shahara a fagen ilimi da fahimtar addini. Kuma mafiya yawansu sun dauki zamani mai tsawo suna tare da Manzon Allah (saww).

Masu kokari ne wajen Ilmantarwa da karantarwa tun azamanin Manzon Allah (saww) da kuma bayansa. Wadanda daga irin fatawoyinsu ne aka gina fahimtoci na manyan Mazhabobin nan na Maluman Fiqhu.

Mafiya shahara daga cikin Fiqaha'us Sahabah sun hada da :

- Sayyiduna Abubakrin bn  Abi Quhafah (Assiddeeq).

- Sayyiduna Umar bn Al-Khattab (Al Faruq).

- Sayyiduna Uthman bn Affan (Dhun Nurayn).

- Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib (Abul Hasanaini).

- Abdullahi bn Mas'ud.
- Zaidu bn Thabit.
- Abu Musal Ash'ariy.
- Mu'az bn Jabal.
- Ubayyu bn Ka'ab.
- Abud Darda'i.

Sai kuma Ummul Mumineen,  Nana A'ishah bintu Abibakrin  (Allah shi yarda dasu baki dayansu).

Sannan acikin kashi na biyu kuma akwai wadanda ake kira "AL- ABADALAH". Wato dukkansu sunayensu Abdullahi ne. Kuma dukkansu 'ya'yan Sahabbai ne kuma sun riski lokacin rayuwar Manzon Allah (saww). Kuma sun tattaro Ilimai masu yawa wadanda kusan sun shiga kowanne fanni na ilimin addini. Gasu nan kamar haka :

- Abdullahi bn Abbas.
- Abdullahi bn Umar.
- Abdullahi bn Zubayr bn Awwam.
- Abdullahi bn Amru bn Al-As.

Allah shi yarda dasu baki dayansu.

Dukkansu baki daya kowanne yana da manyan abubuwan da ya kebantu dasu na falala da fifiko acikin sauran Sahabbai.

Muhammad 'dan Sahlu dan Abu Khaysamah ya karbo daga Babansa yana cewa :

"Wadanda suka kasance suna bayar da fatawa azamanin Manzon Allah (saww) mutum uku ne daga Muhajirun, uku kuma daga mutanen Madeenah.

Umar da Uthman da Aliyu da Ubayyu bn Ka'ab  da Mu'azu bn Jabal da Zaidu bn Thabit. Shi kuwa Abdullahi bn Abbas ya kasance idan an tambayeshi game da wani abu, in dai babu acikkn littafin Allah da Sunnar Annabinsa (saww) to yana yin furuci ne da Qaulin Abubakar (ra) idan kuma babu to yakan yi fatawa da maganar Umar (Allah shi yarda dasu baki dayansu. Ameen.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (17/10/2017 27-01-1439).


Share:

NA SAKI MATATA SAU BIYU, SAI NA SAKE SAKINTA BAYAN DAURA SABON AURE, KO AKWAI DAMAR KOME?? Dr.jamilu yusuf zarewa



*NA SAKI MATATA SAU BIYU, SAI NA SAKE SAKINTA BAYAN DAURA  SABON AURE, KO AKWAI DAMAR KOME ?*


*Tambaya*

Assalamu alaikum don Allah malam ka warware mana wannan matsala, yanzu haka muke cikinta, mutum ne ya sake matarsa shika Daya 1, ya koma da ita bayan wasu shekaru ya sake mata shika daya, har idarta ya kare ya sake biyan sadaki ya dawo da ita yanzu kuma sun sake rabuwa shika daya 1, kuma suna son junansu akwai aure a tsakaninsu ko sai ta sake auren wani ? shikan bayan da ya mata har idarta ya kare aka sake daura aure a matsayin shika nawa ne yake kanta nagode Allah ya kara imani da basira sai naji daga gareka


*Amsa*
Wa'alaykumussalam

To dan'uwa idan abin haka yake kamar yadda ka siffanta, to babu damar kome, sai in  ta auri wani mijin na daban, saboda igiyoyin da suke tsakaninku sun yanke gaba dayansu .
Auren da kuka sake, ba zai goge sakin da ka yi a baya ba, da ace ta auri wani bayan saki biyun da ka mata, kafin ka sake auranta, da ba'a kirga da saki biyun baya ba, a daya daga cikin maganganun malamai, amma tun da ba ta auri wani  ba, ya wajaba ku hakurewa juna .

