Menene Hukuncin lika Ayatul Kursiyyu Abango da Nufin neman kariya? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Tuesday 7 November 2017

Menene Hukuncin lika Ayatul Kursiyyu Abango da Nufin neman kariya?

*Tambaya ta (219)*

*Menene Hukuncin lika Ayatul Kursiyyu Abango da Nufin neman kariya?*

الحمد لله واحد القهار.

*AMSA:*Lika Ayatul kursiyyu ko qananun alluna ajikin gida ko mota ko shago, ko makaranta ko wajan kasuwa, akwai barna mai yawa acikin hakan, bisa Abunda shari'a ta hana.

@ - Mafi Rinjaye Ana likawa ne dan Ado da gayu, wanda bango ana sanya masa launuka na fenti hakan saiya zama sababi na wulaqanta Alqur'ani.
Wannan yana daka cikin juyar da Alqur'ani daka manufar saukar dashi, daka shiriya da wa'azi kyakkyawa dakuma Ibada da tilawarsa dasauransu..

Alqur'ani Ba'a Saukar dashi danyiwa bango Ado dashi ba, an Saukar dashi dan shiriya ga Mutane, dakuma Bayani.

2- Wasu Suna likawa ne dan Neman tabarruki, Wannan Bidi'ane Tabarruki Mai kyau shine bauta da karanta Alqur'anin, Bawai likashi ajikin bango ko juyashi zuwa jikin Alluna masu Ado ba.

Sannan Yin hakan yasabawa Abunda Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yake akai, da khalifofinsa shiryayyu Allah yakara yarda dasu, dukkan Alkhairi yana cikin binsu, bawai wajan Saba musu ba,

Tarihi yanuna wannan dabi'a taliqa karamin Allo mai dauke da ayatul kursiyyu ko wani Bangare na Alqur'ani ajikin gida ko mota ko kasuwa, ba'a fara yinsa ba sai bayan shudewar  Nagartattun Musulmi sai lokacinda Musulmai suka zama masu rauni a'aqida da ilmi dariko da Addininsu.

Haka nan Lika irin wannan alluna dauke da Alqur'ani hanyace dazatakai Mutum ga shirka, domin Wasu suna qudurta cewa wadannan kananun Alluna da'ake likawa akasuwa ko mota ko gida kariyane ga gidan ko motar daka Wani Sharri, qudurce wannan kuma Shirkane.

Mai bada kariya na Hakika shine Allah, daka cikin dalilan da zaisa kuma yabawa Mutum kariya shine tilawar Alqur'ani ka yin zikirori wadanda Sukazo acikin hadisai Ingantattu, bawai likashi abangon gida ko mota ba.

Adunqule dai bai halatta rubuta ayar Alqur'ani abangon gida ko sanya karamin Allo ajikin mota ko shago ba, koda abangon masallacine bai halatta ba, bidi'ane.

Sanyawa kuma tareda qudurce bayar da wata kariya ga Mutum wannan kam Shirkane.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك نشهد أن لا إله إلا أنت نستغفرك ونتوب إليك.

🖊 *Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai*
*+2347033406106.*
*+2348140925493.*
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support