Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Saturday, 8 July 2017

Goron sallah 3 daga (kitabu was-sunnah)

*GORON SALLAH3???!!!*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
:
Yau 14-10-1438, wacce tayi dai dai da 8-7-2017***
:
Taken Lekca
.
*GORON SALLAH-3*
-
Wannan shine bayani na Uku
....
....
*ﺇﻥ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ، ﻧﺤﻤﺪﻩ ﻭﻧﺴﺘﻌﻴﻨﻪ، ﻭﻧﺴﺘﻐﻔﺮﻩ، ﻭﻧﻌﻮﺫ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻣﻦ ﺷﺮﻭﺭ ﺃﻧﻔﺴﻨﺎ، ﻭﺳﻴﺌﺎﺕ ﺃﻋﻤﺎﻟﻨﺎ، ﻣﻦ ﻳﻬﺪﻩ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻼ ﻣﻀﻞ ﻟﻪ، ﻭﻣﻦ ﻳﻀﻠﻞ ﻓﻼ ﻫﺎﺩﻱ ﻟﻪ، ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﻋﺒﺪﻩ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ*
.
_Bayan haka Inbaku mantaba acikin bayaninda ya gabata mun tsayane a inda Annabi Ibrahim (AS) ya dauko matarsa Hajara da Danta Isma'il wanda shekarunsa biyu a duniya a wannan lokacin seya kawosu wannan kwari wanda yake acikin dokar daji ya ajjesu, yajuya yakama gabansa zetafi, ananne ita hajara setabishi abaya, har yakai saman wani tudu inda ake cema saniyya seta qwala masa kira tace Ya Ibrahim yaya zaka kawomu wannan daujin kuna katafi kabarmu?? Shin Allah ne yace kayi hakan?? Seyace Eh Allah ne yace inyi hakan, sekawai tace to tafi abinka insha Allahu nasan Allah baze tozartamu ba*****_
          _Anan yakamata mudanyi ratse mujawo hankalin mazaje akan wayansu ababe guda biyu, na farko dai shine yanada kyau maza su sani cewa haqqine akansu su raba tsakanin matayensu musamman idan yazamana babu jituwa tsakanin matayen, wanda asalima shine ba,a hada mata guda biyu a gida daya batareda amincewarsuba, inhar zaka qara aure to lallai katanadarma kowacce gidan da zaka ajjeta, amma idan bazakayi hakanba to lallaine kafara neman yardarsu kafin kadasu inkuma daya tace bata yarda ka hadata gida da wata matar takaba, to lallai sedai ko kafasa auren kokuma kanema mata inda zata zauna, wannan shine farkon darasinda muka samu a wannan qissa ta Dauke hajara da Annabi Ibrahim yayi ya rabata da Uwargida Sarah***_
              _Abu nabiyu kuma shine mazaje suzama sun sabawa matarsu da gaskiya banda qarya, kunga dai irin wajenda Annabi Ibrahim yazo ya ajjiye Hajara wajene wanda yake dokar daji babu mutane awajen amma dayake yasaba mata da gaskiya dakuma tsoron Allah, tanaji yace Allah ne yace yakawota shikena  babu musuba gaddama ta amince, shin kadauka kaine hakan tafaru da kai shin kana tsammanin cewa matarka zata yarda dakai bazata qaryatakaba saboda tasan halinka????_
          _Saboda haka yanada kyau muzama masu gaskiya a zamantakewarda mukeyi da matayenmu kada musaba musu da qarya kuma mudena daukarwa kanmu abinda mukasan cewa bazamu iyaba****_
_Kuma wannan yana nuna mana muhimmancin barin mata suyi karatun Addini sufahimci girman Allah yadda zasu dinga mutunta al'amarin ubangiji yadda bazata kasance tanada za6iba aduk wani al'amrinda aka sanya ubangiji acikinsa*****_
             _Toh bayan Hajara takoma can wajenda ya ajjiyeta, shikuma Annabi Ibrahim yahau saman tsauni seyafadi wannan addu'ar wacce tazo acikin Suratul Ibrahim Ayata 37:_
*ﺭَﺑَّﻨَﺎ ﺇِﻧِّﻲ ﺃَﺳْﻜَﻨْﺖُ ﻣِﻦْ ﺫُﺭِّﻳَّﺘِﻲ ﺑِﻮَﺍﺩٍ ﻏَﻴْﺮِ ﺫِﻱ ﺯَﺭْﻉٍ ﻋِﻨْﺪَ ﺑَﻴْﺘِﻚَ ﺍﻟْﻤُﺤَﺮَّﻡِ ﺭَﺑَّﻨَﺎ ﻟِﻴُﻘِﻴﻤُﻮﺍ ﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓَ ﻓَﺎﺟْﻌَﻞْ ﺃَﻓْﺌِﺪَﺓً ﻣِﻦَ ﺍﻟﻨَّﺎﺱِ ﺗَﻬْﻮِﻱ ﺇِﻟَﻴْﻬِﻢْ ﻭَﺍﺭْﺯُﻗْﻬُﻢْ ﻣِﻦَ ﺍﻟﺜَّﻤَﺮَﺍﺕِ lﻟَﻌَﻠَّﻬُﻢْ ﻳَﺸْﻜُﺮُﻭﻥَ ‏( 37 ‏)*
*YA UBANGIJINMU! LALLAINE NI, NA ZAUNARDA WASU DAGA CIKIN ZURIYATA AWANI KWARI WANDA BABU SHUKA A WURIN DAKINKA ME ALFARMA. YA UBANGIJINMU! DOMIN SU TSAYARDA SALLAH SEKUMA KA SANYA ZUKATA DAGA MUTANE SUNA GAGGAUWAR BEGEN ZUWA GARESU, KUMA KA AZURTASU DAGA 'YA'YAN ITACE MEYIWUWA NE SURIQA GODEWA****
:
:
Zamu dakata Anan sekuma bayani nagaba Idan Allah yakaimu
=
=
_Almajirinku dan mutanen kabo_
'
_Jameel Alhassan Haruna Kabo_
_Alwahhaby-Assalafy_
.
 Nake mana fatan Alheri wassalamu alaikum
..
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka  Wa,atubu ilaika
Share:

Goron sallah 2 daga (kitabu was-sunnah)