Don neman Karin bayani duba : Al-mugni na Ibnu-Khudaamah 7\388 .

Allah ne mafi sani .

*Dr, Jamilu Zarewa*

3\5\2015

Ga dukkan mai son shiga ​ZAUREN FIQHUS SUNNAH​ sai ya yi saving wannan number +2348122248585  sannan ya tura da sunansa da adireshinsa ta whatApp. Duk abun da mutum ya turo matukar ba suna ba ne ba za a kula shi ba.

ADMINS
Share:

Monday, 23 October 2017

Audio:-Muhadara:Manzon Allah (S A W) Rahma ne - Sheikh ahmed tijjani yusuf guruntum


MUHADARA MUHADARA

Daga:-

Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum 


DOMIN SAUKO DA WANNAN AUDIO SAIKU SHIGA WANNAN BLUE RUBUTU DAKE KASA.


Ayi saurare lafiya

Share:

HUKUNCIN KALLON WASAN KWAIKWAYON ANNABAWA!!? Dr.jamilu yusuf zarewa

*HUKUNCIN KALLON  WASAN KWAIKWAYON ANNABAWA*


*Tambaya*


Assalamu Alaikum
Malam Don Allah Tambaya Na ke da shi Da Fatan Za'a  Fahimtar da ni. -wai Shin Kaset din da akeyi na Tarihin Annabawa Ya Halatta A Kalle shi ? Allah Ya Saka Da Alkhairi .



*Amsa*
Wa'alaykumussalam.

To dan'uwa  malamai da yawa sun haramta yin wasan kwaikwayon annabawa saboda dalilai kamar haka :

1. Hakan zai iya bude kofar da wasu masu kallon za su yi  isgilanci ko ba'a ga annabawan Allah, isgilanci ga annabawa kuma yana iya  fitar da mutum daga musulunci, kamar yadda aya ta : 65 a suratu Atttauba ta yi nuni zuwa hakan.

2. Wasu daga cikin masu shirya film din suna wuce gona-da-iri, kamar masu nuna annabi Isa a matsayin Allah, addinin musulunci kuma ya haramta duk abin da zai kai a riki wani annabi ko managarci a matsayin Allah.

3. Irin wadannan wasannin na kwaikwayo, suna ragewa annabawa matsayi, saboda masu film din suna cakuduwa da matan da ba muharramansu ba, wanda hakan kuma  ragewa annabawa kima ne.

4. Kasancewar hakan ya sabawa hikimar Allah ta sanya shaidanu ba sa iya kama da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi , kamar yadda ya zo a hadisi.

5. Kasancewar hakan zai jawo aki girmama annabawa, a kuma yi musu karya, domin wasu masu yin wadannan fina-finan mutanen banza ne, ka ga sai a dinga kallon annabawan da siffar wadannan.

Allah ne mafi sani.

*Dr Jamilu Zarewa*

13/6/2014

Ga dukkan mai son shiga ​ZAUREN FIQHUS SUNNAH​ sai ya yi saving wannan number +2348122248585  sannan ya tura da sunansa da adireshinsa ta whatApp. Duk abun da mutum ya turo matukar ba suna ba ne ba za a kula shi ba.

ADMINS
Share:

HUKUNCIN AURE CIKIN AURE?? Dr.jamilu yusuf zarewa

*HUKUNCIN AURE CIKIN AURE*


*Tambaya*

Assalamu alaikum, mallam tambaya muke da ita. Mace ce aka aurar
tana ‘yar-shekara 14 ga wanda bata so, to sai
mijin yayi tafiya har tsawon wata hudu (4) To
sai matar tasa aka rubuta mata saki tace ya
saketa, bayan ya dawo yace bai saketa ba,
amma ba’a yarda ba.
Da ta kare idda tayi aure
da wani har suka haihu, daga baya kuma suka
rabu, kuma yanzu ta ga musifu suna ta
samunta, sai take tunanin ko wancan abin ne da
tayi. Tana neman fatawa, ina hukuncin ta, da
yaran data haifa da miji na biyu?


