Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Friday, 7 July 2017

Hukuncin qasru 8

*HUKUNCIN SALLAR QASRU-8!!!???*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Taken Lekca........
.
*SALLAR QASRU!!!!??*
.
Wannan shine bayani na takwas****
.
Cigaba***
.
.
_Acikin Alwajiz fi fiqhus sunnah, malam yace malamai sunyi sabani gameda nisanda tafiya zatakai kafin ayi mata qasru, Ibnul Munzir ya hikaito sabanin malamai samada  maganganu 20 gameda nisanda tafiya zata kai kafin ayi mata qasru, wato kenan kamar yanda nagaya muku abaya, ita qasru kusan duk wata gaba da zaka dauka nata seka tarar anyi sabani acikinta, toh shiyasa zeyi wahala ayi magana akan sallar qasru batareda kayima wani raddiba***_
.
_Shi kansa Imamu malik acikin muwadda, babi guday yabude akan wannan matsalar ta nisanda tafiya zatakai kafin ayimata qasru, toh amma shima acikin babin zakuga hadisanda yakawo kusan gaba dayansu sunacin karo da juna, wanda imamu malik akarshe kawai seya zabi guda daya daga cikin maganganunda yakawo kawai yace shi kam yafison wannan, wato itace buridi hudu***_
.
_Acikin Mudauwanah kuma imamu Malik cewa yayi kawai dazarar kafita daga garinku toh kawai kafara qasru***_
..
_Imamul qurdubi yakawo ruwayar Harith dan Abu rabi,ah cewa shi alokacinda yayi shiri zeyi tafiya sekawai yaima abokan zamanshi limanci kuma qasru yayi, agidanshi bema fara tafiyarba, shine qurdubi yace: shi yana fassara *(DARABTUM)* da Allah yafada awaccan ayar, da ma,anar *(AZAMTUM)* kamar yanda bayani yagabata abaya***_
.
_Har ila yau qurdubi yakawo fahimtar Imamu mujahid wanda shi yana ganinma matafiyi baze fara qasruba aranarda yayi tafiyar harse dare yayi tukunna sannan zaka fara qasrun***_
.
_muma dai anan bazamu iya yanke hukunciba gaskiya dan sabanin yayi yawa wallahi kuma dukkansu suna karo da juna, ammadai bari muji abindasu Ibn taimiya zasuce kafin musan tudun dafawa***_
.
_Ibn qudama yana cewa idan da zaka hado kakaf sabaninda akayi gameda qasru, katara maganganun wayanda suke cewa sai tafiya takai nisan kaza sannan ake mata qasru, kokuma sai tafiya iri kaza akeyiwa qasru, Ibn qudama yace su kansu zaka samu maganganunsu sunacin karo da juna, ibn qudama yace idan kagama tara maganganun toh zaka samu wanda yake cewa sai ankai wani nisa bashida hujjah, yace: amma hujjah tana wajen wanda yace maka kawai duk tafiya kayi qasru, kuma bai kayyade maka nisaba***_
.
_Ibn qudama acikin mujallad na uku Almugni yace: duk wanda zaice maka se tafiya takai nisan kaza kokuma kwanaki kaza akeyin qasru toh wannan yanaso yarabakane da sunnar Annabi muhammad***_
.
_Ibn Taimiya acikin fatawa yace wannan maganar ta ibn qudama baidace asamu wani mutum yana saba mataba, saboda yace inhar sunnah kakeso toh Allah da manzonshi basuce ga wani adadin tafiyarda zakayiba kafin kayi qasru, kuma basuce sai tafiya iri kaza akeyiwa qasruba, ibn taimiya yace manzon Allah har yamutu baice se tafiya takai nisan kaza kafin ayi qasruba, kuma har yabar duniya baice inka zauna agari kwana kaza kadena yin qasruba***aduba majmu,u fatawa mujallad na 23, yace duk mutuminda yace maka sai tafiya takai nisan kaza akeyin qaaru toh wannan maganar tashi babu ita Alittafin Allah kuma babu ita a sunnar Annabi muhammad***_
.
_Ibn qayyum Aljauziyya acikin zadul ma,ad mujallad na farko shafina 481 shima yace: manzon Allah har yabar duniya baice idan kayi tafiya kwanaki kaza toh kayi azumi, kuma baice inkayi kwanaki kaza kacika sallah, kawai yanda Allah yace acikin qur,ani idan kayi tafiya toh karama azumi awasu ranaku nadaban, baice inkayi kwanaki kaza kacika azumiba, yace amma duk wanda zaice maka ga wasu kwanakinda zakayi qasru toh wannan maganar bata ingantaba kuma bata cikin sunnar Annabi muhammad (s.a.w)***_
.
_Saboda haka abinda yafi dacewa shine mudauki waccan maganar ta Ibn Qudama semu gina hukuncinmu na karshe akanta, yanzu dai kunji irin yanda malamai suka tafka wayannan sabani, toh kuma duk wanda kadauka aciki toh sauran kuma kayi musu raddine fa***_
.
_Misali idan kace mutum baze fara qasruba harse ya wuce gonaki, toh kaga kayi raddima wanda yace kana iya farawa tun kana gida, sannan kuma wanda yace bazaka fara aranarda kayi tafiyarba shima kaimasa raddi, gakuma wanda yace sai kaci mil uku shima kaimasa raddi, ga wanda yace sekaci buridi uku shima kayimai raddi, ga wanda yace gidaje zaka wuce ba gonakiba shima kai masa raddi, gakuma wayanda sukace kwata kwata ba,ayin qasrun sai ahalin tsoro kaga suma kai musu raddi, toh yanzu dan Allah menene mafita yanda zakaima wayannan mutanen adalci batareda kayima kowannensu raddi ba????_
.
_Sannan kuma idan kace mudauki fahimtar malamanda sukace qasru ba,a wuce sati biyu anayi, in mutum yawuce sati biyu sai ya cika sallah, toh kaga semuce wannan maganar taka raddi ce ga mazhabar malikiyya da shafi,iyya dasu imamu laisu da dabari, wayanda sukace kwanaki uku kawai akeyi, kuma raddi kakeyima su imamu Ahmad dasukace salloli 21 kawai akeyi, sannan kuma suma wayanda sukace qasru batada iyaka suma kayi musu raddi****_
.
_Yawaitan wayannan sabanin shine yasa mukace arike waccan maganar ta Ibn Qudama, wato mutattara musu sabaninsu mu ajje musu mukoma mudauki zahirin ayar qur,ani da hadisin manzon Allah (s.a.w)***_
.
_kenan semuce nafarko dai sunnah shine duk sanda kayi tafiya toh kayi qasru koda kuwa tafiyar taka ta sabon Allah ce, saboda   Allah da manzonshi basu kebance wata tafiya sukace ita ba,a yinmata qasruba****_
.
_Na biyu kuma koda shekaru nawa zakayi a garinda kaje toh ya halasta kayi qasru harse kadawo, saboda aikin manzon Allah (s.a.w) ya nuna hakan, tunda ayakin tabuka be dena qasruba har seda yadawo gida, hakama zamanshi a makka kwanaki goma a hadisin Anas, awani hadisin kuma kwanaki 19***_
.
.
_Sai abiyomu acikin bayani nagaba zamu cigaba in Allah yaso****_
.
.
_Almajirinku kamar kullun_
.
```Jameel Alhassan Haruna Kabo```
_(Abu khausar)_
 .
.
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
https:/t/m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka  Wanatubu ilaika
Share:

Hukuncin qasru 7

*HUKUNCIN SALLAR QASRU-7!!!???*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Taken Lekca........
.
*SALLAR QASRU!!!!??*
.
Wannan shine bayani na bakwai****
.
Cigaba***
.
.
_Kamar yanda kukaji abaya cewa Annabi har yabar duniya duk sanda zeyi tafiya qasru yakeyi, ba,a taba samun inda yacika sallah ba, kuma baice inkayi tafiya tawuce kwanaki kaza ba kacika sallah, ballantana ma gakuma wannan shahararren hadisin na yakin tabuka, inda Anas yace Annabi (s.a.w) yakwashe kwanaki 20 yanayin qasru***_
.
_Gakuma hadisin bukhari wanda yana cikin Bulugul maram wanda Anass yace manzon Allah ya kwashe kwanaki 19 agarin makka yana yin qasru****_
.
_saboda haka mafi ingancin magana shinw sallar qasru batada wani adadin kwanakinda ake denewa***_
.
_Kuma abinda ya tabbata a qur,ani da sunnah shine kawai duk sanda kayi tafiya toh yahalasta kayi qasru, koda tafiyar bata addini bace**_
.
_Matar aure wacce tayi aure awani gari wanda ba nasuba toh duk sanda zatazo ganin gida qasru zatayi duk da cewa gidan iyayenta tazo toh qasru zatai tayi harse takoma gida koda kwanaki nawa zatayi****_
.
_Dalubai wayanda suka zuwa makarantar kwana kuma qasru zakuyitayi harse kundawo koda kuwa shekaru nawa zakuyi acan, abinda Allah yace kawai inkunyi tafiya babu laifi kuyi qasru toh ga tafiya kunyi kunzo makaranta dan haka sekucigaba dayin qasru har zuwa lokacinda zaku koma gida****_
.
_Alhazai wayanda suke zuwa aikin hajji da masu umura kuma qasru zakui tayi harse kundawo***_
.
_Yan kwallo wayanda suke zuwa wata kasa domin sana,ar kwallo toh kuma qasru zakui tayi harse kundawo*****_
.
_Barawo wanda zaije wani gari domin yayi sata, toh kaima qasru zakaitayi har sekadawo, hakama dan fashi wanda zaije ya tare hanya kaima qasru zakayi harse ka dawo*****_
.
_karuwa wacce zataje wani gari danufin tayi zina kema qasru zakiyi tayi harse kindawo***_
.
_Kana aikine a ofishin jakadanci wata kasa, toh kaima qasrun zakaitayi harse ka dawo***_
.
_Abinda Allah yace kawai shine idan kunyi tafiya babu laifi kuyi qasru, amma Allah baice banda tafiya iri kaza, banda iri kaza ba, toh duk wanda zezo yacire mana wata nau,in tafiya yace mana ita ba,a yin qasru toh yazama dole yabamu aya ko hadisinda yace hakan, kukaranta tafsirin qurdubi jama,a cikin mujallad na biyar shafina 256***_
.
_Amma kamar wanda yake aiki awani gari aiki irinna zama, kamar soja ko dan sanda da sauran irin wayannan, toh wancan garinda aka kaika shine garinku ayanzu dan haka awannan garin kai bazakayi qasruba, cika sallah zakayi domin kai ba matafiyi bane, amma sanda kakoma garinku dan ganin gida da iyayenka toh anan kuma qasru zakayi tunda yanzu bakone kai, amma idan anturaka wani gari na wucin gadi kamar kunje aikin wanzarda zaman lafiya wata kasa akace zakuyi shekara daya acan kokuma fiyeda haka, wato andai qayyade lokacinda zakuyi kafin kudawo gida toh qasru zakui tayi harse kundawo gida koda shekaru nawa akace zakuyi***_
.
_shima mutuminda yakeda mata biyu misali amma ba a gari daya sukeba, wannan tana nan waccan tana can, toh shima babu qasru akanshi, duk inda kake yanzu gidane dan haka cika sallah zakayi, matukar ba wani akine yakawoka wani garinba wanda kake nufin inka gama zaka koma gida***_
.
_Na,am ansamu jumhurin malamai suna suna cewa wai tafiya inhar ta sabon Allah ne, wai baza,ayi qasruba toh wannan maganar tasamu kai tsaye basuda hujjah, kawai qiyasi sukeyu kuma irin kiyasinda ake cewa ma,al fariq***_
.
_Amma Allah duk idan yatashi yin sauki ga Al,umarsa zaka samu baya warewa, ko awajen azumi cewa yayi inkunyi tafiya ku ajjiye azumi, baice banda tafiya iri kaza da iri kaza ba, hakama sallah cewa yayi in kunyi tafiya abayan qasa kuyi qasru amma baice banda tafiya iri kaza da iri kaza ba, hakama manzon Allah bai ware wata tafiya yace banda itaba har yabar duniya***_
.
_kawai duk tafiyarda kayi kowacce irin tafiyace koda sata zakaje kayi ko karuwa zataje tayi zina, duk ya halasta suyi qasru harse sundawo, kuma wannan itace fahimtar Abu hanifa da auza,i da sufyan Assaury, kai shi kanshi imamu malik ansamu ruwaya daga wajenshi inda yake cewa duk tafiyarda zakayi toh yahalasta kayi qasru koda kuwa tafiyar ta haram ce***aduba Almuhalla ko Almugni na ibni qudama, kokuma Majmu,ul fatawa ta ibn taimiya***_
.
_Sukuma wayanda suke cewa wai banda tafiyar sabon Allah suna kafa hujjah ne da ayoyinda suke cikin suratul ma,ida da wacce take suratul baqara gameda hukuncin cin mushe sukace ai Allah daya halasta cin mushe ga masu larura, bai halastashi ga mutanen banzaba, toh shine suka dauko hukuncin cin mushe sukayi kiyasinshi da sallah, amma ibn taimiya yai musu raddi acikin majmu,ul fatawa mujallad na 24, ya raunana wannan maganar tasu***_
 .
_hakama ibn qayyum acikin zadul ma,ad yayi raddin maganar***_
.
_Amma babu shakka sharadinda Allah yaimana shine idan munyi tafiya abayan qasa babu laifi muyi qasru, amma duk wanda zaice banda dan fashi, banda karuwa banda kaza banda kaza, toh wannan maganar tana bukarar dalili nassi qur,ani ko hadisi ba wani kiyasiba, yan uwa***_
.
_Amma babu wata hujjah ta alqur,ani ko hadisi wacce tace me tafiya ta haramun bazeyi qasruba, babu wannan A qur,ani kuma babushi a hadisan Annabi muhammad, shin ko kuna gani Allah da manzonshi basusan akwai mutanen banza masu yin tafiya bane??***_
.
.
_zamu dakata anan sekuma fitowa tagaba idan Allah yakaimu***_
.
.
.
_Almajirinku kamar kullun_
.
```Jameel Alhassan Haruna Kabo```
_(Abu khausar)_
 .
.
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
https:/t/m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka  Wanatubu ilaika
Share:

Hukuncin qasru 6

*HUKUNCIN SALLAR QASRU-6!!!???*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Taken Lekca........
.
*SALLAR QASRU!!!!??*
.
Wannan shine bayani na shida****
.
Cigaba***
.
.
_Idan baku mantaba acan baya nakawo muku yanda aka tafka sabani gameda adadin kwanakinda mutum zeyi yana yin qasru, daga ciki nakawo fahimtar Imamu malik da shafi,i da Laisu bin sa,ad da dabary wayanda sukace kwanaki uku akeyi, kuma nace wannan maganar abarta batada inganci, toh cewa danayi ba kwanaki uku bane adadi qasru hakan yaharzuwa wasu masu da,awar bin mazhabar malikiyya, wanda har hakan yasa nadan tsawaita harshe akansi abayaninda yagabaci wannan***_
.
_Toh Imamul qurdubi shima dan malikiyyane toh aduba tafsirinshi mujallad na biyar shafina 258 yakawo sabanin malamai sosai gameda adadin kwanakinda akeyin qasru, toh yanzu misali incemuku kwanaki uku kawai akeyi ana qasru,  shin toh inakuma batun su Sa'idu bin musayyib wanda shikuma malamin malaman imamu malik ne, gakuma Abu hanifa da imamus sauri wayanda sukace kwanaki 14 akeyi ana qasru kenan idan nace kwana uku, ai kunga nawatsarda maganarsu, bayan kuma sunfi imamun malik daraja dan su tabi,aine wato Almajiran sahabbai***_
.
_Toh idan zamu dauka kamar yanda kukace, kin amfanida fatwar imamu malik kukace cin mutuncinshine kokuma zaginshi, toh shikuma imamu malik din menene hukuncinshi daya bada fatwarda ta sabama tasu Abuhanifa da sa'id nin musayyib?? Kenan shima ya zagesune kokuwa yaci mutuncnsu??***_
.
_cewa dakukayi 'yan salafiyya wai mazhabar Albani sukebi toh ashe Saleem Ibn ed Alhilali bashi bane yatattaro dukkanin muwaddodin wayanda akai ruwayarsu awajen imamu malik yahadasu waje guda?? Kuma ai saleem Almajirin Albanine, shin idan Albani bayason imamu malik har za,a samu dalubanshi suna wannan aiki na tattara muwaddodinnan awaje guda???***_
.
_toh wallahi kaunar imamu malik mu awajenmu aqeedace kuma duk wanda baya son imamu malik toh dan bidi,a muke daukarshi, amma wannan baya hukunta semunbi malik a inda yayi kuskure***_
.
_hakanan itama wannan maganar tasu Abu hanifa dasu Ibn musayyib dasukace qasru ba,a wuce sati biyu, itama wannan maganar me raunice mu ajjeta***_
.
_gakuma su Ahmad bin hambal wayanda sukace salloli 21 kamar yanda kukaji abaya***_
.
_toh yanzu dan Allah jama,a muyi adalci, gadai wayannan malaman sunyi sabani, kuma duk wanda muka ajje mabiyanshi zasuce mun wulakantashi, toh kenan dan Allah ya zamuyi???***_
.
_mafita kawai guda dayace, kamar yanda Allah ta,ala yace: idan kunyi jayayya gameda wani abu toh kumaidashi zuwaga Allah da manzonshi***_
.
_kafin mukai can ma toh gama wata riwaya daga imamu malik tana cikin muwadda daga Nafi'u yace: Abdullahi dan umar ya zauna amakka tsawon kwanaki goma yana qasru***_
.
_Imamul Qurdubi shima dan malikiyya ne, kuma yakawo wani asari dayace Anas dan malik yaje garin naisabur yakwashe kwanaki 60 acan yanayin qasru***_
.
_sannan shi qurdubin yakawo ruwayar  Abu mijlaz daya tambayi Ibn umar cewa zanje garin madina saboda wata bukata kuma zan zauna acan tsawon watanni bakwai ko takwas shin yaya zanyi sallah? Sai yace: kaita yin qasru***_
.
_Awata Ruwaya ta Anas dan malik (Ra) yace: Allah ya farlanta sallah akan harshen Annabinku, ahalin zaman gida raka,a hudu hudu, ahalin tafiya raka,a biyu biyu, ahalin tsoro kuma raka,a daya***_
.
_gakuma hadisin sayyadina umar yace: Sallar matafiyi raka,a biyune, sallar juma,a itama raka,a biyune, sallar idi karama raka,a biyune, babbar sallah itama raka,a biyune, kuma haka haka suke acike ba ragesu akayiba, dama can haka suke akan harshen Annabinku, wanda kuma yayiwa Annabi karya toh ya tabe***_
..
_kunji wayannan hadisan, wayanda suma masu ganin cewa dolene natafiyi yayi qasru, toh suna kafa hujjah da wannan hadisin na umar, wanda shima daliline akan cewa matafiyi asali gameda sallarshi dama can raka,a biyune, kuma umar yace wanda yaima Annabi karya toh ya tabe***_
.
_nan kusa kusa jama,a kuduba ALWAJIZ FI FIQHUS SUNNAH, wayannan hadisanfa sunanan aciki, bama se anje da nisaba***_
.
_Gakuma hadisin Anas dan malik yace: lokacinda muke dawowa daga makka zuwa madina tareda Annabi muhammad yakasance yana mana raka,a bibbiyune har muka iso gida, sai wani ya tambayeshi: shin Annabin ya zauna acan makka dinne?? Sai Anas yace eh ya zauna kwanaki goma acan kuma qasru yakeyi****_
.
_Toh ga dungurun gum kenan: Annani muhammad yazo makka wacce mahaifarshice amma ya kwashe kwanaki goma yana qasru****_
.
_Ibn taimiya acikin majmu,ul fatawa yace idan mutum yayi tafiya toh yarika yin sallah raka,a bibbiyu wannan shine sunnar Annabi muhammad, da khulafa,ur rashidun***Ibn taimiya yace Annabi (s.a.w) har yabar duniya duk sanda yayi tafiya qasru yakeyi, hakanan Abubakar da umar, da usman afarkon lokacin khalifancinsa***_
.
..
_zan dakata anan sekuma bayani nagaba idan Allah yakaimu***_
.
.
.
_Almajirinku kamar kullun_
.
```Jameel Alhassan Haruna Kabo```
_(Abu khausar)_
 .
.
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
https:/t/m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka  Wanatubu ilaika
Share:

Hukuncin qasru 5

*HUKUNCIN SALLAR QASRU-5!!!???*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Taken Lekca........
.
*SALLAR QASRU!!!!??*
.
Wannan shine bayani na biyar****
.
Cigaba***
.
.
_Kwanakin baya nataba yin wani rubutu gameda sallar qasru, nace batada adadin kwanaki, toh hakika nasamu kalubale meyawan gaske musamman awajen masu taqlidanci da mazhabar malikiyya, sunci mutuncina sosai saboda nace sallar qasru batada adadin kwanaki, wanda hakan kuma su yasabama mazhabarda sukebi ta malikiyya, wacce nakawo muku fahimtar imamu malik acan baya inda nace dashi da Shafi,i da wasu malamai suna ganin cewa anayin qasrune kwanaki uku kawai, wato matafiyi idan yayi tafiya zeyi qasrune na kwanaki uku, inhar kawuce kwanaki uku acan garinda kaje sukace zaka cika sallah***_
.
_Toh Alhamdulillahi nidai ba dan malikiyya bane, sannan kuma ba imamu malik nakebiba, Annabi muhammad aka turomin ba imamu malik ba***_
.
_Amma aqidarda nakeba ta salaf, mu awajenmu kaunar Imamu malik Addinine, kuma aqidace, awajenmu duk wanda bayason imamu malik toh dan bidi,ane, kuma makiyinmune, saboda hadisanda muke aiki dasu, wayanda Imamu malik yaruwaito muna basu wata daraja ta musamman, amma munada tabbacin imamu malik yana kuskure tunda shima mutum ne kamar kowa kuma ba ma,asumi bane, sannan kuma akwai malamai dayawa wayanda suka fishi ilimi da daraja nesa ba kusaba, tunda shi imamu malik ba sahabi bane, baiga manzon Allah ba, sannan kuma ba tabi'i bane tunda bai taba gani wanda yaga manzon Allah ba, amma munyarda cewa babban malamine wanda zan iya cewa azamaninshi babu irinshi, kuma aqidarshi aqidace mekyau wanda muke kyautata masa zato, kuma muna sonshi fiyeda yadda mukeson iyayenmu wayanda suka haifemu***_
.
_Amma shi imamu malik da bakinshi yake cewa *MA MINNA ILLA RADDUN, WA MARDUDUN ALAIHI* wato dukkanmu malaman musulinci muna acikinmu kowannenmu yana yima wasu raddi, kuma shima ana yimai raddi, ashe kenan ba abun mamaki bane dan imamu malik yabada fatwa anki akarbeta wannan baya nuna cewa an wulakanta malik kokuma anzageshi***_
.
_Kukaranta Sweedy acikin tanwirul hawalik, yakawo maganar imamu malik lokacinda Sarki Abdulmalik yanemeshi da yabada muwaddarshi dan tazama kundin musulinci wacce za,arika hukunci da ita adukkan kasashen musulinci, amma imamu malik sai yace: Aa sahabbai sun watsu aduniya kuma sun watsa karatu dan haka akwai hadisai dayawa wayanda ni bansansuba dan haka baze yiwuba ace littafina kadai za,a rika hujjah dashi***toh kunji imamu malik dakanshi yayiwa ilimi Adalci toh danme wani ayau zezo yace dole semunbi mazhabar malikiyya??_
.
_Imamu malik watarana yatara dalubanshi yakaisu gaba qabarin manzon Allah, yace musu duk duniya babu wanda ba,a daukar maganarshi a ajje wacce bata daceba, face wanda yake cikin wannan qabarin, toh ashe kenan ba abin mamaki bane dan munce abar fahimtar imamu malik awajenda yayi kuskure shinema yace muyu hakan, kunga kenan munsawa hatta shi kanshi imamu malik idan muka bishi awajenda yayi kuskure***_
.
_mu awajenmu duk wanda ya rusa imamu malik toh yarushe 50% kashi hamsin cikin dari na hadisanda muke kafa hujjah dasu***_
.
_Kuma naji kuna korafi dan munce Sahihul bukhari shine mafi ingancin littafin hadisi, toh da kunnena naji wani malami dasunan da,awar sunnah wai yana kokarin kare imamu malik naji yanata cin mutuncin imamu shafi,i da imamul bukhari, harma yana cewa wai duk hadisanda suke cikin bukhari wai bolace na hadisanda imamu malik ya watsar wayanda basu ingantaba wai sune imamul bukhari yakwaso yazuba acikin littafinshi***_
.
_Toh wannan maganar karyace zunzurutu kuma son zuciyace kokuma jahilci, amma abinda shi wancan malamin besaniba shine: Na,am bama shakka cewa Imamu malik nesa ba kusaba yafi bukhari daraja, kuma yafi bukhari kota waccce fuska, toh amma abinda yafaru shine: bukhari besamu ganin imamu malik ba, toh amma kusan zan iya cewa kakaf daluban malik wayanda sukayi ruwayar muwadda awajenshi, dukansu saida bukhari yabisu daya bayan daya yakoyi hadisai awajensu kuma muwaddar suka koya mishi, wannan yasa zakaga hadisi abukahri kuma kaganshi acikin muwadda, wanda hakanma yana nuna karyar shi wancan malamin, tunda yace duk hadisanda suke cikin bukhari wayanda malik ya watsar ne, toh wannan karyane tunda ga hadisainan rututu a bukhari kuma sunanan jibge acikin muwadda***_
.
_kai kusanma ince maka babu wani hadisinda yake bukhari face yananan acikin muwadda, sedai kila kai muwaddarda take ahannunka yazama babu hadisib aciki, saboda mutane dayawa sun ruwaito muwadda awajen imamu malik, amma kuma inka hada muwaddodin zakaga ba hadisai iri daya bane acikinsu, zakaga wannan malamin yaruwaito hadisin wancan kuma bai ruwaitoba, toh bukhari duk wayanda sukai ruwayar muwadda awajen malik seda yabisu yakoyi muwadda awajensu***_
.
_misali Muhammad Ibn Hassan Ahs shaibani, wanda shinema yaba bukhari shawarar yadage yakoyi ilimin hadisi, saboda afarko bukhari ya shagaltune da koyon ilimin fiqhu***_
.
_kunga kenan saimuce bukhari Almajirin almajiran malik ne, kuma koda ake cewa sahihul bukhari yafi muwadda inganci, saboda bukhari tunfarko saida yayima kanshi sharadi cewa bazai kawo hadisinda bai ingantaba acikin wannan littafin nashi, sannan kuma cewa akayi bukhari yafi muwadda inganci, ai wannan ba suka bane ga imamu malik, darajacema muka kara mishi, tunda hadisanshine sukafibyawa acikin bukharin***_
.
_Ayi hakuri jama,a munsaki asalin karatun munkoma wata magana, toh itama wannan maganar tanada fa,idarta awannan lekcar saboda wata kurace muke dan takewa saboda korewa mutanenmu shubuharda ake dankara musu***_
.
_kuma ana cewa wai manhajin salaf damukace munabi, wai mazhabace ta Nasirudden Albani, toh wannan kuma karyace, tun kafin asan za,a haifi kakan kakan Albani malamai suke kira abi manhajin salaf, Kukaranta Imamus sabuni, wanda yau yafi shekara dubu da mutuwa musammab ya wallafa littafi yasamai suna *AQEEDATUS SALAF, ASHABUL HADIS****_
 .
_akoma a karanta muqaddimar Risala, ta Ibn Abu zaid Alqirawani cewa yake Abi manhajin salaf, sannan kuma can karshen risala wasiyyarda yakara yi kenan cewa arike manhajin salaf, wanda duniya tayi shaida akan cewa mai risala dan malikiyyane, harma cemai ake *IMAMU MAKIK KARAMI* toh tayaya wani dan son zuciya ayau zerika zagin malamai yana cewa sune suka kawo cewa abi manhajin salaf***_
.
_Kukaranta dan podio acikin littafanshi irin Nasihatu Ahliz zaman dasu Ihya'us sunnah dasauransu shima cewa yake lallai abi manhajin salaf***_
.
_idan akace salaf ana nufin malamai wayanda suka rayu a shekaru 300 na farkon musulonci, wayannan sune salaf, wanda imamu malik yana cikinsu, toh sunefa ake cewa ayi watsida duk wata fahimta ta wani malami azo arike tasu, duk wanda yazo a bayan shekaru 300 na farkon musulinci ba,a kiranshi salaf sedai idan yayi koyi dasu sai akirashi salafy, kuma Allah shine yafara kira da abi manhajin salaf***_
 .
_karanta suratul baqara ayata 137 Allah yace: *IDAN KUKAYI IMANI DA IRIN ABINDA WAYANCAN MAGABATAN SUKAYI TOH KUN SHIRYU, INKUWA KUKA JUYA MUSU BAYA TOH KUNFADA CIKIN HALLAKA* wannan ayar qur,anice jama,a kuje kuduba fassararta***_
.
_barema Imamu malik har yamutu besanda wata mazhaba malikiyyaba, kuma betaba cewa abi malikiyyaba, kai cewa yayi: *BABU ABINDA ZAI GYARA WANNAN AL,UMAR FACE ABINDA YA GYARA WAYANDA SUKA GABACETA* toh da wacce hujjah zakuce mubar abinda yake shine daidai muzo dole dole mubi mazhabar malikiyya???**_
 .
_kukaranta Ibn Abdulbarri akan fatwar imamu malik dayace adadin gejin kwanakin jinin haihuwa kwanaki 60 ne, Ibn Abdulbarri yace wannan fatwar imamu malik ce, amma mu mazhabar malikiyya fatwarmu shine jinin haihuwa baya wuce kwanaki 40, kunji shima ya ajje fatwar imamu malik yadauki hadisin Annabi toh danme kukuma zakuce mu mu ajje hadisi mudauki fatwar imamu malik???***_