*GORON SALLAH2???!!!*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
:
Yau 13-10-1438, wacce tayi dai dai da 7-7-2017***
:
Taken Lekca
.
*GORON SALLAH-2*
-
Wannan shine bayani na Biyu
....
....
*ﺇﻥ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ، ﻧﺤﻤﺪﻩ ﻭﻧﺴﺘﻌﻴﻨﻪ، ﻭﻧﺴﺘﻐﻔﺮﻩ، ﻭﻧﻌﻮﺫ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻣﻦ ﺷﺮﻭﺭ ﺃﻧﻔﺴﻨﺎ، ﻭﺳﻴﺌﺎﺕ ﺃﻋﻤﺎﻟﻨﺎ، ﻣﻦ ﻳﻬﺪﻩ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻼ ﻣﻀﻞ ﻟﻪ، ﻭﻣﻦ ﻳﻀﻠﻞ ﻓﻼ ﻫﺎﺩﻱ ﻟﻪ، ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﻋﺒﺪﻩ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ*
.
_Bayan haka In baku mantaba abaya mun tsayane Inda Wannan Azzalumin sarki ya sauka daga wannan qa'idar tashi, wato asali munce dama baya kama wacce batada miji, to amma yadda tsabar kyawu na Sarah ya tafiyarda tunaninsa duk da cewa ta manyanta amma take wannan sarki yakama sarah dukda cewa tagaya mishi cewa Annani Ibrahim (As) dan uwantane ba mijintaba****_
             _Alokacinda sarkinnan ya kadaita da ita a daki babu kowa dagashi se ita, se kawai yamiqa hannunsa ze kamota, inda nan take hannayensa suka bushe yazamana baya iya sarrafasu, ganin haka tasa wannan sarkin ya roqi sarah akan toyi masa Addu'a hannun nashi sukoma daidai, itako nan take setayi Addu'a, tana yin addu'ar se hannayen nashi suka koma daidai****_
           _Amma dayake dan Adam butulu ne seyasake yunquri a karo nabiyu yasake kai hannu ze kamata nanma dai hannun nashi suka qara maqalewa, seda akayi hakan har sau uku hannayen nashi suna shanyewa***_
              _Ganin wannan al'amarine yasa wannan sarkin ya fusata seya kira shugaban wayannan jami'ai nashi wayanda suke kamo masa mataye, yace dan mene zaka kawo min irin wannan matar???****_
            _Awannan lokaci se wannan sarki ya tsorata qwarai ya razana da Al'amarin Sarah, se yayi mata kyautar wata kuyanga mesuna Hajara, saboda dai yanaso dai a rabu lafiya kada wata matsala ta qara samunshi*****_
            _Bayan Annabi Ibrahim (AS) sun cigaba da tafiya sun isa qasar Falasdin se ita Sarah tabashi kyautar wannan kuyanga wacce wannan mugun sarki yabata kyautarta wato hajara, shikuma Annabi Ibrahim seyayi Sadaka da ita, wanda awannan lokacin har ita Hajara ta dauki ciki, wanda awannan lokacinne sekuma Kishi yakama Sarah, kasantuwar sun kwashe shekaru masu yawa suna tareda Annabi Ibrahim ita bata dauki cikiba****_
_Ana cikin haka sai wannan baiwa Hajara ta haihu wanda aukuwar hakan yasan kishi ya tsananta qwaqarai ta 6angaren uwargida Sarah tana ganin yaza,ayine daga zuwan wannan baiwa se kawai ta haihu alhalin ita e suke tareda Annabi Ibrahim tun suna quruciya amma ita bata haihuba****_
           _Wannan yasa ita Saratu take yiwa Hajara barazanar cewa zata Daddatsa ta kamar Yadda Ibnu Hajar ya Ambata acikin Fathul bari*****_
         _Wannan yasa ita hajara setaji tsoro,seta samu wani zani take daurawa ajikinta wanda shi zanin yanada jela ita kuma jelar zanin tana jan qasa, dan haka yakasance setake tafiya tana bin rerayi duk inda ta taka to wannan jelar zanin nata zeshare sahunta tana yin hakane saboda kada saratu tagane inda take, wato tana 6oyewa kenan, wanda malaman tarihi sukace Itace tafara yin dammara wanda mata sukeyi, wato alokacin wannan 6oye 6oyenda takeyi shine tayi wannan dammarar ajikin zaninta wannan yasa tazama mace tafarko da tafara yin dammara****_
           _To shikuma Annabi Ibrahim sa'adda yaga halinda Ita hajara tashiga ciki shine seya yanke shawarar ya dauketa daga nan wajen yakaita wani waje na daban, to shine sai kuma Allah yayi masa wahayin cewa yakaita can wani kwari, adokar daji wanda babu komai acikinsa face duwatsu da kwazazzabai****_
_To da wannan umarni hakanan Annabi Ibrahin yadaukota itada wannan dan nata Isma'ila wanda awannan lokacin baifi shekaru biyuba a duniya, amma Annabi Ibrahim hakana ya ajjesu awannan kwazazzabo wanda babu shuke shuke acikinsa kamar yadda Allah ta'ala ya labarta mana hakan acan cikin suratul Ibrahim*****_
:
:
Zamu dakata Anan sekuma bayani Nagaba Idan Allah yakaimu
=
=
_Almajirinku dan mutanen kabo_
'
_Jameel Alhassan HarunaY Kabo_
_Alwahhaby-Assalafy_
.
 Nake mana fatan Alheri wassalamu alaikum
..
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-152200029806y7561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka  Wa,atubu ilaika
Share:

Goron sallah daga (kitabu was-sunnah)

*GORON SALLAH???!!!*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
:
Yau 13-10-1438, wacce tayi dai dai da 7-7-2017***
:
Itace ranarda cikin ikon Allah da amincewarsa muke fara gabatarda lekca me taken
.
*GORON SALLAH*
....
....
*ﺇﻥ ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ، ﻧﺤﻤﺪﻩ ﻭﻧﺴﺘﻌﻴﻨﻪ، ﻭﻧﺴﺘﻐﻔﺮﻩ، ﻭﻧﻌﻮﺫ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻣﻦ ﺷﺮﻭﺭ ﺃﻧﻔﺴﻨﺎ، ﻭﺳﻴﺌﺎﺕ ﺃﻋﻤﺎﻟﻨﺎ، ﻣﻦ ﻳﻬﺪﻩ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻼ ﻣﻀﻞ ﻟﻪ، ﻭﻣﻦ ﻳﻀﻠﻞ ﻓﻼ ﻫﺎﺩﻱ ﻟﻪ، ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﻋﺒﺪﻩ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ*
.
_Bayan haka Muna farawa da miqa dubban gaisuwa da dumbin salata marasa adadi, zuwaga uban dakinmu babban jagora Miji awajen zainab kuma baban Zainab, dan gatan Allah shugaban masu kyauta, kuma shugaban manzonni Annabinmu muhammad (s.a.w) Allah ta'ala yayi dadin tsira da daukaka a gareshi****_
                _Bayan haka 'yan uwan wannan wasu 'yan taqaitattun bayanaine muka qunsosu wayanda mukeso mu gabatar dasu gareku matsayin goron sallarmu gareku, dan kuwa yau kwanaki 13 kenan da muka kammala azumin watan ramadan wanda muke fata gamida roqon Allah madaukakin sarki yaji tausanmu ya kar6a mana wayannan ibadu da mukayi****_
              _Muna farawa da neman taimakon Allah madaukakin sarki da yabamu ikon rubuta abinda yake shine dai dai kuma yakauda alqalaminmu akan rubuta kuskure sannan kukuma masu karatu Allah ta'ala yabaku ikon fahimtar wannan bayanai namu a daidai kuma yabamu ikon amfanuwa da wayannan taqaitattun bayanai, dan kuwa zamuy qoqari matuqa wajen taqaitawa dan bamaso wannan lekca ta cika tsawo*****_
            _Amma wannan lekcar zamu dinga kawo wayansu ruwayoyine ta hanyar ishara wayansu kuma tahanyar rubuta fassarar larabcin batareda munkawo nassin bayanin da larabciba duk saboda qoqarnda mukeso muga munyi na taqaitawa*****_
            _Na'am abune wanda zanniya cewa baze yiwuba ace anyi magana akan Ruwan zam zam batareda an ambaci asalinsaba, To amma kasantuwar nafada cewa taqaitawa zamuyi, asali gameda ruwan zam zam yana farowane Lokacinda Annabin Allah Ibrahim yayi hijira daga mahaifarsa wato Qasar Iraqi bayan yasha gwagwarmawa da mahaifinsa da sauran jama'arsa akan suyi imani da Allah daya sesukaqi harma sukayi yunqurin jashe shi, wanda tsanani sadda yakai tsanani shine se Annabi Ibrahim ya dauki matarsa Saratu da Dan dan uwansu wato Annabi ludu yafita dasu akan zasuyi hijira****_
          _To a hanyar tasu sesuka biyo ta qasar masar wacce alokacin akwai wani azzalumin sarki wanda yake baza jakadunsa awannan gari suna tare baqi idan sukaga mutum yana tafe da mace kyakkyawa inhar aka bincika akaji cewa wannan mutuminda yake tareda wannan matar shine mijinta to wannan mugun sarkin ze qwace wannan matar yace shine ya cancanta yazama mijinta ba wannan ba****_
          _To Annabi Ibrahim kuma yasanda wannan batun yasan wannan aika aika ta wannan sarkin na masar mugu azzalumi***_
          _To lokacinda Annabi Ibrahim yashigo masar da matarsa sarah wacce a wannan lokacin ta manyanta wato dattijuwace amma kuma tsabar kyawunta yananan bai gusheba****_
         _Se Annabi Ibrahim yace mata idan aka tambayeki wanene ni?? Kice ni dan uwankine, nima kuma zance ke 'yar uwatace tunda kinga dai mune anan kawai musulmai dan haka ke 'yar uwatace a addini nima kuma dan uwankine a addini*****_
  _To shikuma wannan sarkin qa'idarsa itace in mace tace batada miji wannan da suke tare dan uwantane, to baze kar6etaba ze qyaleta, to awannan lokacinda wannan mamuguncin sarkin yaga tsabar kyawu na Sarah se kawai yakarya wannan qa'idar tasa, ya kar6e saratu a hannun Annabi Ibrahim (AS)******_



Ayi Haquri Zamu dakata anan sekuma bayani nagaba idan Allah yakaimu zamuji yadda takaya tsakanin Wannan Azzalumin sarki da wannan mata Sarah
:
:
_Almajirinku dan mutanen kabo_
'
_Jameel Alhassan HarunaY Kabo_
_Alwahhaby-Assalafy_
.
 Nake mana fatan Alheri wassalamu alaikum
..
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar

http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪy ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka  Wa,atubu ilaika
Share:

Wasu mahimman kalamai da annabi (S A W) ya fada akan mata !!