*Amsa*
Wa'alaykumussalam

Malam amsar wannan tamba yana da mutukar
wahala, saidai na nemi taimakon wasu daga
cikin malamaina, ga abin da na samo :

1. Abin da ta yi mummuna ne a shari’ar
musulunci saboda ta yi aure cikin aure.

2. Zaman da su ka yi da mijinta na biyu, a
matsayin mazinaciya take, saboda haka duk
kwanciyar da suka yi da wannan mijin na ta
zina ne.

3. Yaran da su ka Haifa da mijnta na biyu,
‘ya’yansa ne, tun da bai san abin da ya faru ba
a baya.

4. Har yanzu igiyar aurenta ba ta warware ba
tsakaninta da mijinta na farko, saboda haka har
yanzu ita matarsa ce saidai in ya sake ta.

5. Mijinta na farko, zai iya dawowa da ita, ba
tare da sake daura aure ba, saidai dole sai
bayan ta tuba, domin ita a matsayin
mazinaciyya take, kuma Allah ya hana auren
mazinaciya.

6. Ya wajaba a gare ta ta yawaita istigfari
saboda girman zunubin da ta aikata.

7. Zai yi kyau su je wajan Alkali wanda ya san

shari’ar musulunci, domin ya yi musu hukunci.

ALLAH NE MAFI SANI.

*Dr. Jamilu Zarewa*

20/11/2016
Share:

HUKUNCIN MATAR DA TA YI AURE KAFIN A SAKETA - Dr.jamilu yusuf zarewa

*HUKUNCIN MATAR DA TA YI AURE KAFIN A SAKETA*


*TAMBAYA :*

Assalamu alaikum Malam.  Mace ce aka aurar tana 'yar-shekara 14 ga wanda bata so, to sai mijin yayi tafiya har tsawon wata hudu (4) To sai matar tasa aka rubuta mata saki tace ya saketa, bayan ya dawo yace bai saketa ba, amma ba'a yarda ba. Da ta kare idda tayi aure da wani har suka haihu, daga baya kuma suka rabu, kuma yanzu ta ga musifu suna ta samunta, sai take tunanin ko wancan abin ne da tayi. Tana neman fatawa, ina hukuncin ta, da yaran data haifa da miji na biyu?


*AMSA:*
Wa alaikum assalam

 Malam amsar wannan tambaya yana da mutukar wahala, saidai na nemi taimakon wasu daga cikin malamaina, ga abin da na samo :

*1.* Abin da ta yi mummuna ne a shari'ar musulunci saboda ta yi aure cikin aure.

*2.* Zaman da su ka yi da mijinta na biyu, a matsayin mazinaciya take, saboda haka duk kwanciyar da suka yi da wannan mijin na ta zina ne.

*3.* Yaran da su ka Haifa da mijnta na biyu, 'ya'yansa ne, tun da bai san abin da ya faru ba a baya.

*4.* Har yanzu igiyar aurenta ba ta warware ba tsakaninta da mijinta na farko, saboda haka har yanzu ita matarsa ce saidai in ya sake ta.

*5.* Mijinta na farko, zai iya dawowa da ita, ba tare da sake daura aure ba, saidai dole sai bayan ta tuba, domin ita a matsayin mazinaciyya take, kuma Allah ya hana auren mazinaciya.

*6.* Ya wajaba a gare ta ta yawaita istigfari saboda girman zunubin da ta aikata.

*7.* Zai yi kyau su je wajan Alkali wanda ya san shari'ar musulunci, domin ya yi musu hukunci.
Allah ne mafi sani.