.
_Kuyi hakuri kubiyoni cikin bayani nagaba semu koma kan asalin karatunda mukeyi***_
.
.
_Almajirinku kamar kullun_
.
```Jameel Alhassan Haruna Kabo```
_(Abu khausar)_
 .
.
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
https:/t/m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka  Wanatubu ilaika
Share:
*HUKUNCIN SALLAR QASRU-4!!!???*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Taken Lekca........
.
*SALLAR QASRU!!!!??*
.
Wannan shine bayani na hudu****
.
Cigaba***
.
_Ibn Nasir Assa,ady acikin tafsirinshi yace: Idan aka duba wancan sabanin nafarko damukayi magana na cewa shin qasru dole ne ko ba dole bane? Sa'ady yace: Abinda yafi dacewa shine duk wanda yayi yafiya kawai yayi kasaru, wannan yafi dacewa da sunnah, saboda kakaf malamai da masu cewa dole ne, da wayanda suke cewa ba dole bane toh kansu ya hadu bakidayansu akan cewa Annabi muhammad (s.a.w) har yamutu qasru yakeyi duk sanda yayi tafiya toh tunda dukkansu sunyarda cewa idan Annabi yayi tafiya  qasru yakeyi, toh wannan yana nuna mana cewa lallai ayi qasrun shine abinda yafi***_
.
_sannan yasake komawa kan wancan hadisin na Ya,ala wanda Annabi (s.a.w) yace: ita qasru sadakace ta Allah gareku, dan haka ku karbi sadakar Allah***_
..
_cewa mukarbi sadakar Allah wannan yana nuna lallai mafi kyawun abinda yadace ga matafiyi shine yayi qasru****_
 .
_malamai suna bada misalin wannan hadisin, sukace kamar misali ace sarkin garinkune ya aika akiraka, dakazo fadarshi seyace dama wata kyautace yakeso yayi maka, seya dauko wani abu yabaka kyauta, shin idan kace bazaka karba ba, kana ganin kuwa shi sarkin garin naku zaiji dadi??? Na tabbata bazeji dadiba, toh ina kuma ga ace Allah yaimaka kyauta amma kaki karba dan uwa?? Saboda haka mafi dacewa shine duk sanda mutum yayi tafiya toh yayi qasru***_
 .
_sallolinda akeyi musu qasru, guda uku ne, sune: Azahar, La,asar da Isha'i, wato duk sallah me raka,a hudu itace ake maida ita raka,a biyu, amma sallolin magriba da Asubahi su ba,ayin musu qasru, cikasu akeyi asubahi ko ahalin tafiya ko zaman gida raka,a biyu akeyi, hakanan itama magriba raka,a uku akeyinta ko ahalin tafiya ko zaman gida***_
.
.
_Sekuma cewa da wasu malamai sukayi wai sekayi tafiyar mita kaza ko kilo mita kaza sannan zakayi qasru, toh itama wannan maganar me raunice, ko ace seka wuce gonaki, kokuma ka wuce gidajen garinku duk wayannan kawai maganganune na malamai, sedai muroki Allah ya yafe musu***_
.
_Amma waccan ayar ta suratun Nisa'i ayat 101, Allah kawai cewa yayi babu laifi akanku idan kunyi tafiya kuyi qasru, kunjifa Allah cewa yayi idan kunyi tafiya abayan qasa toh kuyi qasru, kunjidai Allah baice mita kaza ko kilo mita kaza ba, kuma Allah baifadi gonakiba kokuma inka wuce gidaje***_
.
_Ashe kenan tunda Allah mai shari,a yace idan kunyi tafiya kuyi qasru, toh waye kuma ya isa ya iyakance yace se tafiya takai nisa kaza ko kawuce gonaki kaza kafin kayi qasru?? Dan Allah inaso kugayamin wanene ya isa ya iyakance abinda Allah da manzonshi basu iyakanceba????***_
.
_Kafin mucigaba bari mudan ratse mukawo wata magana ta Albani, acikin muqaddimar *BID'UL JANA'IZ*, yace daga cikin hanyoyinda ake samun bidi,a tana shigowa cikin al,umma akwai: Idan Allah da manzonshi sukabar kofar wata ibada asake basuyi mata iyakaba, se wasu mutane suzo suyi mata iyaka da wani kaidi, kamar sukebance wani waje, ko wani lokaci kowata siffah***_
.
_Toh gashi Allah yace idan munyi tafiya abayan kasa toh babu laifi muyi qasru,  toh sekuma wani yazo yace amma karmu wuce sati biyu munayin qasrun, wani kuma yace karmu wuce kwanaki uku, wani kuma yace karmu wuce salloli kaza, wani kuma yace bazamu fara yin qasrunba harse munwuce gidaje ko gonaki, ko kilomita, toh kunga ashe wayannan maganganun dukansu fahimtane tasu su malaman dan haka semubar musu kayansu mudawo mubi Abinda Allah yace mana kawai mutsaya anan, sukuma ba zaginsu zamuyiba, Aa zamu roka musu Allah ne akan yayafe musu***_
.
_Toh Alhamdulillahi gama wani hadisinan na shurahbil bin samdin, wanda shine zeraba gardama, shurahbil yace: lokacin Sayyadina Umar yana khalifa, sai yataso daga cikin madina zuwa Zulhulaifah, sekawai yazo zeyi sallah sai akaga yayi qasru***_
..
_Duk wanda yasan garin madina ai yasan ko inane zulhulaifah, toh nan wajenfa umar yazo, wanda itama zulhulaifa cikin madina take itacema mikatinsu na hajji, toh anan wajenfa umar yazo sekuma akaga yayi sallah qasru, sai shurahbil ya tambayeshi, ya sarkin musulmi yanaga haka kuma kayi qasru anan wajen?? Sai kawai Umar yace Nayinefa kamar yanda naga Annabi yayi****_
.
_Kunji umar yace haka yaga Annabi yayi, toh a inakuma aka samo cewa se ankai kilomita kaza kafin ayi qasru?? Toh gashi umar unguwace yaje acikin madina kuma  yayi qasru sannan yace haka Annabi yayi***_
.
_toh dan Allah ku dauki wannan hadisin ku hadashi da waccan ayar kugani shin akwai bambanci?? Allah yace idan kunyi tafiya, baice sekunkai nisan kaza  ba, toh gakuma umar kunga dai 'yar tafiyar dayayi, kuma kunji abinda yace toh ashe kenan batun kuma ace saika wuce gonaki ko gidaje, ko kilomita, toh wannan maganar ashema sam batama tasoba, kawai rikicin malaman fiqhu ne, kuma suma sunyi sabani tsakaninsu, duk wanda ka dauka aciki toh kaga kayi watsi da maganar wasu,  toh mafi dacewa shine mu ajje musu sabaninsu mudauki Qur,ani da hadisin Annabi muhammad (s.a.w)***_
.
_wannan kuma itace fatwar ibn taimiya acikin majma,u fatawa, hakanan dawudu azzahiri, da Ibn qudama Alhambali acikin Almugni, da Ibn qayyum acikin zadul ma,ad***_
.
_Ibn qudama yace idan da zaka tattaro fahimtocin dukkan malaman ka hadasu waje daya toh zakaga hujjarda tafi karfi itace wayanda sukace inkayi tafiya kawai kayi qasru, batareda iyakance nisan tafiyarba kuma basu qayyade yawan kwanaki ba****_
.
.
_zan dakata anan sekuyi hakuri musake haduwa acikin bayani nagaba in Allah yaso***_
.
.
.
_Almajirinku kamar kullun_
.
```Jameel Alhassan Haruna Kabo```
_(Abu khausar)_
 .
.
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
https:/t/m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka  Wanatubu ilaika
Share:

нυĸυncιn qaѕrυ 3

*HUKUNCIN SALLAR QASRU-3!!!???*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Taken Lekca........
.
*SALLAR QASRU!!!!??*
.
Wannan shine bayani na uku****
.
Cigaba***
.
.
_Hadisi ya tabbata ruwayar bukhari da muslim daga sahab Abdullahi dan umar, yace na aboci manzon Allah (s.a.w) kuma shi yakasance baya kara sallarshi samada raka,a bibbiyu ahalin tafiya, hakama Abubakar da Umar da Usmanu, suka kasance**_
.
_Toh amma yatabbata Sayyadina Usmanu lokacinda yake khalifa yazo aikin hajji kuma seya rika cika sallah, kuma sahabbai suka bishi basu yimai inkariba, toh wannan abinda sukayi shima yana nuna cewa sallar qasru ba dole bane***_
.
_kenan Usman afarkon khalifancinsa baya cika sallah, qasru yakeyi, amma daga baya seyabar yin qasrun yakoma yana cikawa***_
.
_Toh malamai sunyi sabani gameda gwargwadon tafiyada ake iya yimata qasru shin adadin wanne irin nisane akeyin qasru***_
.
_Dawuduz Zahiri  yanada fahimtar cewa kowacce irin tafiya anayi mata qasru karamar tafiyace ko babba, koda kuwa tafiyar ta mil uku ce, yana kafa hujjah da wani hadisi ruwayar musulim daga Yahya bin yazid Alhuna'i wanda yace: na tambayi Anas dan malik gameda qasrun sallah, sai yace: Manzon Allah (s.a.w) yakasance idan yafita tafiya ta kimanin mil uku ko farsakhi uku yakanyi qasrun sallah***_
..
_wasu malamai sukace wannan hadisin baya zama hujjah dankuwa ansamu shakka acikinshi, inda yace mil uku ko farsakhi uku***_
.
_wasu kuma malamai sukace Aa idan tafiyarda zakayi doguwar tafiyace toh bazaka fara yin qasruba harse kaci mil uku kokuma farsakhi uku acikin tafiyar sannan zaka fara yin qasru***_
.
_Wasu kuma sukace dazarar kawuce gidan karshe na garinku toh shikenan sai kawai kafara yin qasru****_
.
_Wasu kuma sukace sai ka gama wuce gonakin garinku sannan zaka fara yin qasru****_
.
_wasu kuma sukace Ai ita qasru saukice Allah yayiwa matafiyi, toh dan haka duk wata tafiya metsawo toh ya halasta kayi qasru, ammasu basu iya kance nisan tafiyarba kawai sudai sunce tafiya menisa***_
.
_wasu kuma sukace Allah dai yace idan kunyi tafiya abayan qasa babu laifi kuyi qasru, sesukace kenan tsananinda ake samu ahalin tafiya shine yajawo saukinda yasa akace muyi qasru, saboda haka sukace bazaka fara qasruba harse kafara tafiya, wato raddine sukeyima wasu malamai wayanda suka fassara kalmar *DARABTUM* wanda yazo acikin ayar, sesukace ma,anarsa ai *AZAMTA* watoh dazarar kayi nufin tafiya koda kuwa bakama fara tafiyarba inhar kayi niyyar zakai tafiyar, toh kawai sukace kafara yin qasru*** toh wannan maganar itace wayancan malaman sukema raddi, shine sukuma dasuka tashi fassara waccan kalmar ta *DARABTUM* sesukace ma,anarta ai *SAFARTUM* idan kunyi tafiya, toh ai kai yanzu kana gida bakayi tafiyaba, kuma sukace tafiyarma sekayi menisa sannan zaka fara qasru amma bawai yar karamar tafiyaba, sukace wannan unguwa kaje ba tafiya kayiba***_
.
_Wasu malamai kuma sukace Qur,ani da Hadisi basuce ga tsawon tafiyarda zakayiba kafin kayi qasru kokuma kafara yin qasru, amma sesukayi tawaqqufi basuce komaiba****_
..
_Toh mu ajje wannan batun zuwa gaba kadan zan kawo muku mafi ingancin zance gameda hakan***_
.
_Toh sekuma irin tafiyarda take halasta ayi mata qasru, shin kowacce irin tafiyace akeyin qasru kokuwa an kebance wasu nau,oin tafiya wayanda ba,a yinmusu qasru??? Toh nanma malamai sunyi sabani, wato jama,a zeyi wuya a fiqhun musulinci kasamu wani abu wanda akai sabani sosai akanshi, fiyeda sallar qasru, ita kusan babu wata gaba da zaka dauka acikinta baka samu anyi sabani ba****_
.
_Imamul qurdubi ya hikaito Ijma,in malamai akan ya halasta ayi qasru a tafiyar aikin hajji da umura, da tafiya ta sada zumunci da gudun hijira, toh wayannan sune tafiye tafiyenda kan malamai yahadu akan cewa lallai anayi musu qasru, amma duk tafiyarda basuba toh anyi sabani***_
.
_Jumhurin malamai sukace ya halasta ayi qasru adukkan wata tafiya ta halas, kamar kasuwanci ko makamancin haka***_
.
_sannan jumhurin malaman suka kara cewa bai halastaba mutum yayi qasru a tafiya ta sabon Allah, kamar karuwa ko dan fashi, da sauransu, duk wayannan bai halasta garesu suyi qasruba inji jamhurin malamai***_
.
_Itama wannan maganar mu ajjeta se gaba kadan zanmuku gamsashshen bayani akanta, akan shin akwai tafiyarda ba,a yimata qasru kamar yanda wayannan tattaruwan malaman sukace???***_
.
_Sekuma adadin kwanakinda mutum zeyi yana yin qasru, shima wannan ansamu sabani akanshi, kamarfa yanda nagaya muku ita qasrun sallah kusan babu wata gaba acikinta wacce ba,ayi sabani ba***_
.
_Imamu Malik da Shafi'i, da Laisu bin sa,ad da Dabari, da wasu malamai sunada fahimtar cewa qasru ba,a wuce kwanaki uku: dazarar ka wuce kwanaki uku sukace zaka cika sallah su a fahimtarsu shine qasru kwanaki uku akeyi, wato idan kayi tafiya, dazarar ka kwana uku kana qasru agarinda kaje toh zaka cigaba da cika sallah***_
.
_Sa'idu bin Musayyib, da Abu Hanifa da Imamus Sauri sukuma sunada fahimtar cewa qasru anayin kwanaki 14 ne, idan kayi tafiya kanada damar kaita yin qasru tsawon sati biyu, amma dazarar ka haura sati biyu toh zaka cika sallah, sukuma wannan itace fahimtarsu***_
.
_Ansamu wata ruwayar kuma daga sa,idu dan musayyib wanda shine fahimtar Ahmad bin Hambal, da wayansu malamai sukuma sukace anayin qasru ne adadin salloli 21 na farilla, kawai sukace dazarar kayi tafiya toh kanada damar qasrune a salloli 21, amma dazarar kawuce haka sukace toh zaka cika sallah****_
.
_Wayansu malamai kuma sukace ai duk matafiyi yanada damar yaita yin qasru har abada, kawai indai sunanka matafiyi toh kaita yin qasru harse kadawo, koda shekaru nawa zakayi, sun kafa hujjah da hadisin Anas dan malik daya kwashe kanaki sittin agarin Naisabur kuma qasru yaitayi, akwaima asarai dayawa wayanda sahabbai sukayi tafiya kuma sukaita yin qasru har suka dawo***aduba tafsrin qurdubi mujallad na biyar shafina 259, wayannan maganaganun duk za,a gansu***_
.
_toh itama wannan matsalar mu ajjeta seku biyoni cikin bayani nagaba semuji gamsassun bayanan dakuma wayanda sukafi karfin hujjah in Allah yaso****_
.
_Yanzu dai mun kawo muku kanun bayanan malamai kenan gameda irin tafiyarda ake mata qasru, da adadin kwanaki, dakuma nisan tafiyar, sannan kuma yaushe ake fara qasrun, toh wayannan zamu gaya muku abinda yafi inganci akan kowannensu, amma se cikin bayani nagaba in Allah yaso***_
.
.
.
_Almajirinku kamar kullun_
.
```Jameel Alhassan Haruna Kabo```
_(Abu khausar)_
 .
.
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
https:/t/m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka  Wanatubu ilaika
Share:

Thursday, 6 July 2017

Hukuncin sallar qasru 2

*HUKUNCIN SALLAR QASRU-2!!!???*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Taken Lekca........
.
*SALLAR QASRU!!!!??*
.
Wannan shine bayani na biyu****
.
Cigaba***
.
_Imamul Qurduby yace: Toh wancan hadisinda mukaji na ya,ala shima wasu daga cikin daluban Shafi,i sun kafa hujjah dashi cewa  yana kara tabbatar mana da halascin ayi sallar qasru koda ba,a halin tsoroba, kenan yazama sabanin waccan fahimtar tasu Malam Abubakar Gummi dasauran magabata wayanda sukace ba,ayin qasru sai ana halin tsoro, toh ga hadisi karara manzon Allah yace ita qasru sadakace garemu, dan haka yace mukarbi sadakar Allah***_
.
_sannan qurdubi yakara da cewa: ai ita sallar tsoro ba,a lurada wayancan sharuddan acikinta, (sharuddan sune farkon Ayar Allah yace: Babu laifi agareku idan kunyi tafiya, toh cewa idan kunyi tafiya wannan sharadine, saikuma inda yace: inkunajin tsoron kafirai zasu fituneku, toh shima wannan sharadine, kenan ba,ayin qasrun sallah se anceka wayannan sharadda idan muka duba zahirin ayar kenan) toh shine qurdubi yake cewa aima ita sallar tsoro sam ba,a duba wayannan sharuddan idan za,ayita, saboda ai koda bamuyi tafiya abayan kasa ba, se kawai kafirai suka biyomu garinmu misali zasu yakemu acikin garinmu ai yahalasta muyi sallar tsoro, bazamu tsaya kokarin cika sharuddanba***_
.
_Wannan magana ta qurdubi itama tana kara nuna mana cewa eh lallai ya halasta muyi qasrun sallah ahalin tafiya koda tafiyar bata yaki bane kuma ba,a halin tsoroba***_
.
_misali kaine zakaje kauyenku ziyara, kokuma zakaje kasuwanci ko aikin hajji misali duk kaga wannan tafiyar aidai babu tsoro, toh amma yahalasta kayi qasrun sallah, shine mafi ingancin magana kuma shine yadace da wancan hadisin na ya,ala***_
..
.
_Malamai sun sake tafka wani sabani akan shin waima sallar qasru dolene kokuwa ba dole bace???_
.
_nasan baku ganeba, toh ina nufin idan kayi tafiya kai amatsayinka na matafiyi, shin wajibine akanka dole sai kayi qasrun sallah kokuwa ba dole bane?? Toh shine nace malamai sunyi sabani gameda hakan***_
.
_Ansamu ruwayoyi daga manyan malamai dayawa wayanda suke ganin cewa yin qasrun sallah ga matafiyi dole ne, wannan shine Zancen Umar Ibn Abdul,azeez, da mafi yawan malaman kufah, wato iraqi kenan ayau, kuma wannan shine fahimtar Isma'il Alqadi, da  Hammadu bin sulaiman, kuma sun kafa hujjah da hadisin Aisha (Ra) tace: Afarkon musulinci Anfarlanta sallah raka bibbiyu ahalin zaman gida dakuma halin tafiya, amma daga baya, bayan isra,i da mi,iraji kenan, sai aka kara tsawon sallar gida takoma raka,a hudu, amma aka tabbatarda sallar matafiyi a raka,a bibbiyun,...****_
.
_Toh amma wasu malamai sukace babu wata hujjah acikin wannan hadisin saboda ita kanta Aisha ta kasance tana cika sallah ahalin tafiya***_
.
_Imamul Qurdubi acikin tafsirinsa yakawo wata fatwar imamu malik inda shima yake bayan wayanda suke ganin lallai dolene matafiyi yayi sallar qasru, inda imamu malik yace: duk wanda yacika sallah ahalin tafiya toh zesake wannan sallar matukar lokacinta bai fitaba***_
.
_Imamu shafi,i kuwa cewa yayi, nidai banaso inga mutum yana cika sallah ahalin tafiya saboda kwadayin dacewa da sunnah***_
.
_Sekuma musake komawa kan wancan hadisin na Ya,ala bin umayya wanda Annabi (s.a.w) yace: Ita qasru sadakace wacce Allah yayima bayi......***Toh wasu malamai sun kafa hujjah da wannan hadisin wajen cewa lallai yin qasrun sallah ahalin tafiya ba dole bane, saboda Annabi (s.a.w) cewa yayi sadaka ce, sukace ai ita sadaka yinta da karbanta ba dole bane, idan da manzon Allah yana nufin dolene da baze kirata sadaka ba sedai yace mata zakka***_
..
_Toh sekuma wayancan malaman wayanda suke ganin lallai yin qasru dolene, suma se suka sake daukar shi wannan hadisi, suka aunashi da wata qa,ida ta usul, inda malaman usul suke cewa: *AL AMRUL YAQTADIL WUJUB* wato umarni yana hukunta wajabci: sesukace toh ai acan karshen hadisin Annabi (s.a.w) yace; kukarbi sadakar ubangijinku, toh cewarda Annabi yayi kukarba, sukace ai wannan shima umarnine dan haka lallai yahukunta cewa dolene matafiyi yayi sallar qasru ba wai zabi bane ake bashi***_
.
_Toh amma atakaice dai, kada mutsawaita harshe akan wannan kadiyyar ita kadai toh bari mu takaita, lallai mafi ingancin magana shine yin qasrun sallah ga matafiyi ba dole bane, saboda Allah cewa yayi babu laifi akanku kuyi qasrun sallah***_
.
_Atakaice dai yin qasrun ba dole bane, ammadai wanda yayi qasru yanada falala fiyeda wanda yacika sallah, saboda dacewarda yayi da sunnah***_
.
_kenan semuce yin qasrun shine yafi akan acika, ammadai ba dole bane***_
.
_Ma,anar dole kuma a sallar qasru shine: bayan kayi tafiya kafara qasru na wani dan lokaci, toh bakada ikon cewa ka fasa yin ita qasrun, awajen malamanda suke ganinta amatsayin dole****_
.
.
_zan dakata anan sefitowa tagaba zamuji wasu muhimman bayanan_
.
.
.
_Almajirinku kamar kullun_
.
```Jameel Alhassan Haruna Kabo```
_(Abu khausar)_
 .
.
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
https:/t/m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka  Wanatubu ilaika
Share:

Hukuncin sallar qasru

*HUKUNCIN SALLAR QASRU!!!???*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Taken Lekca........
.
*SALLAR QASRU!!!!??*
.
.
_Muna farawa da godema Allah, muna neman taimakonshi da agajinshi, wanda Allah ya shiryar shine cikakken shiryayye, wanda yabata kuma babu me shiryar dashi***_
.
_Dubban salati marasa adadi zuwaga shugabanmu uban dakinmu Annabi muhammad (s.a.w), Shugaban Halittu, mijin zainab kuma baban zainab (S.A.W)***_
.
_Bayan haka, hakika yau itace ranar juma,a 4-02-1438 wacce tayi dai dai da 4-11-2016, itace ranarda zan iya cewa kwari ya karye, tunda yau dai gashi Allah cikin ikonsa yabani ikon fara rubuta wannan bayanin, wanda yau kusan watannin hudu kenan inata cewa zanyi bayanin, toh yau ga ranar Allah yayi zamu gabatarda takaitaccen bayani na musamman gameda sallar qasru****_
.
_Abinda ake cema *QASRU* shine takaitawa, atakace wani abu daga yanda yake cikakkenshi sai a takaitashi***_
.
_Ibnul munzur yace: Malamai sunyi Ijma'i akan cewa Qasru ababin sallah shine arage yawan raka'oin sallah me raka,a hudu amaida ita raka,a biyu wannan shine abinda ake cema qasru, kuma malamai sunyi ijma,i akanta****_
.
_Itadai Qasru Allah ya ambacetane acikin Surata hudu ayata 101, inda Allah ta,ala yace: *KUMA IDAN KUNYI TAFIYA ACIKIN QASA, TOH BABU LAIFI AKANKU KURAGE DAGA SALLAH IDAN KUNJI TSORON WADANDA SUKA KAFIRTA SU FITINEKU, LALLAINE KAFIRAI SUN KASANCE, AGAREKU MAKIYI BAYYANANNE****_
..
_dogaro da wannan ayar itace take nuna mana cewa lallai qasrun sallah shari,ar musulincine****Abinda kuma ake cema qasru shine rage tsawon sallah me raka,a hudu, amaidata raka,a biyu a halin tafiya, kokuma alokacin tsoro ko yaqi, wanda qasru alokacin yaki harma raka,a daya anayi toh wannan shine qasru, kuma wannan ayar itace kadai acikin qur,ani wacce tayi magana akan sallar qasru kaitsaye***_
.
_Toh ita wannan ayar malaman tafsiri sunyi sabani akanta, shin tana maganane akan kasrun sallah ta tafiya zuwa unguwa? Kokuwa tana nufin qasrunda akeyine afagen yaki wato sallar tsoro??_
..
_toh malamai dai sunyi sabani, wanda shikanshi Malam Abubakar gumi dayazo tarjamar wannan ayar acikin tarjamarsa ta hausa shima yace wannan ayar tana maganane akan qasrun sallah alokacin yaki wato sallar tsoro, malamanda suke kan wannan fahimtar tacewa sallar tsoro ake nufi, sunyi la,akarine da sharadin da yazo acikin ayar inda Allah yace *IDAN KUNJI TSORON WADANDA SUKA KAFIRTA SU FITINEKU****_
.
_Ibn jarir Addabary acikin tafsirinsa mujallad na 5 shafina 287 yakawo wata ruwaya daga Aisha (Ra) wai ita takasance tana cewa ahalin tafiya: Kucika sallarku: sai akace mata Aikuma manzon Allah (s.a.w) yakasance yanayin qasru ahalin tafiya, sai tace: Aishi yanayin hakane alokacin yaki, kuma yana halin tsoro, shin kuma tsoron kukeji??? Toh wannan ruwayar bata ingantaba daga Aisha***_ 
.
_akwai dai ruwayoyi dadama wayanda sukazo gameda hukuncin sallar qasru, inda wayansu suke ganin cewa lallai dai sallar qasrunda wannan ayar take nufi anayintane alokacin tsoro, wato ansamu wayansu malamai wayanda suke kore yin sallar qasru ahalin tafiyarda bata yakiba***_
.
_Imamu Dabari yakawo wata ruwaya daga Aliyu dan Abu dalib, wayansu mutane 'yan kasuwa sunzo wajen Annabi (s.a.w) suka tambayeshi, ya Manzon Allah: mun kasance munayin tafiye tafiye abayan kasa toh shin yaya sallarmu zata kasance?? Sai aka saukarda farkon wannan ayar inda Allah yace: *IDAN KUNYI TAFIYA ACIKIN QASA, TOH BABU LAIFI AKANKU KURAGE DAGA SALLAH* iyaka nan wajen aka saukar, ba,a cigaba ba***_
.
_bayan haka da shekara daya sai manzon Allah yayi yaki kuma ya sallaci azahar awannan yakin, sai mushirikai suka fara fadar wayansu maganganu gameda Annabi da sahabbai sunaso sukulla musu makirci idan la,asar tayi: toh shine sai Aka saukarda cikon ayar wato inda yace: *IDAN KUNJI TSORON WADANDA SUKA KAFIRTA SU FITINEKU* toh wannan ruwayar itama bata ingantaba tanada rauni***aduba tafsirin Dabary mujallad na 5 shafina 286****_
.
_Toh amma bari muji raba gardama kai tsaye daga Annabi (s.a.w) shin Qasrun sallah anayintane ahalin tsoro kawai kokuwa ana iya yinta koda ba,a halin tsoroba??_
 .
_Imamul Qurdubi acikin Tafsirinshi ALJAMI,U LI AHKAMUL QUR'AN mujallad na 5 shafina 261 yakawo hadisin Ya'ala bin umayyah***_
.
_Ya'ala bin umayyah yace: nacema sayyadina umar, shin mene yasa mukeyin qasru alhalin bama cikin halin tsoro? Kuma gashi acikin qur,ani Allah yaimana sharadine cewa babu laifi mu takaice sallah idan muna halin tsoro, toh mukuma meyasa muke takaice sallar bayan kuma gashi muna cikin aminci? Sai umar yace: Kayi mamakin abinda nima nataba yin mamaki akansa, sai na tambayi manzon Allah (s.a.w) gameda hakan? Sai yace: Ai ita qasru sadakace wacce Allah yayimuku ita dan haka kukarbi sadakarda Allah yaimuku***Imamu muslim yaruwaito wannan hadisin (686)_
.
_kenan duba da wannan hadisin zamu fahimta cewa lallai anayin qasru ahalin tafiya koda kuwa babu tsoro acikin tafiyar***_
.
_Toh masu karatu inaso ku ajjemin wannan hadisin da ita waccan ayar seku biyoni cikin bayani nagaba insha Allah zamu cigaba sesu zamar mana sune ginshikai wayanda zamu gina bayananmu akansu insha Allahu***_
.
.
_Almajirinku kamar kullun_
.
```Jameel Alhassan Haruna Kabo```
_(Abu khausar)_
 .
.
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
https:/t/m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka  Wanatubu ilaika
Share:

Menene hukuncin mutumin da akabashi ajiyar kudi sai yake kasuwanci da kudin yana samun ribah ??

     
*_Tambaya ta (324)_*
:
_Menene hukuncin Mutumin da akabashi *ajiyar kuɗi* sai yake kasuwanci da *kuɗin yana samun ribah??*_
:
*_Amsa:_*
:
_Asalidai a *Shari'ance* idan akabawa Mutum ajiyar wasu *Kuɗaɗe* kokuma kadarori to wajibine akansa yakiyaye wannan amanar da'akabashi, Sannan kuma bazaiyi amfani da'itaba dole sai in yanemi izinin mai ita, to amma idan har Mutum yayi amfani da *Kuɗin ajiya* yana Kasuwanci dasu yana samun riba, anan sai *Malamai sukayi Saɓani dangane da hukuncin wannan ribar da'aka samu,* Mazhabin *Malikiyya da Shafi'iyya* sunaganin cewa wannan riba da'akasamu ta shi Mutumin da yajuwa *Kuɗin ne* wato wanda akabawa ajiyar Kuɗin kenan, sukace wanda yabada ajiya za'amayar masa da asalin Kuɗinsane da yabayar a ajjemasa, amma wanda akabawa ajiyar Kuɗin shine zaidauki abinda yakaru aciki, domin shine yayi wahala wajen yin kasuwanci da'ita, duk dacewa *yayi amfani da Kuɗaɗenne* ta hanyar ta'addanci batare da izinin maisuba,_
:
_*Hujjarsu anan itace,* tunda haryayi ta'addanci nayin amfani da *Kuɗaɗen ajiya* wanda kuma inda wadannan *Kuɗaɗen zasu salwanta to wajibine akansa sai yabiya,* danhaka kenan tunda ramuwa tana kansa idan akayi asara to hakanan kuma idan akasamu riba shine zairiketa, kamar yadda *Ƙa'idarnan ta Fiƙ-hiyya* datake cewa:_
               *(الخراج بالضمان)*
_Saidai *Mazhabin Hanabila* suntafine akancewa wannan riba da'akasamu ta mai asalin wanda yakawo ajiyar *Kuɗinsane domin da Kuɗaɗensa ne akasamu wannan riba danhaka tasace,* amma Mazhabin *Hanafiyya* suntafine akan cewa da wanda yabada ajiyar da wanda akabawa ajiyar dukkaninsu babu wanda zaidauki wannan riba ta Kuɗi da'akasamu, danhaka saidai ayi *Sadaƙa da Kuɗin kawai,* Saidai wasu daga cikin Malamai sukace a'a, *kawai za'araba wannan ribar Kuɗaɗen da akasamune gida biyune* sai suraba atsakaninsu, kowa yadauki rabi,_
:
_Danhaka kenan asali *Haramunne amma akwai Malaman dasukace Makaruhine* Mutum yayi amfani da dukiyar da'akabashi ajiya batareda izinin mai'itaba, to amma idan har ya aikata hakan batareda izinin mai'ita ɗinba meye hukuncinsa? Malamai sukace yayi ƙoƙari yanemi afuwa da yafiya daga wajen mai asalin dukiyar shikenan magana taƙare,_
:
*_o(шαʟʟαнυ- тα'αʟα α'αʟαмυ)o_*
:
*_ωαηαη sнιηε gωαяgωαdoη ɗαη αвιηdα ιʟιмιη мυ dαкυмα вιηcιкεηмυ үαкαι zυωα gαяεsнι, dαηнαкα ιdαη αηgα ωαηι кυsкυяε αcιкιη αвιηdα мυкα яυвυтα тo αηα'ιүα ғαɗαкαя dαмυ мυgүαяα, тαяεdα кαωo нυננα мαι ƙαяғι:_*
:
*_Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:_*
                 *_↓↓↓_*
:
*"مغني المحتاج" (3/363)*
:
*"المغني لإبن قدامة" (5/159)*
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
              *Daga Zaυren*
             *Fιƙ-нυl-Iвadaт*
                *(فِقْهُ الْعِبَادَاتِ)*
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
              *_→AMSAWA←_*
           *Mυѕтαρнα Uѕмαи*
              *08032531505*
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
_*Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾*_
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Share:

Wednesday, 5 July 2017

Duniya budurwar wawa

Sheikh Ibrahim Disina


DUNIYA BUDURWAR WAWA!!!
ﺃﻭﻝ ﻣﺎ ﻳﺴﻘﻂ ﻣﻨﻚ ﻋﻨﺪ ﻣﻮﺗﻚ ﻫﻮ ﺍﺳﻤﻚ ..
Farkon abinda da zai bace maka shine
...sunanka
ﻟﺬﻟﻚ ﻋﻨﺪﻣﺎ ﺗﻤﻮﺕ ﻳﻘﻮﻟﻮﻥ ﻋﻨﻚ ﺃﻳﻦ ﺍﻟﺠﺜﺔ .. ؟
Saboda haka ne idan ka mutu zasu ce
gameda kai: Ina gawar?
ﻭﻋﻨﺪﻣﺎ ﻳﺮﻳﺪﻭﻥ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻋﻠﻴﻚ ﻳﻘﻮﻟﻮﻥ ﺍﺣﻀﺮﻭﺍ
ﺍﻟﺠﻨﺎﺯﺓ .. ؟
A lokacinda za su yi ma sallah su ce, "A
kawo mamacin"
ﻭﻻ ﻳﻨﺎﺩﻭﻧﻚ ﺑﺈﺳﻤﻚ
Ba za su kiraka da sunanka ba
ﻭﻋﻨﺪﻣﺎ ﻳﺸﺮﻋﻮﻥ ﺑﺪﻓﻨﻚ ﻳﻘﻮﻟﻮﻥ ﻗﺮﺑﻮﺍ ﺍﻟﻤﻴﺖ ﻭﻻ
ﻳﻨﺎﺩﻭﻧﻚ ﺑﺎﺳﻤﻚ !..
Idan za su turbudeka zasu ce "Ku miko da
gawar". Ba za su kiraka da sunankaba
ﻓﻼ ﺗﻐﺮﻙ ﻗﺒﻴﻠﺘﻚ ﻭﻻ ﻳﻐﺮﻙ ﻣﻨﺼﺒﻚ ﻭﻻ ﻧﺴﺒﻚ ..
Kada ka bari kabilarka ko matsayinka ko asalinka ya rudeka ...
ﻓﻤﺎ ﺃﺗﻔﻪ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﻭﻣﺎ ﺃﻋﻈﻢ ﻣﺎ ﻧﺤﻦ ﻣﻘﺒﻠﻮﻥ
ﻋﻠﻴﻪ ..
Duniya itace mafi kankantar abu. Inda muka fuskanta ne mafi girman abu.
ﺳﻄﻮﺭ ﻣﻦ ﺫﻫﺐ ..
Ga Wasu Shedaru na Zinari..
ﺍﻟﺤﺰﻥ ﻋﻠﻴﻚ ﺳﻴﻜﻮﻥ ﺛﻼﺛﺔ ﺃﻧﻮﺍﻉ؟؟
Nau'i uku na bakin cikin ne za su kasannce
a gareka??
1- ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﻌﺮﻓﻮﻧﻚ
ﺳﻄﺤﻴﺎً ﺳﻴﻘﻮﻟﻮﻥ
ﻣﺴﻜﻴﻦ ‼
1- Mutaneda suka sanka sama-sama za su
ce: Miskini (Bawan Allah)‼
2- ﺃﺻﺪﻗﺎﺅﻙ ﺳﻴﺤﺰﻧﻮﻥ ﺳﺎﻋﺎﺕ ﺃﻭ ﺃﻳﺎﻣﺎً ﺛﻢ
ﻳﻌﻮﺩﻭﻥ ﺇﻟﻰ ﺳﻮﺍﻟﻔﻬﻢ ﻭﺿﺤﻜﻬﻢ ‼
2- Abokanka za su yi bakin ciki na Awowi ko
Kwanaki daga nan sai su koma ga
hidindimunsu da dare-darensu‼
3- ﺍﻟﺤﺰﻥ ﺍﻟﻌﻤﻴﻖ ﻓﻲ ﺍﻟﺒﻴﺖ ‼ ﺃﻫﻠﻚ ﺃﺳﺒﻮﻉ
ﺃﺳﺒﻮﻋﻴﻦ ﺷﻬﺮ ﺷﻬﺮﻳﻦ ﺃﻭ ﺣﺘﻰ ﺳﻨﺔ ؟؟
3- Tsananin bakin-ciki a cikin gida‼ zai kau
bayan Mako guda ko biyu ko kuma har
tsawon shekara??
ﻭﻣﻦ ﺛﻢ ﺳﻴﻀﻌﻮﻧﻚ ﻓﻲ ﺃﺭﺷﻴﻒ ﺍﻟﺬﻛﺮﻳﺎﺕ ‼
Daga nan kuma za su saka kwandon
‼mantuwa
ﻭﻫﻜﺬﺍﻭﻫﻜﺬﺍ
Haka ne
ﺍﻧﺘﻬﺖ ﻗﺼﺘﻚ ﺑﻴﻦ ﺍﻟﻨﺎﺱ
Labarinka ya kare a tsakanin mutane.
ﻭﺑﺪﺃﺕ ﻗﺼﺘﻚ ﻣﻊ ﺍﻟﺤﻘﻴﻘﻴﻪ؟؟؟؟؟
Kissarka zata soma a Matabbata??????
ﻭﻫﻲ ﺍﻵﺧﺮﺓ
It a ce Lahira
ﻟﻘﺪ ﺯﺍﻝ ﻋﻨﻚ؟؟؟
Lalle ka rasa???
-1 ﺍﻟﺠﻤﺎﻝ
2- ﻭﺍﻟﻤﺎﻝ
3- ﻭﺍﻟﺼﺤﺔ
4- ﻭﺍﻟﻮﻟﺪ
5- ﻟﻘﺪ ﻓﺎﺭﻗﺖ ﺍﻟﺪﻭﺭ ﻭﺍﻟﻘﺼﻮﺭ
6- ﻭﺍﻟﺰﻭﺟﺔ ؟؟؟
1. Kyawo
2.da Dukiya
3.da Lafiya
4. da 'Ya'ya
5. Lalle ka rabuda Gidaje da Benaye.
6 da Mata???
ﻭﺑﺪﺃﺕ ﺍﻟﺤﻴﺎﺓ ﺍﻟﺤﻘﻴﻘﻴﺔ
ka soma tabbatacciyar rayuwa
ﻭﺍﻟﺴﺆﺍﻝ ﻫﻨﺎ :
ﻭﺍﻟﺴﺆﺍﻝ
Tambaya a nan itace:
ﻣﺎﺫﺍ ﺃﻋﺪﺩﺕ ﻟﻘﺒﺮﻙ ﻭﺁﺧﺮﺗﻚ؟؟؟؟؟؟؟؟؟
mene ne ka tanada domin Kabarinka da
Lahirarka?????????
ﻫﺬﻩ ﺣﻘﻴﻘﺔ ﺗﺤﺘﺎﺝ ﺍﻟﻰ ﺗﺄﻣﻞ ؟؟؟؟؟؟؟؟؟؟
wannan gaskiya ce da ke bukatar
tunani????????
ﺍﺣﺮﺹ ﻋﻠﻰ ؟؟
To ka kiyaye da??
-1 ﺍﻟﻔﺮﺍﺋﺾ
2- ﺍﻟﻨﻮﺍﻓﻞ
3- ﺻﺪﻗﺔ ﺍﻟﺴﺮ
4- ﻋﻤﻞ ﺻﺎﻟﺢ
5- ﺻﻼﺓ ﺍﻟﻠﻴﻞ
ﻟﻌﻠﻚ ﺗﻨﺠﻮ
1. Farillai
2. Nafilo.
3. Sadaka a boye.
4. Sallar Dare
wata kilan ka tsira
ﻟﻮ ﺳﺎﻋﺪﺕ ﻋﻠﻰ ﺗﺬﻛﻴﺮ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺑﻬﺬﻩ ﺍﻟﻤﻘﺎﻟﺔ ﺇﻥ
ﺷﺎﺀ ﺍﻟﻠﻪ
da kuma zaka iya taimkawa wajen
fadakrada mutane akan wannan maganar .
Da yardar Allah:
ﺳﺘﺠﺪ ﺃﺛﺮ ﺗﺬﻛﻴﺮﻙ ﻓﻲ ﻣﻴﺰﺍﻧﻚ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ
Zaka samu tasirin tunatarwarka a
ma'auninka ranar Kiyama.
‏( ﻭﺫﻛّﺮ ﻓﺈﻥ ﺍﻟﺬﻛﺮﻯ ﺗﻨﻔﻊُ ﺍﻟﻤﺆﻣﻨﻴﻦ )
(ka tunatar lalle tunatarwa na amfanar
Muminai)
ﻟﻤﺎﺫﺍ ﻳﺨﺘﺎﺭ ﺍﻟﻤﻴﺖ
me Ya sa Mamaci ke Sabin
“ ﺍﻟﺼﺪﻗﺔ ”
ﻟﻮ ﺭﺟﻊ ﻟﻠﺪﻧﻴﺎ
Sadaka
Da zai dawo a Duniya.
ﻛﻤﺎ ﻗﺎﻝ ﺗﻌﺎﻟﻰ
kamar dai yadda Madaukakin Sarki ya ce:
ﺭﺏ ﻟﻮﻻ ﺃﺧﺮﺗﻨﻲ ﺇﻟﻰ ﺃﺟﻞ ﻗﺮﻳﺐ
‼ ﻓﺄﺻﺪﻕ ‼
Ya Ubangiji da dai ka dan yimini jinkiri
zuwa wani dan lokaci
‼domin in yi Sadaka‼
ﻭﻟﻢ ﻳﻘﻞ :
Kuma bai ce:
domin in yi Umrah
Ko Sallah
Ko Azumi ba.
ﻻﻋﺘﻤﺮ
ﺍﻭ ﻷﺻﻠﻲ
ﺃﻭ ﻷﺻﻮﻡ
ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻌﻠﻤﺎﺀ :
ﻣﺎ ﺫﻛﺮ ﺍﻟﻤﻴﺖ ﺍﻟﺼﺪﻗﺔ ﺇﻻ ﻟﻌﻈﻴﻢ ﻣﺎ ﺭﺃﻯ ﻣﻦ ﺍﺛﺮﻫﺎ
ﺑﻌﺪ ﻣﻮﺕ ‼
Malamai sun ce:
Mamaci bai ambaci Sadaka ba face sai domin
irin girman tasirinta ne da ya gani a bayan
mutuwa.
ﻓﺄﻛﺜﺮﻭﺍ ﻣﻦ ﺍﻟﺼﺪﻗﺔ
ku yawaita yin Sadaka
ﻓﺈﻥ ﺍﻟﻤﺆﻣﻦ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ ﻓﻲ ﻇﻞ ﺻﺪﻗﺘﻪ
hakika Mumini zai kasance a karkashin
inwar Sadakarsa a ranar Kiyama.
ﻭﺃﻓﻀﻞ ﺻﺪﻗﺔ ﺗﻔﻌﻠﻬﺎ ﺍﻵﻥ ﻫﻲ :
Mafificiyar Sadakar da zaka yi a yanzu itace :
ﻧﺸﺮ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻜﻼﻡ ﺑﻨﻴﺔ ﺍﻟﺼﺪﻗﺔ
Yada Wannan magana da niyyar yin Sadaka
ﻷﻥ ﻛﻞ ﻣﻦ ﺳﻴﻄﺒﻖ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻜﻼﻡ ﻭﻳﻌﻠﻤﻪ ﻟﻸﺟﻴﺎﻝ
ﺍﻟﻘﺎﺩﻣﺔ ﻓﺄﺟﺮﻩ
Dominduk wanda ya Atwater da Wannan
magana, to Ladarsa
ﻳﺼﻠﻚ ﺑﺈﺫﻥ ﺍﻟﻠﻪ
Zata sadu da kai da izinin Allah
Share:

Tuesday, 3 January 2017

Hukuncin MMM Business

Hukuncin MMM Business
An dade ana tambayata hukuncin MMM Business daga ciki akwai tambayar da akayimin a July da ya shude a A.B.U Zaria bayan na kamala wata public lecture, kuma yanzu haka akwai tambayoyi da yawa acikin inbox dina. Ko nace ban saniba ko na kyale saboda bani da cikakken bincike akai, amma yanzu nayi bincike akai. Abubuwan da na bincika kafin wannan fatwa sune:
i) Website din MMM
ii) Website din Securities and Exchange Commission, Nigeria, domin jin ra’ayinsu gameda MMM
iii) Online Videos da documentaries gameda MMM Business ciki harda 41 mins video na kaddamar da business din a Nigeira
iv) Tattaunawar da wasu ‘yanuwa sukayi gameda Bussiness din.
Bayan haka nafito da natija kamar haka:
1) MMM Business kamar yadda matar da tayi presentation din shi a Nigeria ta bada definition shine: “MMM is a platform that links [a] giver to the receiver… and when I give I get rewarded for it.” [ Mai bayarwa ya baiwa mai nema domin wanda yabayar ya samu fa’ida] Wannan shine definition din da kowa yake bayarwa koda yake wani lokacin kalimomin sukan sha ban ban amma ma’anar daya ce.
2) Wannan business din baya halasta domin shine ainihin ﺭﺑﺎ ﺍﻟﻔﻀﻞ ” wanda Musulunci ya hana. Ka bada kudi ga mai nema domin a mayarma ka da fiye da abinda ka bayar. Ko kafin ka bayar za’a baka faidar ko bayan ka bayar duka dayane, ko wanda ka baiwa bashi zai baka ko ta wata hanya za'a karbo maka duka daya ne. Ba dole bane sai lokacin da za’a mayar maka ne za’ayi Karin ba, ko wane lokaci Karin zai shiga haram ne, don wannan aka haramta ﺑﻴﻊ ﺍﻟﻌﻴﻨﺔ ” a Musulunci. A MMM za’a baka faidar 30% tun kafin a karbi kudinka.
3) Wannan Business din yana da hadarin gaske domin haramtaccen business ne a Nigeria da kasashe da yawa. Securities and Exchange Commission, Nigeria sun yi gargadi da hana jama’a shiga wanna business da kiransa illegal kamar yadda suka fada a wani article da sukayi publishing a website din su a ranar 30/08/2016 sukace: “The general public is hereby advised to distance themselves from this online scheme. Please note that anyone that subscribe to this illegal activity does so at his/her own risk.” Irin wanna kadai ya isa ya hana wanna Business din
4) Kasashe dayawa sun haramta wannan Business ga jama'ar su domin ganin cewa ba tabbas akwai rudi aciki. Cikin kasashen da suka hana akwai China da South Africa. Samun rudi ﻏﺮﺭ a business zai iya zama dalilin haramcin sa a musulunci.
5) Duk mai hankali ya dibi Business din yasan akwai rudu ciki maiyawan gaske, kuma yasan karshensa jama’a da yawa zasu rasa dukiyar su. A musulunci idan mutun zai bada bashi saida shaidu guda biyu sai idan ya amince da wanda zaibaiwa, a MMM zaka bayarda dukuyarka ga wanda baka sani ba. Saboda hakane ma hukumomi suke yaki dashi. Duk abinda masana sukace karshen sa akwai hadari mai girma to wanna ma ya isa ya haramtashi a Musulunci.
Allah yayi man jaogora.
Jabir Sani Maihula, Nottingham, UK.
15/11/2016
Share:

Abubauwa 4 masu matukar riba a rayuwar mu

*ABUBUWA 4 MASU MATUKAR RIBA ARAYUWAR MU.*

1. SHIRU yana kawo Aminci, Annabi (SAW) ya ce, "wanda yayi imanida ALLAH da ranar karshe ya fadi alheri ko yayi shiru".

2. BIYAYYA tana kawo DAUKAKA, Sayyidina Ali R/A yace, "wanda ya kaskantarda kai ga ALLAH, to ALLAH zai daukakashi"

3. KYAUTA tana kawo MATSAYI, Annabi (SAW) ya ce, "kuyi kyauta za kuso juna".

4. GODIYA Tana kawo KARI, ALLAH (SWT) yace, "idan kun gode zan kara muku. Allah yasa mu dace. Ameen summa Ameen.

Share:

Nasihohi 35 zasu taimakeke wurin samun ingantaçciyar rayuwa

*NASIHOHI 35 zasu taimakeka wurin samun ingantacciyar rayuwa*
______________________________________
1- ka fara yininka da sallar asubahi da azkar domin samun rabo da tsira.

2- ka zarce da istgfari har sai shaidan ya debe
tsammanin samun rabo a jikinka.

3-kar ka daina addu'a dumin itace igiyar tsira

4-ka tuna cewa mala'iku suna rubuta maganganunka.

5-kyawun yatsu shine ka rika qidaya TASBIH dasu.

6- idan ka shiga damuwa da qunci kace" la ila ha illallah".

7- ka sayi addu'ar talakawa da soyayyan marayu da kudadenka.

8-doguwar sujada 1 wanda aka yita saboda tsoron ALLAH yafi maka bene da aka gina na zinari.

9- ka tauna magana kafin kafadeta domin tana iya zama ajalinka.

10- ka guji addu'ar wanda aka zalunta da hawayen wanda aka hana.

11- kafin ka karanta jaridu da mujallu mai zai hana.kafara karanta alqur'ani.

12- ka zama dalilin gyaruwan iyalanka.

13- ka tilastawa ranka wurin bin dokokin Allah ,
domin ita rai tana umarni ne da sabon Allah.

14- kafin tsufar iyayanka ka daure ka samu yardarsu.

15-tsoffin tufafinka sababbi ne a wurin talakawa.

16- kar kayi fushi , domin rayuwa kadan ce ba kamar yadda kake tsammani ba.

17- tare dakai akwai wanda yafi kowa qarfi yafi kowa wadata, shine Allah.

18- kar ka rufe qofar tuba saboda sabon Allah.
19- sallah itace mafi alkhairin abun da zata taimakeka akan musibu da wahalhalu.

20- ka nisanci munanan zato, zaka huta kuma zaka hutar.

21- dalilin kowane damuwa juyawa Allah bayane, ka juyo zuwa gareshi mana.

22-kayi sallah irin wacce kakeso a shigar dakai qabari tare da ita.

23- idan kaji wanda yake gulma , kace dashi: yaji tsoron Allah.

24-ka dawwamar da kanka wurin karanta suratul MULK domin tana tseratarwa.

25- wanda aka hana( yayi hasara) shine wanda aka hanawa sallar dake cike da tsoron Allah , da idon dake zubar da hawaye.

26- kar ka cutar da bayin Allah nagari wadanda suka shagaltu da bautar Allah.

27- ka sanya soyayyar ka duka zuwa ga Allah da manzonsa.

28- ka yafewa wanda yayi gulmarka, domin ya baka kyautar kyakyawan aikinsa ne.

29- Sallah da ambaton Allah da karatun alqur'ani alqawurane masu nauyi akan qirjinka.

30- duk wanda ya tuna da zafin wuta zai iya hakuri akan sabon Allah .

31- indai ana dare gari yana wayewa, to watarana sai labari tsanani zai zama sauqi.

32- ka nisanci ANCE-KACE ( jita-jita) domin kai game da ayyuka kamar dutsene.

33- kayi sallah da tsoron Allah , domin duk abun da zakayi bayan sallar bai kai sallah ba.

34- ka sanya alqur'ani daf dakai , domin karanta aya daya acikinsa yafimaka duniya da abun dake cikinta.

35- rayuwa akwai dadi, mafi dadin rayuwa shine kaganka da iimaninka.
________________________________
ALLAH Yasa Mudace!
____________________________
*TEMAKA KA YADA DOMIN ANFANIN ALUMMA*
Share:

Addu'o'i guda (12) da suka zo a hadisai

ADDU'O'I GUDA (12) DA SUKA ZO A HADISAI:

1. LA'ILAHA ILLAHUWA WAHADAHU LA SHARIKA LAHU LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDA WA HUWA ALA KULLI SHAY'IN QADIR (10 ko 100)

Manzon Allah (S.A.W) yace wanda ya fadi wannan 100 za'a kankare masa zunubai dari, kuma za'a rubuta masa kyawawan aiki dari, kuma a wannan rana bawani da zaizo da wani aikin alheri kamar nasa sai wanda ya fadi fiye da abinda ya fada kuma za tsareshi daga sharrin shaidan da duk wani abun qi kuma yace babu wani zikiri ko addu'a kamar Hailala..

2. LA'ILLA HA ILLAHUWA MALIKUL HAQQUL MUBIN. (100)

Manzon Allah(S.A.W) yace duk wanda ya fadi wanann sau dari a rana bashi ba talauci kuma za'a tsareshi daga fitinar kabari

3. BISMILLAHI RAHAMANI RAHEEM, LA HAULA WALA QUWATA ILLA BILLAHIL ALIYUL AZEEM. (100)

Manzon Allah(S.A.W) ya cewa da Sayyadina Aliyu ba wanda zai fadi wannan kalmomi duk wata masifa ko bala'i duk rintsi sai ya fita.

Annabi Alaihisalam yace wanda yake karanta Lahaula bashi ba talauci kuma kanzi ce daga kanzi na aljanna tana toshe kofofi saba'in na bala'i da cuta mafi kankanta ciki shine bacin rai da damuwa kuma yace: duk wanda samun arziki yayi masa wuya to ya yawaita yin LAHAULA...

Kuma duk wanda yake karanta BISMILLAH (21) bayan isha'i cutar annoba ko ta hauka bazata taba kamashi ba kuma bazai mutuwar fuju'an ba..

4. SUBAHANALLAHI WA BI HAMDIHI. (100)

Shine Tasbihin Annabi Nuhu, shi kuma mala'iku suke Allah yake arzuta dukkan halittar shi..

