Wasiyan mala'ika jibrilu ga annabi S A W ~ Duniyarfatawa.com™

Š²arÄøarÄøĻ… da zĻ…wa ÄøĻ…cĪ¹ gaŠ²a da Äøaѕancewa da wannan ѕŠ½aŅ“Ī¹n doŠ¼Ī¹n cĪ¹gaŠ²a da ѕaŠ¼Ļ…n Ī¹nganтaттĻ…n Ņ“aтawa a cĪ¹ÄøĪ¹n vĪ¹deo/aĻ…dĪ¹o Äøo rĻ…Š²Ļ…Ń‚Ļ… daga Š¼alĻ…Š¼a daŠ²an-daŠ²an na aŠ½lĻ…Ń•-ѕĻ…nnaŠ½ Š¼Ļ…ngode

Recent Post

Tuesday, 3 January 2017

Wasiyan mala'ika jibrilu ga annabi S A W

WASIYYAR MALA'IKA JIBRILU GA ANNABI S.A.W

Wata rana Mala'ika Jibrilu S.a.w yazo wajan Ma'aikin Allah s.a.w sai yace dashi;

{Ya Muhammad, ka rayu aduniya duk yanda ka keso,watan wata rana kai mai mutuwane, kayi duk aikin da kakeso watan wata rana za'a sakamaka abinda ka aikata,Kuma kaso duk wanda kaso,watan watarana zaku rabu dashi.

Lallai kasani, mafificiyar daukakar Mumini itace Sallar dare,Kuma mumini yana samun daukakane gwargwadon yin afuwarsa ga yan uwansa Mutane.

#SaheehuT Targheeb~824

Fadakarwa.

Acikin wannan wasiya mai tsada zamu dauki guziri guda biyar~5

1-Duk yanda ka zauna aduniya watarana sai ka mutu, da akwai wanda zai zauna aduniya bai mutuba da Annabi s.a.w

2-Dukkan ayyukan da ka aikata anan duniya sune Allah zai saka maka agobe alkiyama.

3-Kuma duk yanda kake so ko kaunar mutum wata rana sai mutuwa ta rabaku.

4-babban aikin da yake sanya mumini ya samu mafi daukakar matsayi awajan Allah,itace Sallar dare.

5-Idan kana yawan yafiya ga Yan uwanka mutane zaka sami izza da buwaya.

Allah ka bamu ikon kiyaye wannan wasiyaa.
Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support