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
30/6/2014
Share:

TA YI AURE DA CIKIN-SHEGE?? Dr.jamilu yusuf zarewa

*TA YI AURE DA CIKIN-SHEGE??*

 *Tambaya:*

Assalamu alaikum. Malam Wata tayi cikin shege da wani mutum,sai ta nemi wani daban ya rufa mata asiri ya aureta.
Yanzu sunyi Auren,yaya hukuncin Auren a Shari'a yake???

 *Amsa*

Wa alaykum assalamu Zina sabon Allah ne da kuma yada fasadi a bayan qasa. Aure kuwa sunnar Manzon Allah ne, da samar da zuriya mai albarka. Kuma an kwadaitar da mu yin sa. Amma Mazhabar Malikiyya suna ganin matar da aka yi zinar da ita sai ta yi jini wanda ake kira Istibra’i, kafin a daura mata aure domin a raba maniyyin zinar da na aure. Kuma idan har an daura aure ba ta yi wannan jinin ba, to, za a raba wannan auren ko da sun haifi `ya`ya, domin suna ganin an daura auren ne a cikin idda, kuma Allah Ya hana daura aure a cikin idda. Saboda haka, a wurinsu, wannan auren batacce ne kuma rusasshe.
Amma Mazhabar Abu Hanifa da Imam Shafi`i suna ganin macen da ta yi zina, an so ta yi istibra’i kafin ta yi aure, amma idan har an daura auren ba ta yi istibra’i ba, auren yana nan daram, ba za a raba su ba. Kuma suka qara da cewa ko da tana da cikin zinar ne aka daura mata aure, to, auren yana nan. Sai dai Imam Abu Hanifa ya ce: mijin da ta aura, ba zai sadu da ita ba, har sai bayan ta haihu, ko da kuwa cikin zinar nasa ne ko na waninsa.
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Duk wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira, to kada ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa" Abu- dawud : 1847.
Don neman karin bayani duba : AL-MUDAWWANNAH aL-KUBRAH 2\173 da Al-mugni na Ibnu-Khudaamah 8/79.

A fahimtata, fatawar Malikiyya ta fi inganci kafin ayi auren, saboda fita daga sabanin malamai abin só ne, sannan kuma za'a kaucewa fadawa hadari, amma idan an riga an yi auren to fatawar Hanafiyya abar lura ce, saboda akwai bambanci tsakanin zina da aure, saidai ya wajaba şu nisanci saduwa, kafin ta haihu Saboda hadisin da ya gabata.

Allah ne mafi sani.

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*
27/02/2016
Share:

IDAN SAKI YA FITO DAGA BAKI BA YA KOMAWA !! Dr.jamilu yusuf zarewa

*IDAN SAKI YA FITO DAGA BAKI BA YA KOMAWA !!*


*Tambaya*

Assalamu alaikum malam wata baiwar Allah ce suka sami sabani da mijinta sai yabita inda take aiki yaje yana nemanta sai tafadama wata agurin taje tacemai batanan sai mijin yace d yar sakon tace yasaketa saki uku kuma itama taji da kunnenta,sai daga baya yace shi be saketa b shine tace atambaya mata ta saku ko aurensu nanan tunda ba ita yafada ma ba.Nagode


*Amsa*
Wa alaikum assalam,

Ta saku mana tun da saki ba'a wasa da shi in har ya fito daga baki  ko da wasa ne ba ya komawa, musamman kuma wacce aka yiwa sakin ta ji da kunnanta, ai karya ta kare.
Inkarinsa ba zai yi amfani ba, tun da an tabbatar ya furta.

Don neman karin bayani duba: Zadul-ma'ad 5/204.

A mazhabarmu a Malikiyya ta saku saki uku, amma akwai malaman da suke ganin za'a bar shi a saki daya, tun da saki uku A kalma daya Bidi'a ne, kuma haka  ake hukuntawa a zamanin Annabi S.A.W. da zamanin Abubakar RA da wani bangare na zamanin Umar RA .
Kamar yadda hadisin Ibnu Abbas ya tabbatar da hakan

Allah ne mafi sani.