5. HASBUNALLAHU WA NI'IMAL WAKIL(450)

Shine Tasbihin da Annabi Ibrahima yayi lokacin da aka jefa shi wuta Allah ya mayar masa da ita sanyi itace sahabbai sukayi lokacin yaqin Badar Annabi yayi nasara kuma basu ji tsoron kafirai ba duk da sunfisu yawa..

6.  LA ILA HA ILLA ANTA SUBAHANAKA INNI KUNTU MINAL ZALIMIN (sau 41 ko 100)

Manzon Allah(S.A.W)  yace: "Addu'ar Annabi Yunusa lokacin da yake cikin kifi babu wani mumini da zai roki Allah wani abu dake damunsa face Allah ya maganata masa. Kuma yace Ismullahil Azeem, sunan Allah ne da in akayi addu'a yake amsawa, kuma idan aka rokeshi yake bayarwa itace addu'ar Annabi Yunusa.

7. ASTAGFURULLAHA LAZI LA'ILA HA ILLAHUWAL HAYYUL QAYYUM WA ATUBU ILAIHI. (100)

Manzon Allah(S.A.W) yace: Ba wanda zai fadi haka fache an gafarta masa duk zunubansa koda sun kai kunfar kogi. kuma Alqawarin Allah ne a cikin suratul hudu, duk wanda ya lazumci Istigfari zai jiyar dashi dadi kuma yabashi arziki kan arziki kuma zai bashi girma da daukaka..

8. SUBAHANALLAHI WABI HAMDIHI SUBAHANALLAHIL AZEEM ASTAGFRULLAH(100 kafin Asubah)

Wani Sahabi yazo wajen Manzon Allah Alaihisalam yayi masa kukan duniya ta juya masa baya(talauci)  yasanar dashi tasbihin Mala'iku sai Annabi yasanar dashi yace ya ringa karantashi bayan raka'a tainul fajar kafin Asuba. Bai gushe ba sai da ya dawo wajen Annabi Alaihisalam yace Allah yabashi duniya (arziki)  har ya rasa inda zai kaita..

9. YA HAYYU YA QAYYUM LA'ILA HA ILLA ANTA(sau41)

Imamu Shafi'i (Rahimahullah) yayita mafarki da Annabi sai watarana sai yace shin kasanar dani wani abu da Allah zai dinga haskaka mani kuma ya raya zuciyata akan imani(ibada) sai Annabi ya sanar dashi wannan. Ya ringa yi kafin Asubah ko bayan Asubah sau 41 (Saboda haka ba wanda zai lazumceta sai yazama mai maida hankali akan ibada kuma yazama wanda mutane zasu dinga jin maganarsa kuma abin so a cikinsu...

10. SUBAHANALLAHI(33) WAL HAMDULLAHI(33) WAL LAHU AKBAR(34) da dare kafin bacci

Wannan shine Tasbihin da Annabi ya bawa Sayyada Fatimah lokacin da ta nemi Annabi ya bata hadimi sai ya sanar da ita wannan tasbihi da ta ringa yi kullum kafin ta kwanta bacci shine mafi alkhairi a gareta da yabata hadimi..

11. SUBAHANALLAHI(10) WALHAMDULLAHI(10) WALLAHU AKBAR(10) bayan Salloli biyar

Watarana Ummu Sulaim tazo wajen Annabi Alaihisalam tace ya sanar da ita wani abu da zata dinga rokon Allah dashi sai yace tayi wannnan tasbihin sai ta roki Allah bukatarta za ace anzartar anzartar (wato an amsa mata abinda ta roka)

12. SALATIN ANNBI (10 ko 100 ko 500 ko 1000 har abinda yayi sama)

Manzon Allah(S.A.W)  yace: "wanda bukatarsa tayi masa wahalar samu to  ya yawaita salati gareni lalle yana tafiyar da damuwa da bakin ciki da kuncin rayuwa kuma yana yawaita arziki da kuma biyan bukatu.

Kuma Imamu Ghazali yace: Duk wanda yake salati Annabi 500 kullum bashi ba talauci kuma bazai mutu ba sai yaga Annabi Alaihisalam.

Ubangiji ALLAH ya sa mu dace duniya da lahira, 😭😭😭

Don Allah ina roqon ku da ku saka ni cikin addu'ar ku, Allah yabamu lafia, arziqi da wadata, ya albarkaci rayuwar mu, ya amince mana duniya da lahira, ya kuma magance mana duk abinda yake damun mu, ya biya mana dukkan bukatun  Dan shiga group din mu mai tarin Albarka na🕌THE HOLY RAMADAN 🕋 sai katura slm tare da rubuta Ramadan ta wannan number 08037902332  pls share it to others groups
Share:

Yadda ake wankan janaba dana haila

*YADDA AKE WANKAN JANABA DANA HAILA*
.
.
*A ciki zamuga Bayanin Maniyyi da Maziyyi da Wadiyyi da Jinin haila* inkayi seka turama wani
:
DAGA ZAUREN
*Khulafa'ur-rashiidun*
:
Lucture 8
.
Muna me farawa da sunan ALLAH m rahama me jinqai, Tsira da amincin ALLAH su tabbaga ga shugaban halitta Annabi Muhammad (ﷺ).  Tare dashi da iyalansa da wadan da suka biyo bayan shi da kyautatawa irin au Sayyidina Abubakar, umar, usman, aliyu, dalha, zubair ibin auwam da sauran su.
;
A har kullum muna bada hakuri ga masu chanjamana  post suyi hakuri dan girman ALLAH kada ku chanja mana wannan post in, idan ka chanja ka cuci wanda ze karanta na gaba, ka hanashi  sauraron darasin baya dakuma nagaba wanda zamu gabatar da yaddan ALLAH,  Idan bazaka iya tura ma wani ba, ka hakura kada ka chanja mana post in mu dan ALLAHU.
°°°°°°°°°°°
*
*BABBANCHI TSAKANIN MANIYI DA MAZIYI DA WADIYI, DA RUWAN CIWON SANYI!!*
*
🚩MANIYYI-Yana fita ayayin babban sha'awa, kokuma ta hanyan mafarki, ko saduwa,ko wasa da Al-aura, kalan shi fari ne, yana da kauri sannan yana dan wari haka,  yayin fitan shi yana tunkudan juna, inyafiata kuma yana sa kasala./ kalan maniyin mace  yana daukeda launin yellow.
:
🚩MAZIYYI-wani kalan ruwan ne shima dayake fitowa daga Al-aura yayi qaramar sha'awa, maziyyi baida kauri yana nan da yaukie, yana fita yayina baligi yafara tinanin kusantan mace komace tayi sha'awa  namiji, idan ya fito tsarki kawai akemar sannan a wanke gurin.
:
🚩WADDIYI- Wani ruwa ne makaman cin maniyyi amma baya fita se bayan mutum ya girma wato ya tsufa, yawanci kuma yafi fitowa bayan gama fitsari
:
🚩CIWON SANYI-  wani ruwa ne me kauri da wari-wari dayake kwaranya kullum a farjin mata,  batare da wani sha'awa ba, kalan shi yakusa kama da maniyyi, yana fitane sanadiyan cuta, shi wannan yana buqatan inmace ta gani taje asibiti a bata magani!!
🚩
JININ HAILA
*
HAILA
     Shine wani jinin dake fita a farjin mace alhani lafiyarta qalau ba haihuwa tayi ba. Kuma ba kwanciya da wani na miji da yafi qarfinta ya fasa ta ba. Toh wannan shine jinin HAILA.
*
*
Duk sanda aka ga jini a farjin 'ya mace mai shekaru 7,8,9,10,12 ba tare da wani matsala a farjinta koh mahaifarta ba, ba kuma wani na miji da dafi qarfinta ya fasa ya ba toh wannan za abashi hukuncin jinin HAILA.
*
*
Balagar mace yana da alaqa da irin wajan da take rayuwa, yanayin halittar, jin dadinta. Shiyasa wasu suke fara jinin HAILA da wuri wasu koh nasu yake jinkiri.
*Misali;  Mazauna qasashen yammacin duniya inda akwai zafi baza a hada su da wurare irin su qasashen Russia da Afganistan ba sabo da wajene mai sanyin gaske.
.
.
Haka kuma mata masu cin abubuwan gina jiki da 'ya'yan itatuwa dole yanayin jinin su ya bambamta da na wa'yanda basu samu damar cin wa'yannan abubuwa ba.
.
.
LAUNUKAN JININ HAILA
*
(1) BAQI:
      (ba ana nufin baqi kalar gashi ba) ana nufin Ja mai duhu tare da qarni
   [Imam Abu dawud Nisa'e, Imam daru kudini, Ibn Hibban acikin sahihu muslim]
*
*
(2) JA JAWUR A
        Shine asalin launin jini. Yana dauke da qarni
*
*
(3) FATSE- FATSE
        (Kamar gwaiduwar kwai)
*
*
(4) RUWAN QASA
        Yana nan ne kamar qasa da aka kwaba da ruwa., yana da dan duhu duhu.
:
🚩KWANA KIN HAILA
.
.
Kwana kin haila ba a gayyade adadin sa, galibi wasu mata basa wuce kwana 5 zuwa 7 sai dai-daiku daga cikin su da suke zarce hakan.
.
.
ALAMUN DAUKEWA JININ HAILA
*
*Bushewar fargi qarqaf
        Idan farji ya bushe ba wani alama na jini koh kadan. Toh tsarki ya samu sai ayi wanka.
    Anaso a tanadi auduga mai kyau koh wani faril gyalle yadda za asa a farjin a duba domin tabbatar da tsarkakuwar
.
.
*CHANJAWAR KALAR JINI
   Mun riga munyi bayanin kalolin jini, Idan jinin hailarki baqi ne toh randa ya chanja kala ya koma Ja koh fatsi-fatsi bayan kuma kin cika adadin kwanakin da kika saba yi na hailar toh kin samu tsarki. Sai kiyi wanka ki ci gaba da ibadodin ki.
    SAI DE
       Idan wannan kalar jinin da ya chanje wato (istihada, ana qiran sa jinin ciwo koh jinin jijiya) bai dauke ba toh zaki riqa sake alwala a kowacce sallah, ki wanke inda jinin ma ya ta6a. Har sai sanda jinin ya dauke.
Amma idan ya fito bayan kin riga kin fara sallah toh shikenan ki ci gaba da sallarki.
*
🚩JININ BIKIE-/jinin haihuwa, shima kalanshi daya da na Haila, Sedai shimafi tsawon kwanakinshi shine kwana 60.
:
*MIYAKE WAJABTA WANKAN  JANABA?*
:
fitan maniyyi ta  kowacce hanya, in ma ta hanyan biyan buqata da matar ka, ko ta hanyar mafarki, ko kuma ta hanyan jin babban sha'awa da yayi sanadiyan fitan maniyi.
:
Shigar da kan kachiya cikin farji, yana wajabbata wanka koda kuwa baku fitar da maniyyi ba, wanka yawajaba agare ku.
:
Idan mace ta gama jinin Al-ada, da wance jinin haihuwa ya  dauke mata, wannan duka wajibi ne da suyi wanka.
*
Sekuma wankan shiga musulunchi, da wankan daukan harami. sannan se wankan gawa, gawanda ba'a filin yakie ya mutu ba, kokuma wanda ya qone sanadiyan gobara, ko lalacewan gaggan jiki. Sannan anso wanda yayi wankan gawa yayi wanka shima.
*
Wannan kusan sune wajiban wanka Da nasani.
:
*YA AKE WANKAN JANABA?*
*
Daga nana Aisha uwar muminai ALLAH yaqara mata yadda, tace:- "Manzon ALLAH(ﷺ) yakasance idan zaiyi wankan janaba, sai ya wanke  hannayen sa, sannan yayi wanka, sannan ya duddurza, ya tsattsefe gashinsa da hannayen sa, har inda ya tabbatar cewa ya jiqa fatar sa (kai) sai ya kwaranya masa (shi kan) ruwa sau uku, sannan ya wanke sauran jikn sa" tace;  na kasance ina yin wanka nida manzon  ALLAH (ﷺ) A kwary(baho) daya muna kamfata daga cikin ta baki daya"
(bukari da muslim)
:
_Dan uwa ka ta6ayin wankan janaba da matar ka bayan ta haihu sama da yara uku?  ina tinanin tinda kukayi lokacin kuna shekaran farko baku sake yiba_
*
Daga maimuna 'yar haris (R.A) matar Annabi (ﷺ) uwar muminai tace : "naje wajen Manzon ALLAH (ﷺ) da ruwan wanka janaba, sai ya  zuba ruwa da damansa aan hagunsa sau biyu k sau uku, sannan ya wanke hannunsa sau biyu ko sau uku, sannan ya wanke Al-auran sa, sannan ya daki qasa ko bango (in ba qasa a gefan ka zaka iya wanke hannunka da sabulu)  da hannun sa, sau biyu ko sau uku, sannan ya kurkure baki, ya shakie ruwa, ya wanke fuskar sa da damatsan sa, sannan ya kwaranya ruwa a bisa kansa, sannan y wanke jikinsa, sannan ya koma gefe ya wanke qafafunsa" tace " saina zo masa da kyalle (tawul) sai bai kar6e ba, sai ya riqa sharce ruwan da hannayen sa"
:
(Bukari da muslim)
:
_Anan zamu danyi bayani akan goge jiki da hannu, idan ka goge jikinka da hannu sekafi jin dadin wannan wankan, ba'a musu kusa da gida ka jarraba yauinkaje wanka koda kuwa bana janaba ba_
*
Wannan wanka👆🏽👆, haka akeyi idan mutum zeje sallan juma'a, idi, qarama ko babba, haka zalika anayi a wankan haila. idan kayi baka buqatan se ka sake Al-wala kawai sallah zakayi. sabda wankan karan kanshi Al-wala ne.
:
*YA AKE WANKAN HAILA?*
*
An karbo daga Aishata Allah Ya yarda da ita. Lallai Asma'a ta tambayi Manzon Allah (ﷺ)game da wanka haila, sai Yace: Dayarku ta dauki ruwanta da magaryarta tayi tsarki kuma ta kyautat tsarki sa'annan ta zuba ruwa a kanta, kuma ta cuda shi.., cudawa mai tsanani har sai ta sadar da ruwa ga asalin gashinta (tushen sa) sa'annan ta game jikinta da ruwa, sa'annan ta sami wani yanki na auduga mai kanshi ta tsarkaka da ita.
Sai Asma'a tace: Ya ya zata tsarkaka da ita? Sai Manzon Allah (ﷺ) yace: Subhanaallah! Nace tayi tsarku da ita. Sai Aisha tace: Kamar ita (Asma'a) tana boye wannan. Tace ma ta, "Abinda Annabi  (ﷺ)yake nufi shine ki bi gurbin jinin da ita.
:
(Malamai sun hadu akan shi)
*
Batare da tsawai tawa ba idan mace tana jinin haila bayan ta qare zatayi wanka, to wajibi ne akan ta da ta war ware gashin kanta kaman yadda hadisi ya tabbata a bukari hadisi na317  da Annabi (ﷺ) yace ma nana Aisha ta koma ta dakko miqati sannan ta warware gashinta..
:
An fani da magarya da miski  ba qaramin amfani yake dashi ba wajen taimakawa mace,  ki jarraba  baiwar ALLAH.
;
Dangane da wadan da jinin janaba ta same su a lokacin suna jinin Al-aada,  Abinda yafi shine tayi wanka biyu, daga janaba tasameta tayi wankan janaba, sanna idanjini ya dauke tayina haila. Wallahu a,alamu.
;
HARAMCHIN YIN WANKA DA RAGOWAN RUWAN WANKAN DA WANI YAYI AMFANI DASHI.
:
hadisi Sahihi  ya tabbata a cikin  littafin Bulugul maram Annabi ya hana wanka da ragowan ruwan wankan da wani ya rage haka ya hana wanka da ragowan ruwan mace"
*
 A hadisin dake jikin shi kuma an rawaiyo Annabi (ﷺ) yayu wanka da ragowan ruwan wankan matar shi maimuna":/
:
Wannan kusisiyace ta Annabi muhammad (ﷺ)   amma kai bai halatta kayi wanka da ragowan ruwan wankan matarka ba koitatayi da na ka.  Amma ba laipi kuyi wanka tare.
:
********
Idan ka sanar da wani kaima kayi da'awa kuma kayi taimakekkeniya akan biyayya wa ALLAH, Abin da mamaki sosaiakwai wadanda basu sani ba, yakamata kaisar musu,  sedai a kiyayi turawa  a groups inda suke da Dokan hana tura post, idn ka turabaka cire ka, kai kaso.
;
ANAN ZAN DAKATA  SE KUMA IN ALLAH YAKAIMU WANISHIRIN KUMA,  IDAN ALLAH YASO ZAMUYI BAYANI AKAN YADDA AKE WANKAN GAWA IN SHA ALLAHU
-------***-----------
MUHAMMAD AUWAL ABU JA'AFAR AL-POTISKUMAWI
•°°°°°°°°•
02/01/1438-03-10/2016
_________________
masu buqatan kasancewa damu, se su turo da suna da kuma sunan qasar su, a daure ayimana sallama cikakka dan samun lada cikekke.
*
→ MasU buqatan kasan cewa damu a whatsapp.
+2347035269582
+2348063796175
 tare da cikakken suna da kuma cikakkiyar sallama. don samun karatuttukan mu a facebook, saikubi, mobile.facebook.com/Khulafaur-Rashiidun-1812718708973541/ Subhanak Allahumma wabi hamdika Nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka
Wana tubu ilaik.
Share:

Maganin istihada (zuban jinin haila sama da kanaki, masu yawa !!!)

*MAGANIN ISTIHADA ( ZUBAN JININ HAILA SAMA DA KWANAKII, MASU YAWA!!!)*
:
Daga Zauren
*Khulafa'ur-rashiidun*
:
Assalamu Alaikum warahamatullah  Haqiqa mata dayawa suna fama da cutan ISTIHADA (wato zuban jini sama da kwanakin haila, wata ma nata yanakai wata 3) da lilin haka yasa muka binciko maganin wannan  matsalan.
.
Wasu nasu matsalace ta aljanu, ko sihiri, idan kunyi baiyi amfani ba, ku jarraba yin ruquyya!!.
.            hanya kadan da zaku gane cewa sihirine, idan mijinki yazo miki, sekiga jini ya fara kwaranya!!!  
.
Wata kuma nata jijiya ne yake samun matsala, seya fara zubar dajini!!
________________________________
📍- Ta samu Saiwar magarya ta tafasa da 'yar jar kanwa seta rinqa sha kamar so uku a rana
.
📍 *Ta samu ganyen runhu, balma se ta hade guri daya ta jiqa ya kwana seta riqa Sha.*

📍 Ko kuma ta tafasa' ya'yan kabewa tare da madara ko nono, amma ta tafasa su a tare seta riqa sha insha Allah ze tsaya.

📍 *Ko ta samu garin habbatus sauda da ganyen na'a na'a a tafasa asha*
~_____________________________~          
         
:
A lokacinda kikaga Jini ya miki yawa wato ya wuce iyaka to kinemi wannan maganin, sauki kuma yana wajan ALLAH.
.
Kusani ba wata cuta face Seda ALLAH ya sauke mata Maganin ta, sekuma ya bar Saukin a gurin shi, ka nemi magani ka sha wanda ya dace da sunnah.
______________________________
*Hakan koda bakya fama da wannan matsalan to kiyi Qoqarin haddace wa, saboda mata dayawa suna fama da wannan matsalan.*.
.
.         hukuncin me fitar da wannan jinin, na wuce iyaka(JININ CUTA), fatawa mafi saukie shine  tayi alwala a kowacce sallah Tare dayin tsarki, kaman yadda takeyin tsarkin fitsari.
.
Wannan jinin baya haramta mijinkibya sadu dake. Kaman yadda baya hana sallah da karatun qur'ani da sauran ibadu, wallahu a,alamu
.
*Kutayamu yadashi  amma dai a kiyayi turawa zauren da kukasan zasu cire ku.  Fatan mu ALLAH  ya daura mu akan dai-,dai yasa mu gama da duniya lapiya, yasa wannan aikin danshi mukeyi.*
_______________________________
*MUHIMMIYAN SANAR WA*
      _Muba masu bada magani bane sannan ba kowacce cuta bane, muka sani maganin ta, idan munce bamu sani ba, to bamu saniba shiyasa, mukace bamusani ba!!…_
~;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;;~
*29-01-1438*-31/10/2016
.
→ MasU buqatan kasan cewa damu a whatsapp.
+2347035269582
+2348063796175
 tare da cikakken suna da kuma cikakkiyar sallama. don samun karatuttukan mu a facebook, saikubi, mobile.facebook.com/Khulafaur-Rashiidun-1812718708973541/ Subhanak Allahumma wabi hamdika Nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka
Wana tubu ilaik.
Share:

Sayyidul istigfar

*بسم الله الر حمن الر حيم*

*SAYYIDIL ISTIGFARIN*
 (shugan Istigfari)
.
.
.DAGA ZAUREN
*Khulafaur-rashiidun.*
.
Lucture (13)
                          Assalamu alaikum    warahamatullah    innal hamdulillah nahamaduhu wanasta inuhu Wana uzubillahi minash shaidanur rajim.
.
*wassalatu wassalamu ala nabiyyina muhammad (ﷺ) wa'alihi wa sahabihi waman tabi ihsani ila yaumin din,*  godia ya tabbata ga ALLAH ubanigiji ma madukakin sarki daya azurtamu da manzon rahama(ﷺ), wanda yadamu da damuwar mu, meson kowa ya shiga Aljannah, ALLAH  ka sanya muna ciki.
.
*'yan uwa dukkan wani me zunubi, a ranan gobe qiyama se an mar hisabi, koya shaa! ko a kama shi!!, sakamakon kasancewan mu Yan adam masu rauni, hakan yasa kullum muna cikin zunibi!! se ALLAH yace;-*
 "...LALLE ALLAH YANASON MASU TUBA KUMA YANASON MASUTSARKI"   awani gurin yace  ''DA ANBATON ALLAH AKE SAMUN NUTSUWA".
.
Annabi alaihissalam ya koyar da sahabbai istigarai me girma, wanda harta kai ana kiranta da shugaban istigfari.
.
Tabbas badan muna tuba ma ALLAH ba, da tuni an shafar damu daga doron qasa.
.
Kasancewar zunuban mu sunyi mana yawa!!
.
shiyasa nayi tinanin tuna tar damu wannan addu,an dan mu sake hadda ce ta, wato *sayyidil istigfari*
_________________________________________
.
*اللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّي لَّا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ، خَلَقْتَنِي وَأَنَا عَبْدُكَ، وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ وَوَعْدِكَ مَا اسْتَطَعْتُ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا صَنَعْتُ، أَبُوءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ عَلَيَّ، وَأَبُوءُ بِذَنْبِي فَاغْفِر لِي فَإِنَّهُ لَا يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا أَنْتَ*
.
*Allaahumma 'Anta Rabbee laa 'ilaaha 'illaa 'Anta, khalaqtanee wa 'anaa 'abduka, wa 'anaa 'alaa 'ahdika wa wa'dika mas-tata'tu, 'a'oothu bika min sharri maa sana'tu, 'aboo'u laka bini'matika 'alayya, wa 'aboo'u bithanbee faghfir lee fa'innahu laa yaghfiruth-thunooba 'illaa 'Anta.*
_____________________________________________

_*"YA ALLAH kaine ubangiji na, babu abin bautawa da gaskiya SAI kai. Kai ka halicceni, kuma ni bawanka ne, kuma ina kan alqawarin dana yimaka ( na kadaitaka da bauta)  akuma alqawarin d kayimin ( nashigar da wanda baiyimaka shirk ba, gidan Aljannah) gwargwadon ikona. Ina neman tsarin-ka daga sharin abinda na aikata, ina tabbatar da ni'imar ka gare ni, kuma ina tabbatar da zunubi na; ka gafartamini, domin ba bai gafarta zunubi se kai)"*_
.
_(Bukhari 7/150, -Nasa'i, da-Tirmizi.}_
_________________________________________
 Karka 6ata lokacin ka akan ibadan da ba daga Annabi  (ﷺ) take Ba.
dan haka yanada kyau duk abinda zamuyi in ya shafi addini to mu tabbatar munada hujja me kyau.
.
*Manzon ALLAH yace duk wanda ya karanta ta, da safe ba abinda ze hanashi shiga aljanna sedai mutuwa* (in baka shigaba to baka mutu ba, matuqar kana kan aqida ingan tacciya).
.
Haka zalika inka karanta da yamma, *amma duk dahaka anason ka  karantata da kowana lokaCi bayan kayi na safe da yamma.*
.
Sannan daga cikin falalan ta tana kankare zunubi me tsoka  wanda ya guda na tsakanin ka  ALLAH.
.
_Kasani me karatu Allah fa baya yafe lefin wani akan wani idan ka cuci wani to Allah ze bi masa hakkinsa koda kayi wannan Adu,ar bazata hana a tambayeka hakkin wani ba a lahira dan haka ka gyara tsakanin ka da Allah sannan kadawo ka gyara tsakanin ka da mutane._
.
_Sannan akwai wani hadisi shima a cikin bulugul maram inda Annabi   (ﷺ) yace: duk wanda yake karanta *Ayatul kursiyu* da *Kul'huwallahu* qafa uku a ko wace salla ta farilla to babu abinda ze hanaka Shiga Aljanna sedai in baka mutuba._
.
_Bukhari da Muslim ne suka rawai to shi ibn Hibbana ya ingantashi._

*Yan uwa akwai addu'oi dayawa ,idan mundage dayinsu zasu rabamu da fadawa bidi,a dakuma shirka da kuma dena ziyar tan bokaye..*
_______________________________________
     _lucture mu nagaba in sha ALLAHU 👉🏿(KIYI HANKALI DA QAWA YENKI DANGANE DA NEMAN MAGANI)  tsokaci duk wanda yaje wajen boka ko dan duba hakiqa ya kafurta inbaiyi imandashi ba baza,a kar6i sallan sa na kwana 40 ba!!!_
________________________________________
Dan uwanku a musulunci
.
*Muhammad Auwal Abu-Ja'afar*
*Al-potiskumawi*
.
08/03/1438;:;: 08/12/2016
.
→ MasU buqatan kasan cewa damu a whatsapp.
+2347035269582
+2348133238265
 tare da cikakken suna da kuma cikakkiyar sallama. don samun karatuttukan mu a facebook, saikubi, mobile.facebook.com/Khulafaur-Rashiidun-1812718708973541/ Subhanak Allahumma wabi hamdika Nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka
Wana tubu ilaik.
.
Kuna iya samun mu ta wannan addreshin
http://Www.khulafaurrashidun.blogspot.com
Share:

Wasiyan mala'ika jibrilu ga annabi S A W

WASIYYAR MALA'IKA JIBRILU GA ANNABI S.A.W

Wata rana Mala'ika Jibrilu S.a.w yazo wajan Ma'aikin Allah s.a.w sai yace dashi;

{Ya Muhammad, ka rayu aduniya duk yanda ka keso,watan wata rana kai mai mutuwane, kayi duk aikin da kakeso watan wata rana za'a sakamaka abinda ka aikata,Kuma kaso duk wanda kaso,watan watarana zaku rabu dashi.

Lallai kasani, mafificiyar daukakar Mumini itace Sallar dare,Kuma mumini yana samun daukakane gwargwadon yin afuwarsa ga yan uwansa Mutane.

#SaheehuT Targheeb~824

Fadakarwa.

Acikin wannan wasiya mai tsada zamu dauki guziri guda biyar~5

1-Duk yanda ka zauna aduniya watarana sai ka mutu, da akwai wanda zai zauna aduniya bai mutuba da Annabi s.a.w

2-Dukkan ayyukan da ka aikata anan duniya sune Allah zai saka maka agobe alkiyama.

3-Kuma duk yanda kake so ko kaunar mutum wata rana sai mutuwa ta rabaku.

4-babban aikin da yake sanya mumini ya samu mafi daukakar matsayi awajan Allah,itace Sallar dare.

5-Idan kana yawan yafiya ga Yan uwanka mutane zaka sami izza da buwaya.

Allah ka bamu ikon kiyaye wannan wasiyaa.
Share:

Archive

Unordered List

Support