MENENE HUKUNCIN WANDA YAYI SALLAH ALHALI YASAN YANA CIKIN JANABA?? ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Friday 3 November 2017

MENENE HUKUNCIN WANDA YAYI SALLAH ALHALI YASAN YANA CIKIN JANABA??

*MENENE HUKUNCIN WANDA YAYI SALLAH ALHALI YASAN YANA CIKIN JANABA??*

الحمد لله رب العالمين.

Amsa: Abune sananne awajan musulmi cewa tsarkin  hadasi babba ko karami, wajibine, kuma sharadine na ingancin sallah, duk wanda yai sallah bashi da tsarki da gangan koda mantuwa sallarsa batacciyace bataiba, saiya sake, idan daganganci yayi hakika ya aikata babban laifi cikin manyan laifuka dakuma zunubi mai girma.

Shaikul islam ibnu taimiyyah rahimahullah yace:

"Musulmi kada yayi sallah a inda ba alkibla bane, kada yayi sallah batare da alwala ko ruku'u ko sujjada ba, wanda ya aikata haka yacancanci zargi da uquba,
Min hajussunnah (5/204).

Hakika gargadi mai tsanani yazo gawanda ya aikata haka;

Hadisi daga Abdullahi dan mas'ud yardar Allah takara tabbata agareshi daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam yace: (Anyi Umarni ayiwa wani bawa daka cikin bayin Allah bulala dari acikin kabarinsa, bai gusheba yana tambayar dalilin bulalar dakuma rokon asassauta masa harsaida ya rage saura bulala daya, sai aka karasa masa dayar, aka cika kabarinsa da wuta, lokacin da'aka dauke masa azabar bayan yafarfado sai yace kusanar dani sabo dame akaimin bulala? sai akace dashi kayi sallah ne sau daya batare da tsarki ba, kawuce tawajan azzalumi kuma baka taimakeshiba) Addahawi yaruwaitoshi acikin mushkilil Ãàsaar Albani ya hassanashi acikin silsila saheeha (2774).

Malamai sunyi ittifaqi akan duk wanda yai sallah batare da tsarki ba yana mai halatta hakan, ko saboda isgili, hakika yakafirta, za'a nemi yatuba, idan bai tubaba za'a kasheshi.

Amma idan mutum yai sallah batare da alwala kawai dan wulakanta sallah, bai halatta hakan ba kuma ba izgili yakeba,  Imamu Ahmad yatafi akan cewa mutum yakafirta, jamhurdin malamai kuma sukace: bai kafirta ba, saidai abunda yayi babban laifine cikin manyan laifuka.

Imamun nawawi rahimahulla yace:

Idan mutum yasan yanada hadasi kuma yasan sallah batsarki haramunne, abunda yayi laifine babba cikin manyana laifuka, baya kafirta awajanmu, saidai idan yahalatta sallah batsarki ne, Abu hanifa yace yakafirta saboda izgilinsa.

Abunda yake wajibi akan wanda yai sallah babu tsarki shine yatuba, yayi istigfari, yakuma kuduri niyyar bazai sake aikata hakan ba, sannan saiya sake sallar daya sallata batare da alwala ba, Allah madaukakin sarki yana karbar tuban wanda yatuba yakoma gareshi.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.

Tambayoyin musukunci
Watsapp group
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support