*Dr, Jamilu Zarewa*

16/09/2017
Share:

ANGO YA MUTU KAFIN AMARYA TA TARE, YAYA BATUN GADO DA TAKABA ? Dr.jamilu yusuf zarewa

*_ANGO YA MUTU KAFIN AMARYA TA TARE, YAYA BATUN GADO DA TAKABA ?_*


*_Tambaya_*


Assalam Alaikum, Dr. an daura auren wasu yau ba'a dauko amarya ba sai gobe, amma Allah yayi wa angon rasuwa..tambayata anan wai shin za tayi takaba? Kuma tanada gadonshi?


*_Amsa_*
Wa'alaykumussalam

To dan'uwa idan miji ya mutu bayan an daura aure kafin ya tare da amryarsa, ya wajaba amaryarsa ta yi masa takaba, kuma a bata gadonta cikakke, kamar yadda Annabi S.a.w. ya yi hukunci da hakan ga Barwa'u 'yar Washik lokacin da mijinta ya mutu kafin su tare a hadisi mai lamba ta: 1145, wanda Tirmizi ya rawaito kuma ya inganta shi .

Allah ne mafi sani.

*_Dr. Jamilu Yusuf Zarewa_*

1/05/2016

Ga dukkan mai son shiga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH* sai ya yi saving wannan number +2348122248585  sannan ya tura da sunansa da adireshinsa ta whatApp. Duk abun da mutum ya turo matukar ba suna ba ne ba za a kula shi ba.
Share:

Thursday, 19 October 2017

RIGIJI GABJI! Ina Malikawan Nigeria! Toh yau dai ga Imamu Malik yayi gabas Dr Ahmad Gumi yayi kudu. !

DAGA MIMBARIN SALAFIYYAH NETWORK NIGERIA
!
LALLAI INDA MALIKIYYAR SUKE YI DA GASKE TOH DA KASHE DR AHMAD GUMI KAWAI ZA AYI DOGARO DA FATAWAR IMAMU MALIK DANGANE DA DUK WANDA YAYI MUSUN CEWA QUR'ANI BA MAGANAR ALLAH BANE INDAI HAR BAI TUBA YA JANYE KALMAR BA.
!
RIGIJI GABJI! Ina Malikawan Nigeria! Toh yau dai ga Imamu Malik yayi gabas Dr Ahmad Gumi yayi kudu.
!
Wannan ke 'kara tabbatar da cewa An shigo cikin rigar malikiyya ne kawai ana ta fesa ma al'umma gubar mu'utazilanci a Masallacin Sultan Bello Kaduna. Allah (T) ya ce AlQur'ani maganarshi ce Dr Ahmad Gumi kuma ya ce A'a halittar Allah ne. Lallai inda ace malikiyyan da ake yi na gaskiya ne toh da kashe Dr Ahmad Gumi kawai ya kamata ayi dogaro da wannan bayanin na Imamu Malik acikin wannan rubutun kamar haka:

قيدة الإمام مالك )رحمه الله( في القرآنذكر الإمام البخاري في )خلق أفعال العباد( عن مالك قوله"القرآن كلام الله"وذكر اللالكائي بسنده عن أبي محمد يحيى بن خلف المقري قال كنت عند مالك بن أنس سنة ثمان وستين فأتاه رجل فقال يا أبا عبد الله ما تقول فيمن يقول القرآن مخلوق قال "كافر زنديق اقتلوه"وذكر اللالكائي أيضا عن أبي الحسن بن العطار محمد بن محمد قال سمعت شريح بن النعمان يقول سالت عبد الله بن نافع وقلت له إن قبلنا من يقول القرآن مخلوق فاستعظم ذلك ولم يزل موجعا حزينا يسترجع قال عبد الله بن نافع قال مالك بن أنس من قال القرآن مخلوق يحبس حتى يعلم منه توبةوذكر ابن أبي حاتم بسنده عن ميمون بن يحيى البكري قال قال مالك بن أنس من قال القرآن مخلوق يستتاب فإن تاب وإلا ضربت عنقهوجاء في المدونة "قال ابن نمير: سمعت أبا مصعب يقول: سمعت مالكاً يقول: القرآن كلام الله غير مخلوق، قال أبو مصعب فمن شك أو وقف فهو كافر".وفي ترتيب المدارك للقاضي عياض" "قال ابن أبي أويس سمعت مالكا يقول: )القرآن كلام الله وكلام الله منه وليس من الله شيء مخلوق(
!
Fassara:
Imamul Bukhaariy ya ambaci maganar Maaliku cewa " Alƙur'aani maganar Allaah ne" (Khalƙu Af'aalil Ibaad)Kuma Allaalikaa'iy ma ya ambata daga Baban Muhammad Yahya ɗan Khalaf Almuƙ'riy yace: ina wajen Maaliku ɗan Anas a shekara ta ɗari da sittin da takwas,yayin da wani mutumi ya ce: Allaah gafarta baban Abdullaahi (Imamu Maalik) me zaka faɗi game da wanda yake cewa Alƙur'aani HALITTA ne? Sai yace:"KAAFIRINEZINDIƘI, KU KASHESHI"
!
Har ilaa yau Allaalikaa'iy ya saake ambata daga baban Alhasan ɗan Al-Atɗaar Muhammad ɗan Muhammad yace naji Shuraihu ɗan Annu'umaan yanacewa na tambayi Abdullaahi ɗan Naafi'u na ce dashi ansami daga cikin mutananmuwanda yake cewa ALƘUR'AANI HALITTA NE! sai hankalinshi ya tashi dajin haka, kuma bai gushe ba yana mai takaicin maganar da nuna damuwa matuƙa yana istirjaa'i (salati), Abdullaahi ɗan Naafi'u sai yace Maaliku ɗan Anas yace:DUK WANDA YACE ALƘUR'AANI HALITTANE za'a tsare shi har sai an tabbatar ya tuba daga shi (wannan muguwar aƙidar).
!
Ɗan Baban Haatimu ya ambaci magana ta hanyar Maimuun ɗan Yahaya al-Bakariy cewa Maaliku ɗan Anas yace: DUK WANDA YACE ALƘUR'AANI HALITTA NE, ZA'A NEMESHI DA YA TUBA, INYA TUBA SHIKENAN, IN KUWA YAƘI ASARE WUYANSA.Yazo a cikin Mudawwana (littafin Maalikiyyah) cewa " ɗan Numairin yace: naji baban Mus'abu yana cewa: naji Maaliku yana cewa: ALƘUR'AANI MAGANAR ALLAAH NE ba halitta bane.Sai baban Mus'abu yace: Duk wanda ya yishakkar haka ko kuma yace shi baruwanshi (ba zai ce halittane ko ba halitta ba) KAAFIRINE.
___________________
Muhammad Shittu Abu Uwaisat.
Share:

Dr. Gumi ya ce SALAF basu yi magana ba akan cewa shin Alqu'ani maganar Allah ne ko halittar sa ne ?? TOH AMMA KO SHIN WANNAN MAGANAR NA BABAN BOLA GASKIYA NE?

AN ZO INDA SU SHEIKH SA'IDU MAI KWANO GUSAU DA SHEIKH ALBANIY ZARIA SUKA CE MANA ANA NAN BABAN BOLA ZAI ISO WURIN.
!
BABAN BOLA YA JEFO WASU BOMABOMAN AMMA MALLAM  ABU AHMAD ATEEQ SULAIMAN YA TARWATSA SU DA IZININ ALLAH ASA'ILIN DA YA KAI ZIYARA BABBAN SHAFIN DA YAKE JAGORANTA NA 'YAN 'KUNGIYAR ANTI HADITH.
!
Dr. Gumi ya ce SALAF basu yi magana ba akan cewa shin Alqu'ani maganar Allah ne ko halittar sa ne ?? TOH AMMA KO SHIN WANNAN MAGANAR NA BABAN BOLA GASKIYA NE??
....
AMSA:
Mallam Abu Ahmad Ateeq yace: Dr. Gumi 'karya yake yiwa SALAF _ kuma dama ya saba yi musu 'karya _ , wannan mas'alar tana daga cikin matsalolin da babu wani littafi na SALAF da zaka ga bai tattauna ta ba . Da ace Dr. Gumi ya karanta littafin RISALA na fi'khun MALIKIYYAH , da yaga yanda SALAF suka tattauna mas'alar tun daga mu'kaddimar littafin .

2. Dr. Gumi yace malaman Musulmi magabata sun yi kuskure saboda rashin sani , da suka tafi akan cewa AL'KUR'ANI MAGANAR ALLAH NE !!! TOH AMMA KO SHIN WANNAN MAGANAR NA BABAN BOLA GASKIYA NE??
..
AMSA :
Anan DR.GUMI ya warware maganar sa ta farko , ya fa'da cikin wacce tafi ta farkon muni !! Dama haka 'yan bidi'a suke , basa tabbatuwa akan matsaya 'daya ; kullun suna cikin ru'dani !!!
Bai kamata ba Dr. Gumi ya kuskurantar da magabatan Musulmi akan IJMA'IN su akan cewa Al'KUR'ANI MAGANAR ALLAH ne , tunda sun dogara ne akan nassoshi na shari'a akan wannan matsayar tasu , daga cikin nassoshin akwai kamar haka :
ALLAH YA CE :
" ﻭ ﺇﻥ ﺃﺣﺪ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺸﺮﻛﻴﻦ ﺍﺳﺘﺠﺎﺭﻙ ﻓﺄﺟﺮﻩ ﺣﺘﻰ ﻳﺴﻤﻊ ﻛﻼﻡ ﺍﻟﻠﻪ "
Saboda haka , abunda ya kamata Dr. Gumi yace shine
:
" Allah ya yi kuskure da yace Al'ku'ani maganar sa ne
...
3. Dr. Gumi yace SALAF da suka ce Al'kur'ani maganar Allah ne , hakan da suka ce babu komai lura da yanayin zamanin su , amma Mu a wannan zamanin dolene mu sauka dàga wannan matsaya ta SALAF , sai mu 'kudurta cewa Al'kur'ani HALITTA ne !! TOH AMMA KO SHIN WANNAN MAGANAR NA BABAN BOLA GASKIYA NE??
..
AMSA :
A'a Dr. Gumi , Mu SALAF sun wadatar damu , kuma Mu bama ganin AQIDAR MUSULUNCI tana sauyawa saboda banbancin zamani . Amma kai da kake ganin ana iya yiwa musulunci
gyare _gyare sa'banin yanda yake , to kana iya fita ma daga cikin sa , wannan matsalar ka ce !!!
!
MU TARA A DARASI NA GABA DON JIN CI GABAN WADANNAN AQEEDUN MU'UTAZILAWAN DA AKE DASAWA A MASALLACIN SULTAN BELLO KADUNA.  ALLAH (T) MUKE ROKO DA YA TSARE MANA IMANINMU.
Share:

Wednesday, 18 October 2017

Kissa:- miyasa sai banu umayya??




*ME YA SA SAI BANU UMAYYA?!*
   
(Rubutun Babban Masanin Tarihi, Dr. Ali as-Sallabiy).

Ibnu Kathir (r) yana cewa:

"Kabilar Banu Umayya sun ci kasuwar Jihadi; ba su da abin yi sai shi. Sun kaskantar da kafirci da kafirai. Kwarjinin Musulmi ya cika zukatan kafirai. Ba sakon da Musulmi su ka sa a gaba face sun ci shi da yaki."

Ba a san wata Kabila da ta yi mulki ta yi wa mutane abin da Kabilar Banu Umayya (r) ta yi musu ba. Banu Umayya suna da falala a kan al'ummar Musulmi tun kafuwar Musulunci har zuwa ranar al-kiyama. 

* Uthman dan Affan dan kabilar Banu Umayya ne. Shi ne ya tattara al-Kur'ani.

* Ummul Muminina, Ummu Habiba 'yar Abu Sufyan (r) 'yar kabilar Banu Umayya ce. Ta ruwaito mana sunnonin Manzo (SAW) ma su yawa.

* Mu'awiya dan Abu Sufyan dan kabilar Banu Umayya ne. Daya ne daga marubuta wahayi.

* Abdullahi dan Sa'id dan al-As dan Kabilar Banu Umayya ne. Daya ne daga shahidai goma sha uku na Badr.

* Yazid dan Abu Sufyan dan kabilar Banu Umayya ne. Shi ne ya shigar da Musulunci Lebanon; ya jagoranci rundunonin Sham.

* Yazid dan Mu'awiya dan kabilar Banu Umayya ne. Shi ne kwamandan rundunar farko da ta yaki Kusdandiniyya (Istanbul); Annabi (SAW) kuma ya ce "An gafarta wa rundunar farko da ta yi yaki a Kusdandiniyya).

* A cikin Banu Umayya a ke da Khalid dan Yazid. Shi ne ya kirkiro ilimin kimiyya.

* A cikin Banu Umayya a ke da Ukbatu dan Nafi'u (r). Shi ne ya kai Musulunci arewacin Afirka.

* A cikin Banu Umayya a ke da Umar dan Abdul Aziz.

* Wanda ya gina 'Kubbatul Sakhrah' (ta Masallacin Kudus), Abdul Malik dan Marwan, dan kabilar Banu Umayya ne.

* Banu Umayya ne suka kai Musulunci Andalus da Armenia da Azerbaijan da Georgia. Haka ma Turkiyya da Afghanistan da Pakistan da Indiya da Ozbakistan da Turkumanistan da Kazakhstan. Duka sun shiga Musulunci ne a hannun mahayan Banu Umayya.

* Banu Umayya ne suka kai Musulunci Turai; dama dai Andalus Banu Umayya ne suka bude ta. Kudancin Faransa bai taba zama kasar Musulunci ba sai zamanin mujahidan Banu Umayya.

* Abdurrahman Addakhil dan kabilar Banu Umayya ne. Shi ne ya ceto Andalus daga rugujewa.

* Abdurrahman Annasir dan kabilar Banu Umayya ne. Ya kasance daga manyan sarakunan duniya. Banu Umayya sun baza manzanninsu a lungu da saqon duniya suna kiran mutane zuwa ga addinin Allah (SWT); Manzannin Banu Umayya sun kai Musulunci China, wadanda su ka musu lakabi da *(masu fararen kaya)*.

* Ilimi ya yadu an yi mulki da adalci a zamanin Banu Umayya, a ka fara tattara hadisan Annabi a mulkin Banu Umayya.

* A zamanin Mulkin Banu Umayya a ka fara tattara hadisan Annabi, suka fassara kundaye zuwa larabci, su ka yi takardun kudin na Musulunci, su ka kera jirgin ruwan yaki na Musulunci na farko a tarihi.

* A zamanin mulkin al-Walid dan Abdul Malik dan kabilar Banu Umayya Musulunci ya yi kasaitar da bai taba yin irinta ba a tarihi.

* A zamanin Banu Umayya aka yi kiran sallah a duwatsun Himalayan kasar Sin, da qungurmin yankin Afrika da dazukan kasar Indiya da ganuwar Kusdundiniyya da kofofin Faris, da jigayin Portugal da gabban bakin kogi da fakon Georgia da bakin kogin Cyprus.

* A duk wadannan garuruwan farar tuta ce ta Banu Umayya dauke da kalmar *(La ilaha illallah Muhammadun Rasulullah)* ke kadawa.

*Allah Ya sakawa Banu Umayya kan abin da suka yi wa Musulunci da Musulmi.*

Da wannan na ke ganin dalilin da ya sa suka kafawa Banu Umayya kahon zuka.

Ga dukkan mai son shiga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH* sai ya yi saving wannan number +2348122248585  sannan ya tura da sunansa da adireshinsa ta whatApp. Duk abun da mutum ya turo matukar ba suna ba ne ba za a kula shi ba.
Share:

Archive

Unordered List

Support