Wasu Muhimman Kalamai Da Annabi (SAW) Ya Fada A Kan Mata

GARE KU MATA!

🔘Annabi (SAW) Ya ce: " Ita mace ba ta kasancewa mafi kusanci ga mahaliccinta (a wani wuri) fiye da cikin gidanta."

[Silsilatus-sahiha 2688]

🔘 Annabi (SAW) Ya ce: " Duk macen da ta shafa turare, sai ta wuce wasu mutane don su ji kamshin (jikinta) to ita mazinaciya ce."

[Sahihu sunanin Nasa'i 5141]

🔘 Annabi (SA W) Yace: " Duk macen da tasa turare ta fita zuwa Masallaci, baza’a amsa mata Sallar taba har sai tayi wanka."

[Silsilatus sahiha 1031]

🔘Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: " Duk wanda ALLAH ya azurta shi da mace tagari, hakika ALLAH ya taimake sa da rabin addini, sai ya kiyaye dokokin ALLAH wajen samun sauran rabin addininsa."

[Sahihut Targheeb-1916]

🔘Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: " Duk matar da ta tambayi mijinta saki ba tare da wani laifi ba, to haramun ne ta ji kamshin aljanna.”

[Tirmizy 1199, Abu Dawud 2209]

🔘 Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: " kada wata mata ta bayar da izinin (shiga) gidan mijinta, alhali yana nan, sai da yardarsa .”
.
[Muslim 1026]

🔘Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: " Mutane biyu sallar su ba ta wuce kawunan su:

1→ Bawan da ya gujewa mai gidansa har sai ya dawo.

2→Matar da take sabawa mijinta har sai ta daina."

[Sahihut targib 1948]

🔘Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: " Mace ba za ta taba sauke hakkn ALLAH ba har sai ta sauke hakkin mijinta gabaki daya."

[Sahihut targib 1943]

🔘Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: " Da a ce zan umurci wani ya yi wa wani sujjada, to da na umurci mace ta yi wa mijinta sujjada."

[Sahihut targib]

🔘[160] Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: " ALLAH baya kallon matar da bata godewa mijinta, kuma bata wadatuwa da shi."

[Sahihut targib 289]

🔘Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: " Ku saurara, Ashe bana ba ku labarin matan ku ba a cikin aljanna? (sai yace): "Ita ce mai soyayya kuma mai haihuwa. Idan ta yi fushi ko aka saba mata, ko kuma mijinta ya yi fushi sai ta ce masa: wannan shine hannu na a kan hanunka, ba zan kifta ido ba har sai ka yarda."

[Sahihut targib 1941]

🔘Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: " Matar da take kwaikoyon maza ALLAH Ya La'ance ta."

[Ahmad 2/325, Abu dawud 4098-4099]

🔘Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: "Akwai wasu mutane guda 2 jinsin su na 'Yan wuta ne sai dai bai taba ganin su ba ......... Da kuma mata ga sutura a jikin su amma da su da tsiraici daya suke, karkatattu masu karkatarwa, kawunan su kamar tozon rakumi, ba za su shiga aljanna ba ko kamshin aljannar ba za su ji ba, kuma kamshin Aljanna ana samunta daga wuri kaza zuwa wuri kaza."

[Muslim 2128]

🔘[164] Annabi (Sallallahu Alaihi wasallam) Yace: " Duk matar da ta cire suturar ta agidan da ba gidan mijinta ba, ta qeta hijabin da ke tsakaninta da ALLAH mabuwayi mai d'aukaka."

[Imam Ahmad 6/199, 267, Hakeem cikin Mustadaraka 4/288]

🔘Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: " Kuji tsoron duniya sannan kuji tsoron mata, domin farkon fitinar bani Isra'ila ta kasance daga mata ne."

[Muslim 2742]

🔘Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: " Ana auren Mata da abubuwa guda 4: Don dukiyarta, don kyawunta, don nasabarta, don addininta, na hore Ku da Ku auri ma'abociya addini saboda zaku ribantu da ita."
[Muttafaqun Alaihi]

🔘Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: "Mafi alkhayrin jindad'in duniya, shine ka samu Mace Saliha."

[Muslim]

🔘Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: "Idan mace ta sallaci lokaci biyar, ta yi azumin watan Ramadan, kuma ta kiyaye farjinta kuma ta yi biyayya ga mijinta, ta shiga Aljannah."

[Rawahul Bazzar]

🔘Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: "Mace Saliha idan ka yi duba gareta sai ta debe maka kewa idan ka buya gareta sai ta kiyaye kanta."

[Alhadith]

🔘 Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: " Ya taron Mata Ku yawaita sadaka kuma Ku yawaita neman gafara, domin lallai na ga kun fi yawa a cikin wuta" sai wata mace daga cikin su ta ce: Me muka aikata Ya Manzon ALLAH muka zama mafi yawanmu ma'abota wuta? Sai Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: " kuna zagi sannan kuma kuna kafurcewa (butulcewa) Mazajen Ku."
.
[Bukhari]

Daga Faridah Bintu Salis (Bintus-Sunnah)
Share:

Mai sallar qasru zai iyayin sallar shafa'i da wutiri ??

*Assalamu Alaikum*
.
.
*Tambaya ta 2,386*
..
Mai sallar kasaru zai iya yin sallar shafa'i da wutiri...????

……

Amsa



_Eh, ze iyayi, harma da tahiyyatul masjid, dama qiyamun laili da dukkan wata nafila babu lefi dan kawai kanayin qasru babu wanda yace kar kayi nafila****_


.
Allah yasa mudace
.
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
*مجلس التعليم الكتاب والسنة*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook ta wannan hanyar
http://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.
.
Subhanak Allahumma wabi hamdika ash hadu anla ila ha illah anta astagfiruka  Wa,atubu ilaika
Share:

Sanin gaibu 2

*SANIN GAIBU!!!???2*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS  SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Wannan shina bayani nabiyu****
.
.
Cigaba****
.
.
_zuwa yanzu dai kamar yanda bayani yariga yagabata abaya cewa bayaninmu kai tsaye zamuyishine akan gaibu na kaitsaye wato gaibul Mudlaq***_
.
_Ilimin *Gaibu* ilimi ne da Allah ya kebancewa kansa kawai. Kamar yadda ya tabbata acikin Alqur'ani:_
 .
_ﻗُﻞْ ﻟَﺎ ﻳَﻌْﻠَﻢُ ﻣَﻦْ ﻓِﻲ ﺍﻟﺴَّﻤَﺎﻭَﺍﺕِ ﻭَﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ ﺍﻟْﻐَﻴْﺐَ ﺇِﻟَّﺎ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻭَﻣَﺎ ﻳَﺸْﻌُﺮُﻭﻥَ ﺃَﻳَّﺎﻥَ ﻳُﺒْﻌَﺜُﻮﻥَ_
_*‏(ﺍﻟﻨﻤﻞ  65)*_
.
_Kace, "Bãbu WANDA yasan gaibi a cikin sammai da kasa fãce Allah. Kuma bã su sanin a yaushe ne ake tayar da su"_
_*(Namli  65)*_
.
Allah madaukakin sarki ya sake cewa:
.
ﻭَﻋِﻨْﺪَﻩُ ﻣَﻔَﺎﺗِﺢُ ﺍﻟْﻐَﻴْﺐِ ﻟَﺎ ﻳَﻌْﻠَﻤُﻬَﺎ ﺇِﻟَّﺎ ﻫُﻮَ ﻭَﻳَﻌْﻠَﻢُ ﻣَﺎ ﻓِﻲ ﺍﻟْﺒَﺮِّ ﻭَﺍﻟْﺒَﺤْﺮِ ﻭَﻣَﺎ ﺗَﺴْﻘُﻂُ ﻣِﻦْ ﻭَﺭَﻗَﺔٍ ﺇِﻟَّﺎ ﻳَﻌْﻠَﻤُﻬَﺎ ﻭَﻟَﺎ ﺣَﺒَّﺔٍ ﻓِﻲ ﻇُﻠُﻤَﺎﺕِ ﺍﻟْﺄَﺭْﺽِ ﻭَﻟَﺎ ﺭَﻃْﺐٍ ﻭَﻟَﺎ ﻳَﺎﺑِﺲٍ ﺇِﻟَّﺎ ﻓِﻲ ﻛِﺘَﺎﺏٍ ﻣُﺒِﻴﻦ.
_*‏(ﺍﻷﻧﻌﺎم  59)*_
.
_Kuma A wurinSa mabūdan gaibi suke babu Wanda yake saninsu fãce shi, kuma yanã sanin abinda ke a cikin tudu da ruwa, kuma wani ganyē bãya fãduwa, fãce ya sanshi, kuma bãbu wata kwãya acikin duffan kasa, kuma bãbu danye, kuma bãbu kēkasasshe, fãce yanã a cikin Littãfi mai bayyanãwa._
_*(An'ãm, 59)*_
.
.
*Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam)* ya bayyana wadannan mabudan a matsayin ababe guda biyar da aka ambata acikin _*Suratul Luqmaan*_ inda Allah madaukakin sarki yace:
.
ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻋِﻨْﺪَﻩُ ﻋِﻠْﻢُ ﺍﻟﺴَّﺎﻋَﺔِ ﻭَﻳُﻨَﺰِّﻝُ ﺍﻟْﻐَﻴْﺚَ ﻭَﻳَﻌْﻠَﻢُ ﻣَﺎ ﻓِﻲ ﺍﻟْﺄَﺭْﺣَﺎﻡِ ﻭَﻣَﺎ ﺗَﺪْﺭِﻱ ﻧَﻔْﺲٌ ﻣَﺎﺫَﺍ ﺗَﻜْﺴِﺐُ ﻏَﺪًﺍ ﻭَﻣَﺎ ﺗَﺪْﺭِﻱ ﻧَﻔْﺲٌ ﺑِﺄَﻱِّ ﺃَﺭْﺽٍ ﺗَﻤُﻮﺕُ ﺇِﻥَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻋَﻠِﻴﻢٌ ﺧَﺒِﻴﺮٌ.
_*(لقمان،  34)*_
.
_Lalle ne, Allah a wurinsa kawai sanin sa'a yake, kuma yanaã saukar da girgije, kuma yanã sanin abinda take cikin mahaifannai, kuma wani rai baisan abinda yake aikatatawa a gobe ba, kuma wani rai baisan a wace kasa yake mutuwa ba. Lalle Allah Masani ne, Mai kididdigewa._
_*(Luqmaan, 34)*_
.
.
_*Bukhari* ya ruwaito acikin littafinsa na Sahih a hadisi mai *adam 4477,* cewa *Aisha (radiyallahu Anna)* tace: Duk Wanda yace muku yasan Gaibu karya yake yi._ Sai ta karanta wannan ayar
.
ﻭَﻣَﺎ ﺗَﺪْﺭِﻱ ﻧَﻔْﺲٌ ﻣَﺎﺫَﺍ ﺗَﻜْﺴِﺐُ ﻏَﺪًﺍ.
.
_Kuma wani rai bai san abinda yake aikatawa gobe ba._
.
.
Kalmar *Gaibu* tana nufin boyayyen abu.
.
Akwai ababen da Allah ya boye wadanda babu mai iyasaninsu acikin halittun Allah acikin sammai ko a kasa. Wannan shine Gaibu da Allah ya kebance kansa dashi shine ake kira *Al-Gaibu Mutlaq).* Allah yana cewa :
.
ﻋَﺎﻟِﻢُ ﺍﻟْﻐَﻴْﺐِ ﻓَﻼ ﻳُﻈْﻬِﺮُ ﻋَﻠَﻰ ﻏَﻴْﺒِﻪِ ﺃَﺣَﺪﺍً.
_*(ﺍﻟﺠﻦ  26)*_
.
_Shi kadai ne masanin gaibi, saboda haka, baya bayyana gaibinsa ga kowa._
_*(Aljinni, 26)*_
.
.
_kenan idan muka lura zamusan cewa Akwai Gaibu na ilimantar wani abu cikin halittunsa, ya kuma boyu ga wasu halittunsa. Wannan yazama Gaibu ga wadanda suka jahilce shi, Kuma ba Gaibu ne ba ga wadanda suka samu ilimi akansa kenan yazama gaibul mudlaq wato na kaitsaye, dakuma gaibul muqayyad wanda yakeda togacciya***_
.
_Mai Neman Karin bayani yana iya duba:DARASI
_*Sharh al-‘Aqeedah al-Waasitiyyah (shafi na 158)*_
.
.
_Kenan wannan karatun xamu fahimci cewa babu yanda za,ayi wani ayau yace maka wai kaje wajenshi wai zaimaka istikhara, duk wanda kaji yace zaimaka istikhara toh karya yakeyi, sannan kuma babu abinda ake gani dan anyi istikhara, saidai kaba Allah zabine kawai gameda abinda kayi istikharan saboda shi, amma bawai kawai anyi maka sata ba ko wani abu sai ace kaje wani yaimaka istikhara wai zega barawon, toh karyane duk wanda kaji yace haka toh makaryacine kuma bokane yanaso yarabaka da addinij Annabi muhammad (s.a.w)***_
.
_Kowa shi yake yima kanshi istikhara amma wai saboda zaka fara wata sana,a sai wani zindiki yace wai kazo zeyi maka istikhara toh wannan dan dubane boka ne munafikin Allah ta,ala****_
.
.
Zamu dakata anan, abinda mukayi daidai Allah yabamu ladanshi kuskure kuma Allah ya yafe mana****
.
.
📝✍🏿
```Jameel A Haruna Kabo```
(Abu khausar)
.
Tareda
```Sani Iliyass Yakasai```
(Dan mama)
.
Suke muku fatan Alheri
..
.
Allah yasa mudace
.
.
Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like
https://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
Share:

Sanin gaibu

*SANIN GAIBU!!!???*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS  SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Yau 22-01-1438
24-11-2016, itace ranarda muke gabatar muku da wannan jawabi na musamman wanda mukaimasa takeda *SANIN GAIBU!!!???*
.
.
_Muna farawada mika gidiyar musaman ga Allah muna neman taimakonshi da agajinshi, wanda Allah ya shiryar shine cikakken shiryayye wanda ya bata kuma babu me iya shiryar dashi***_
...
_bayan haka wannan takaitaccen bayani isharace kawai zamuyi gameda korafe korafe da muke yawan samu gameda shin Annabi muhammad (s.a.w) yasan gaibu kokuwa bai saniba***_
.
_Hakika mafi alherin shiriya itace shiriyar Annabi muhammad (s.a.w), amma duk wata shari,a wacce batashiba toh shiriritace kuma bata ce***_
.
_Malamai sukan raba gaibu zuwa kashi biyu, akwai gaibu wanda suke kiranshi mudlaq, wato gaibu na kaitsaye, sannan kuma akwai gaibu Muqayyad wato gaibu me togacciya****_
.
_zamu fara bayani gameda gaibu nabiyu wato muqayyad, shine wabda yakeda togacciya***_
.
_Gaibu me togacciya shine abinda wasu mutane suka sani amma wasu basu saniba, toh awajen wayanda sukasan wannan abin toh ba gaibu bane, amma dai wayanda basu saniba toh sukuma gaibune awajensu***_
.
_Misali, Annabi muhammad kafin yazama Annabi baisan cewa shi Annabi bane, kuma gashi yana raye aduniya, toh kunga awannan lokacin kakaf jama,arda suke tare dashi basusan cewa shi Annabi bane, amma ai Allah yasani, toh wannan saninda Allah yayi shine gaibu na kaitsaye, toh amma sanda Annabi muhammad yabayyana kanshi amatsayin Annabin Allah toh wannan gaibun awannan lokacib yatashi daga gaibu na kaitsaye yakoma gaibu me togacciya, wato yazama muqayyad ba mudlaq ba***_
..
_Abinda yasa yakoma gaibu mukayyad shine  saboda yanzu Ai duk sahabbai da sauran jama,a da shi kanshi Annabi muhammad duk sunsan Cewa shi Annabin Allah ne, toh kunga aidama abinda bakasanshiba baka yayakeba shine gaibu, toh daga lokacinda kasanshi yananan amatsayinshi na gaibun awajen wasu wayanda basu saniba, toh amma kai yanzu tunda kasan abin toh ba gaibu bane awajenka****_
.
_Atakaice dai, duk abinda yazama wani sashen mutane ne suka sanshi, amma wasu basu saniba, toh wannan shine gaibunda yakeda togacciya***_
 .
_Macce ce takeda ciki, ga dai cikin ajikinta amma kuma saikaga bata saniba shin namjine aciki ko mace ne?? Kuma batasan hakikanin ranarda zata haihuba, toh wannan rashin sanin da batayiba toh yasa wannan cikinda yake jikinta yazama gaibu awajenta***amma duk ranarda ta haihu taga jaririn ahannunta karara toh shikenan gaibun yabayyana yanzu baza,a sake kiranshi gaibi ba***_
.
_Ga wani karin misali karara, tunda akan internet muke muna chat, idan kana charting da wani, zakaga ansamaka alama wacce take nuna gashinan yana rubuta sako zai turo maka, toh amma kai dai annuna maka yana typing, amma bakasan hakikanin me yake rubutawaba amma shi yasan abinda yake rubutawa, shin zagi yake rubutawa? Meyake rubutawa baka saniba ammadai tabbas kaga alamar yana rubutu, toh wannan rashin saninda bakayiba yasa wannan abin yazama gaibu awajenka, amma dazarar yaturo maka kagani shikenan wannan abin yatashi daga gaibu kuma yazama ba gaibu ba***_
.
_Toh hakanan shima Annabi muhammad (s.a.w) yasan gaibu amma me togacciya, saboda asali baisan abinba sai sanda akayi masa wahayi aka sanar dashi***_
.
_Asali Annabi muhammad baisan duk wayannan ayoyinda suke cikin qur,aniba amma ta hanyar wahayi ake masa, seyazama duk duniya babu wanda yasan wannan abin saishi, toh wannan saninda yayi amma sauran jama,a basu saniba toh yasa wannan abin yazama gaibu amma me togacciya wato muqayyad***_
.
_Toh dazarar wahayi ya sauka sai Annabi ya sanarda sahabbai toh suma yanzu yazama ba gaibu ba awajensu***_
.
_Da wannan bayanin shine yake nuna mana cewa eh lallai tabbas Annabi muhammad babu shakka yasan wani bangare na gaibu, wato wannan gaibun wanda mukai muku bayani akansa shine wanda Annabi muhammad yasani, amma akwai gaibu na kai tsaye kamar ace yaushene tashin kiyama?? Ko kace yaya hakikanin mala,ika yake, toh kaga mun tabbatar za,ayi tashin kiyama kuma mun tabbatar akwai mala,iku amma bamusan hakikaninsuba saboda gaibune na kai tsaye wanda Allah shine kadai yasani***_
.
_In kuka biyomu abayani nabiyu zamu gabatarda ayoyi da hadisai wayanda karara suka tabbatarda cewa Lallai akwai gaibu na kaitsaye wanda Annabi muhammadu bai sanshiba****
.
.
.
Allah yasa mudace
.
.
Domin samun shafinmu a Facebook sekushiga nan kuyi like
https://m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
Share:

Madigo da luwadi

*MADIGO DA LUWADI 2*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
16-10-2015
.
.
Cigaban lekca metaken
.
*MADIGO DA LUWADI 2*
.
.
_wannan shine cigaba kuma bayani nakarshe akan muni da ba,ala,Inda madigo da luwadi suke haifarwa_
.
.
_Annabi S.A.W yace: Tsinannene Wanda yake saduwa da mace tana haila kuma tsinannene Wanda yake saduwa da mace ta dubura, Wannan hadisine ingantacce Abu dawuda da turmizi da ibn majah suka ruwaitoshi_
.
_Albani ya ingantashi cikin Irwa,ul galil hadisina 2006_
.
.
_Sedai nasan dayawan mutane basusan abunda tsinuwar Allah take nufiba kubiyomu asannu zakuji ta,arifin Kalmar tsinuwa, wato hakikanin ma,anarta_
.
_Awani  hadisin Annabi na cewa:_  *DUK WANDA YASADU DAME HAILA  KO WANDA YASADU DA MACE TA DUBURA KO  WANDA YAJE WAJEN BOKA TOH TABBAS YAKAFIRCEMA ABUNDA AKA SAUKARWA ANNABI MUHAMMAD S.A.W*
.
_Abdullahi Dan Abbas yace: Idan aka kama Yar madigo ko Dan luwadi toh asamu gininda yafi kowanne girma da tsawo agarin ahau saman aratayeshi sannan abishi da ruwan duwatsu kamar yanda Aka aikatawa mutanen Annabi lud**_
.
.
_Abunda tsinuwar Allah take nufi shine_
.
*ALLAH YASA KAYI RIDDA KABAR MUSLINCI KUMA KAMUTU KANA KAFIRI KASHIGA WUTA KA DAWWAMA ACIKINTA DUK WANI SAUKI KO RAHAMAR ALLAH KADA ALLAH YASA KASAMETA BALA,I YAITA NINNINKUWA AKANKA DA AZABA HAR ABADA*
.
_wannan shine ma,anar Allah yatsinema wane_
.
_Duk Wanda kaji yace Allah yatsinemaka toh kaji abunda yake nufi yasameka_
.
_Toh inakuma ace Annabi muhammadu yatsine maka???_
 .
.
_Yaku yan,uwa hakika mutuba mubar wannan mummunan aikin na madigo da luwadi_
.
_Hanyoyin tuba sunada yawa kuma insha,allahu zamu kawo wasu DAGA ciki yanzu_
.
_Kokuma aduba RIYADUS SALIHIN_
.
_Wanda yakeso yaga cikakken bayani gameda sharri da bala,in tsinuwa seya nemi littafi mesuna
HUKUMU ADDU'A'U BIL LA,AN_
.
_wallafar Malam Bashir Nuhu Assalafy_
Da
_Mallam Yahaya muhammad Assalafy Kaduna_
.
_Hakika littafin yanada fa,ida sosai_
.
.
_Daga cikin hanyoyin tuba akwai nisantar wannan mummunan aikin kuma abarshi don Allah Badon waniba ko saboda wata gazawa_
.
_Sannan kuma akudurce cewa baza,a sake komawa kan wannan zunubinba kuma ayi nadamar abunda yawuce ayita istigfari adunga fatar rahamar Allah_
_Ayawaita ibada ayita nafilfilu ana tuba ana sadaka dasauran ayyukan alkhairi kuma anemi ilimi adage ayi aiki dashi saboda aikin addini baya karbuwa sefa anyishi da ilimi kuma yanda annabi yakoyar_
.
_Allah ya tabbatarda duga diganmu akan tafarki irinna Annabi da sahabbai_
.
.
Allah Ta,ala yatsaremu
.
.
```Jameel Alhassan Haruna Kabo```
_(Abu khausar)_
.
Tareda
.
_Ameenatu M. Reemy_
.
_Sune suka tattara wayannan  bayanai, kuma suka rubutashi a shekara ta 2015_
.
_muna rokon Allah ya shiryar damu yasa karshenmu yayi kyau ameen***_
.


.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
https:/t/m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka  Wanatubu ilaika
Share:

Madigo da luwadi

*MADIGO DA LUWADI*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
*LECTURE METAKEN*
*MADIGO DA LUWADI 1*
.
15-10-2015
.
_Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh_
.
_Topic of discussion dinmu yau in sha Allahu ta'ala shine babban annobar data kunno kai a wannan zamani wato "homosexuality and lesbianism" Duk da dai cewar ba baqon abu bane amma sai dai muji labarinsa a wasu qasashe can yau da gobe munaji sai a abun ya shigo mana Kafin muyi nisa cikin darasin zanso musan ma'anar homosexuality and lesbianism in brief suna nufin saduwar jinsi_
.
_Homosexuality shine saduwar namiji danamiji lesbianism shine saduwan mace da Mace: Wal'iyazubillah!!! ALLAH YA TSAREMU DA ZURIA BAKI DAYA AMEEN_
.
_Ammadai Yar,uwa inaso kisani shifa madigo ko luwadi babban zunubine sosai amusulinci Wanda zamu iya cewa idan aka cire shirka da kafirci toh yana iya biyo baya_
.
_Sannan kuma hukuncin wannan mummunan aikin wato madigo da luwadi yana kusan daidaine da hukuncin mutuminda yazagi manzon Allah_
.
.
_Kamar yanda mukasani shi Wanda yazagi annabi koda yatuba dolene bamakawa sai ankasheshi_
.
_Toh shima Dan luwadi da Yar madigo muddin yabari aka kamashi tabbas koda yace yatuba sefa anyimai hukuncin kuma zamuyi bayanin yanda ake hukunta masu wannan aikin insha,allahu_
.
.
_MANZON ALLAH SAW YACE:_
.
_MAFI GIRMAN ABUNDA NAKEJIN TSORONSHI AKAN AL,UMMATA SHINE AIKIN MUTANEN ANNABI LUD sahehu ibn majah 2077_
.
.
_Menene aikin mutanen annabi lud?_
.
_Shine dai madigo da luwadi_
.
_Allah yatsaremu_
.
_Awani hadisi so uku ajere manzon Allah yana tsinema Wanda yake aikata irin aikin mutanen Annabi lud_
.
_Manzon Allah (S.A.W) yace: ALLAH YATSINEMA WANDA YAKE AIKATA IRIN AIKIN MUTANEN ANNABI LUD, ALLAH YATSINEMA WANDA YAKE AIKATA IRIN AIKIN MUTANEN ANNABI LUD, ALLAH YATSINEMA WANDA  YAKE AIKATA IRIN AIKIN MUTANEN ANNABI LUD Aduba musnad na imam Ahmad mujalladi na daya hadisina 309 Imam Hakim annaisaburi yafitarda hadisin cikin mujalladi na Hudu hadisina 356_
.
_Imamul baihaki mujalladi na takwas hadisi 23_
.
_Kuma Ahmad shakir yace hadisine sahehi_
.
_Allah madaukakin sarki yatsaremu_
.
_Har ila yau manzon Allah yace:_
.
.
_DUK WAYANDA KUKA SAMESU SUNA AIKATA IRIN AIKIN MUTANEN LUD TOH KUKASHE MEYI DAKUMA WANDA AKEYI DASHI Ahmad shakir da muhammad nasiruden albani sun inganta wannan hadisin_
.
_Awani wajen kuma manzon Allah cewa yayi: ALLAH BAYA KALLON NAMIJINDA YAKE SADUWA DA NAMIJI KOKUMA MIJINDA YAKE SADUWA DA MACE TA DUBURA_
.
.
_Allah yatsaremu_
.
_Wato yan,uwa hadisai sunada yawa inada aketayin mummunan tanadi na bala,I da musiba ga wayanda suke aikata madigo da liwadi_
.
_Sedai acikin hadisan anasamun masu rauni dama hadisan karya_
.
.
_Amma dai koba komai ai asara da tabewa tagama tabbata akan mutuminda manzon Allah yajeramai tsinuwa harguda uku akanshi_
.
_Allah yatsaremu_
.
_Awani hadisi akace: DUK WANDA YAKEYIN LUWADI IDAN YAMUTU KO TAMUTU BATAREDA YA TUBABA TOH ACIKIN KABARINSHI ZA,A CHANJA SURARSHI IZUWA KAMANNIN ALADE_
.
_Sedai Allam ibnul jauzy yace wannan hadisin karyane betabbataba Daga manzon Allah SAW Yafitardashi acikin littafinsa mesuna AL MAUDU,AT mujalladi na uku hadisina 113_
.
_Ammadai yan,uwa koda wannan hadisin be ingantaba ammadai tabbas akwai abun firgici acikinshi kuma lallai yakamata muji tsoton Allah mukiyaye_
.
_Shekhul Islam Ibn Taimiya yace:_
.
_Sahabbai basuyi sabaniba akan cewa duk Inda akasamu meyin luwadi ko madigo toh kasheshi za,ayi walau shine yake yi kokuma akanshi akeyi sedai sunyi sabani akan irin kisanda za,ayi_
.
_Wasu sukace jefeshi da duwatsu za,ayi_
.
_Wasu sukace  Aa sama za,ahau dashi aratayeshi awajenda yafi ko ina tsawo agarin_
.
_Wasu sukace konashi za,ayi dawuta_
.
.
_Dan,uwa yanzu cikin ukunnan duk Wanda akayi wannene mesauki aciki??_
.
.
_Allah dai yatsaremu_
.
_Bari kuji irin taka tsantsan na magabata akan tsoronda sukeji akan madigo da luwadi_
.
_Watarana Safiyanu Sauri yashiga ban daki Sega wani yaro me kyawun fuska yashigomai_
.
_Safiyanu yace kuyi maza kufitarmin dashi dominkuwa Ni safiyanu inaganin atareda kowacce mace akwai shedan guda daya amma inaganin atareda duk wani yaro mekyau akwai  samada guda goma_
.
.
_Allah sarki kunji bayanin bayin Allah masu kaifin hankali_
.
_Amma Mu yanzu mukanmu munema shedanun_
.
_Allah madaukakin sarki yashiryamu_
.
.
_Bari muji wannan kissar_
.
.
_Daga Khalid bin Walid bin mugira Yarubuta takarda zuwaga sayyadina Abubakar  cewa yakama wani dan luwadi_
.
_Se Abubakar yanemi shawarar sahabbai akan Al,amarin Sayyadina Aliyu yace wannan babban zunubine Wanda kakaf duniya babu Wanda sukeyin irinshi face Al,umma guda daya tal sune mutanen Annabi lud kuma munsan irin hukuncinda Allah yayi musu  don haka ra,ayina shine akonashi da wuta se Abubakar yarubutama Khalid cewa yakonashi dawuta aikuwa take Khalid yasa aka hada wuta yakonashi_
.
_Aduba Attargib wat tarhib, mujalladi na uku shafina 289_
.
.
.
Allah yashiryar damu hanya madaidaiciya
.
.
Allah yatabbatarda duga diganmu akan tafarki irinna annabi da sahhabbai
.
.
```Jameel Alhassan Haruna Kabo```
_(Abu Khausar)_
.
Tareda
.
_Ameenatu M. Reemy_
.
Suka rubuta kuma suke mana fatan alheri semun hadu a bayani nagaba
.
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
https:/t/m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka  Wanatubu ilaika
Share:

Friday, 7 July 2017

Shekaru 500 yana bautar Allah

SHEKARU 500 YANA BAUTAR ALLAH
***************************************
Mala'ika Jibreelu (as) ya bama Manzon Allah (saww) labarin wani mutum daga cikin al'ummomin da suka gabata, wanda ya bauta ma Allah tsawon shekaru dari biyar (500).
Mutumin ya gida bukkarsa wacce yake ibada acikinta bisa kan Kololuwar wani dutse atsakiyar teku mai ruwan gishiri, Amma saboda ibadarsa sai Allah ya sanya wani kogin farin ruwa mai dadi yana bulbulowa daga kan dutsen domin wannan bawan Allahn yasha yayi alwala.
Sannan Allah ya sanya wata bishiyar Teen (wani abu ne mai kamar baure) ta tsiro akan dutsen. kullum wannan bawan Allahn yakan tsinki 'Dan itacen guda 'daya yaci.
Wannan Bawan Allahn yayi wata addu'a yana cewa "YA ALLAH KAR KA DAUKI RAINA, FACHE INA CIKIN SUJJADA".
Allah ya amshi Addu'arsa, ya rasu acikin sujjadah saboda haka duk lokacin da Mala'ika Jibreelu zai sauko Qasa sai ya tarar dashi kamar yana cikin Sallah.
Mala'ika Jibreelu (as) yace aranar ALKIYAMA Allah zai ce ma MALA'IKU "KU DAUKI BAWAN NAN NAWA KU KAISHI ALJANNAH SABODA RAHAMA TA".
Shi kuma wannan mutumin zai ce Shi dai yafi son ashigar dashi Aljannah saboda ladan ibadarsa.
Allah zai cewa Mala'ikunsa su auna ladan ibadar wannan mutumin da kuma ni'imar da Allah yayi masa ta tsawon wannan lokacin. da aka auna sai aka ga cewa ladan ibadar shekaru 500 din nan bai kai nauyin Ni'imar idanun da aka bashi ba ma.
Don haka za'a ce ma Mala'iku su wuce su kaishi wuta. sai mutumin nan ya firgita yace "To Ya Allah ka shigar dani Aljannah saboda rahamarka!!"
To anan ne zasuyi zance da Allah kamar haka :
Allah zai tambayeshi : "YA KAI BAWANA, WAYE YA HALICCEKA?"
Shi kuma zai ce "Ya Ubangiji kai ne ka halicceni".
Sai Allah yace masa "SHIN NA HALICCEKA NE SABODA WATA IBADAR DA KA TABA YIMIN, KO KUMA SABODA RAHAMATA NA YIKA?".
Sai yace ''Ya Ubangiji saboda rahamarka kayi ni".
Sai Allah yace masa "TO WAYE YA RAYAKA TSAWON SHEKARU 500 KANA IBADA ADUNIYA?"
Zai ce "Ya Allah kai ne ka rayani ka bani wannan damar".
Allah zai sake tambayarsa : "SHIN WAYE YA SANYAKA BISA KAN DUTSE ATSAKIYAR TEKU, KUMA YA SANYA RUWA MAI DADI YA BULBULO DAGA CIKIN RUWAN GISHIRI, SANNAN YA SANYA BISHIYA TA TSIRO DOMINKA? KUMA WAYE YA BAKA DAMAR RASUWA ALOKACIN DA KAKE CIKIN SUJJADA?"
Sai mutumin yace : "Ya Ubangijin Talikai! Kai ne duk kayi mun wannan".
Sai Ubangiji yace masa "DUK WANNAN YA FARU NE CIKIN RAHAMATA. KUMA KAI MA ZAKA SHIGA ALJANNAH NE DA RAHAMATA".
– ZAUREN FIQHU - Ya Allah ka sanyamu cikin ALJANNATUL FIRDAUSI don falalarka da rahamarka. ba don ibadarmu ko wani abu daga garemu ba.
Daga littafin Tanbeehul Ghafileen na Abul Layth As-Sarmaqandiy (rah).
DAGA ZAUREN FIQHU
Share:

Yadda zaki tsare kanki daga sharrin miyagun samari

YADDA ZAKI TSARE KANKI DAGA SHARRIN MIYAGUN SAMARI :
TAMBAYA TA 2242
*******************
Assalamu alaikumun
Allah ya taimaki Malam, yasa ka cika dakyau da imani tare da sauran al'umman Muslimai (amin)
Malam shawara nake nema da addu'a. Na kasance a duk lokacin da nayi Saurayi bai da buri illah ya nema ya taba ni ko son yayi lalata dani, kuma basu maganar aure, sai da-daya daga cikin su. Hakan na mutakar damuna, Kasancewa ni macece da bana bayyana ado na, ina kuma kokarin gani na kare mutuncin kaina.
Daga Dalibarka mai bin Shafin Zauren fiqhu.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Hakika kowanne mutum Mumini akwai irin musibar da Allah yake jarrabarsa da ita domin ta zama jarrabawa ga imaninsa.
Ki dauki irin wannan abinda ke faruwa dake din amatsayin jarrabawa ne daga Allah. Kuma hanyar cin jarrabawar ita ce :
- Jin tsoron Allah fiye da komai.
- Dukufa wajen yin addu'ar neman kariya daga Allah bisa rayuwarki baki daya.
- Kiyaye Mutuncin kanki da Iyayenki da danginki.
- Kokarin rabuwa da saurayi da zarar kin gane manufarsa.
- Kiyi kokari ki fidda saurayi guda Mai alamar tsoron Allah da riko da addini.
- Bayan kin tsaida saurayi guda to karki sake amincewa da kowa.
- Kada ki yarda ki kadaita da saurayi koda kuwa ya kai miki sadaki. Wajibi ne ki nemi wata Qawarki, ko Qanwarki ko wani Qaninki mai wayo ya kasance tare daku.
- Duk hirar da zakuyi kar ku wuce kofar gidanku. Kar ki yarda kije dakin saurayi.
- Duk saurayin da zai zo wajenki, to ki gaya masa yazo miki da rana. Ki dena hira dasu da dare.
Kada ki bama saurayi damar ta'ba jikinki koda ya biya sadakinki ai ba'a daura aurenku ba tukunna. Don haka baki halatta gareshi ba.
Komai kyawun saurayi komai kudinsa, kada kici gaba da alaqah dashi mutukar kin fahimci cewa yazo da Mummunar mafuka.
Idan kika rabu dashi domin Allah, to Allah din zai hadaki da wani wanda yafishi alkhairi in sha Allah.
Allah yana cewa :
"DUK WANDA YAJI TSORON ALLAH, TO ALLAH DIN ZAI SANYA MASA MAFITA. KUMA ZAI AZURTASHI TA INDA BA YA TSAMMANI... ".
Allah yace :
"LALLAI ZA'A JARRABEKU ACIKIN DUKIYOYINKU DA KUMA KAYUWANKU..".
Kuma Allah yace :
"KADA KUBIBBIYI HANYAR SHAITAN. HAKIKA SHI MAKIYINKU NE MAI BAYYANAR DA QIYAYYA.
"KA'DAI SHI YANA UMURTARKU NE DA MIYAGUN AYYUKA DA ALFASHA...".
Mazinatan Samari Wakilan shaitan ne. Kuma suna kiranki ne zuwa ga alfasha da kuma Wutar Jahannama. Don haka Kiji tsoron Allah kada garin jin dadin Minti biyar ki janyo ma kanki Azabar sama da shekaru dubu biyar. (Allah shi kiyayemu).
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU
Share:

Abubuwa 3 suna warware chutuka 3

ABUBUWA UKU SUNA WARWARE CHUTUKA GUDA UKU :
1. ABU NA FARKO : Idan kaji an jarrabeka da tsananin sha'awa Mai Qarfi wacce take rinjayarka wajen tunanin aikata alfasha, to ga Maganinsa nan :
Yi kokari ka gyara sallolinka. Watakil ba ka yinsu akan lokaci, ko kuma baka yinsu bisa tsoron Allah.
Domin kuwa Allah yana cewa : "SAI WASU MABIYA SUKA MAYE GURBINSU ABAYANSU, WADANDA SUKE TOZARTAR DA SALLAH KUMA SUKA BI SHA'AWOYI. DA SANNU ZASU HADU DA AZABAR GAYYU (WANI RAMI NE ACIKIN JAHANNAMA).
2. NA BIYU : Idan ka fara samun tsiyacewa da kuma rashin dacewa acikin lamarinka, to lallai kaje ka gyara tsakaninka da Mahaifiyarka. Watakil akwai mushkila atsakaninku.
DALILI : Allah ya bamu labarin Annabi Eisa (as) yana cewa : "(ALLAH YA SANYANI) MAI BIYAYYA GA MAHAFIYATA, BAI SANYANI AZZALUMI MATSIYACI BA".
3. NA UKU : idan ka fara jin Qunci azuciyarka da lalaci wajen yin ibadah. To ka binciki kanka dangane da Zikirin Allah da Karatun Alqur'ani.
DALILI : Allah yana cewa : "DUK WANDA YA JUYA BAYA DAGA AMBATONA, TO HAKIKA ZAI SAMU RAYUWA MAI QUNCI, KUMA ZAMU TASHESHI MAKAHO ARANAR ALQIYAMAH".
ABIN LURA :
Wulakanta Sallah shi ke sanya shagaltuwa da sha'awa, Zina, Madigo, Luwadi, etc.
Rashin bin iyaye shi ke janyo Dagulewar harkoki da kuma Toshewar albarkar rayuwa.
- Qarancin Zikirin Allah shi ke kawo Quncin Zuciya, Quncin rayuwa, da kuma tsirowar Munafurci azuciya.
Ya Allah ka kiyayemu ka kiyaye mana imaninmu, Aameen. Ka Qara mana Son Annabinka (saww) da Qanqame ma Alqur'ani da Sunnarsa da Son bayin Allah na kwarai. Ameen.
DAGA ZAUREN FIQHU
Share:

Hanyoyin da zakabi ka daina zina

HANYOYIN DA ZAKA BI KA DENA ZINA,
TAMBAYA TA 2244
*******************
Salaam Alaikum Mallam Ina maka fatan Alkairi, wannan taimako da kakeyi Allah ya saka maka da gidan Aljanna ameen.
Dan Allah mallam a amsa min wanan wasika. Ina cikin wata damuwa wacce na rasa yadda zanyi ina bukatar taimako na addua da kuma shawara.
Mallam nidai mutum ne makarancin Qur'ani, bana wasa da Azkar, bana wasa da sallah ko kuma Lokacin, mahaifina kuma mutum ne mai illimin addini, ya bani tarbiyya iya karfin sa.
Nidai tun Ina yaro karami Allah ya jarrabe ni da matsananciyar sha'wa Wanda kuma har yanxu na kai shekara 27 amma ban taba cin wanan jarrabawa ba harsai da takai ni ga aikata zina. Duk lokacin da nayi zina Bayan na gama sai naji duk Raina ya baci kuma nayita dana sani Ina nadamar mai yasa nayi zina.
Zan duba na roki Allah ya yafe min amma bayan wani lokaci kuma zan sake aikatawa. Wallah har cikin zuciya inaso na dena aikata wanan sabo amma na rasa yadda zanyi, babu kuma Wanda yasan Ina ina aikata zina kuma ba Wanda ya taba gani na, hatta Wanda muke kwana daki daya bai san ina aikata zina ba sai Allah shikadai ya sani.
Shekaran jiya na aikata wanan alfasha tare da wata mace Bayan mun gama sai bacci ya daukeni. A wanan baccin se nayi mafarkin gani a maqabarta ana tona wani kabari kuma a cikin kabari se aka tono wani wani gabadaya jikin sa gashi. Wanan mafarki ya razana ni kwarai kuma naji a azuciyata lallai na tuba zuwa ga Allah. Mallam a temake ni da addua wacce indai rike ta toh inshallahu zan dena aikata wanan sabo.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!!!
Hakika Ka afka cikin zinubi mafi hallakarwa wanda in banda Shirka babu barnar da ta fishi girma awajen Allah. Kuma Zunubin da Bala'insa ba zai tsaya akanka kai ka'dai ba. Sai ya Kwarara har cikin danginka da dangin ita abokiyar zinar taka!! SUBHANALLAH!!.
Ka biye ma son rai da Kuma sha'awar banza waccs Shaitan (L. A) ya hura maka azuciya, Ka kauce ma hanyar Allah da gangan. Domin kai kanka amatsayinka na Makarancin Alqur'ani ka riga kasan Haramcin Zina da kuma yadda take nisanta tsakanin Mutum da Allah.
Kaci amanar Mahaifinka bisa kyakkyawar tarbiyyar da ya baka, ka gurbata kanka, kuma watakil ka janyo gurbacewar wasu daga cikin zuriyar gidanku. (Allah shi kiyayemu).
Babban Magani anan shine TSORON ALLAH DA KUMA TUNANIN RANAR GAMUWARKA DASHI.
Sannan ka gaggauta tuba da neman gafarar Allah. Ina nufin cikakkiyar tuba. Ba wai irin tuban Mayaudara ba. Ka tuba ka nisanci wannan mummunan aikin. Kuma ka nisanci wacce kukeyi da ita.
In da hali ma ka chanza wajen zama. Yadda zaku dena haduwa da waccan Mazinaciyar.
Ka sake duba sallolinka watakil akwai matsala acikin yadda kake gudanar dasu. Domin kuwa ita sallah tana nisantar da mutum daga alfasha da miyagun ayyuka.
Da ache kana yin irin sallar da Allah yake so, lallai da ba zaka kusanci zina ba, Ballantana har ka rika aikatawa. Don haka ya kamata ka sake duban yanayin sallolinka.
Ka nisanci duk wanda kasan shima yana aikata irin wannan aikin. Ka tsarkake zuciyarka da yawan zikiri. Ka lazimci harkokinka da mutanen kirki.
Kayi kokari kayi aure domin shi aure garkuwa ne ga Mumini daga afkawa cikon alfasha. Idan har babu damar yin auren to ka yawaita Azumin nafila.
Ka runtse idanuwanka daga kallon duk abinda Allah ya haramta maka.
Daga cikin addu'o'in da zaka lazimta, babu kamar yawan Karatun Alqur'ani. Tunda kace kana yin azkar na safe da yamma, to sai ka Qara da zikirai na ko yaushe. Kamar su Istighfari, Tasbeehi, Hailala da Salatun Nabiyyi (saww).
Ka Qara da wannan :
"ALLAHUMMA JANNIBNEE MINKARATIL AKHLAQI WAL AF'ALI WAL AHWA'I WAL AFKARI WAL A'AMAL". (Bayan Salloli).
Wannan Mafarkin kuma watakil gargadi ne Allah yake yi maka akan sakamakon masu yin irin wannan aikin
Allah ya shiryeka ya nisantar da kai damu baki daya daga sharrin Zina da dangoginta. Ameen.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU
Share:

Hukuncin yin aure akan aure

HUKUNCIN YIN AURE AKAN AURE :
TAMBAYA TA 2245
********************
Assalamu alaikum malam da fatan kana lfiya? Allah ya bada lada.
Malam ina da tambya, yar uwa tace tayi aure, sai ta na da ciki wata 6 suka dan samu matsala mijin yace tàje gida ta haihu. Malam shekara goma kenan da dawowanta kuma ya hanata komawa kuma yayi aure ya kai sau uku. Malam ya matsayin auran nasu tunda ba sakin ta yayi ba kuma tace ita wani auran zatayi.
AMSA
*******
Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
A'a bai halatta gareta tayi wani aure ba. Domin har yanzu tana nan amatsayin Matar shi wancan Mijin nata tunda bai ce ya saketa ba.
Abinda ya kamata tayi shine iyayenta da nashi su zauna atsakaninsu su daidaita tsakanin 'Ya'yansu. Idan kuma daidaiton ba zao yiwu ba, to sao a raba auren cikin Mutunci da Girmamawa.
Idan kuma duk ba'a samu Mafita ba, Ya kamata akai maganar nan gaban Alkali domin ya gudanar da bincike ya fidda hukunci atsakaninsu.
Shima Mijin bai yi daidai ba. Domin kuwa bai kamata mutum ya kyale Matarsa har tsawon shekara goma shi bai saketa ba, Kuma bai mayar da ita gidansa ba. Wannan ba daidai bane bisa doron karantarwar Alqur'ani da Sunnar Manzon Allah (saww).
Allah cewa yayi :
"KADA KU CHUTAR DASU DON KU QUNTATA GARESU. IDAN KUMA SUN KASANCE MASU JUNA NE, TO KU CIYAR AKANSU (WATO KU DAUKI NAUYINSU) HAR SAI SUN HAIFE CIKINSU".
Da fatan Allah shi daidaita tsakanin nasu idan hakan ne yafi alkhairi garesu. Tunda Allah yace : "SULHU ALKHAIRI NE".
Idan kuma rabuwar ce tafi alkhairi garesu, to dama don haka aka halatta yin saki din.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU
Share:

Duniyar aljannu da abinda ta kunsa

DUNIYAR ALJANU DA ABINDA TA KUNSA (01)
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM
**************************************
DON ALLAH IDAN KANA DA SAURIN TSORATA/FIRGITA, KAR KA KARANTA..
Mun gabatar da karatun ne a ZAUREN FIQHU WHATSAPP (3). Kuma ga yadda karatun ya kasance:
Duniyar Aljanu wata irin duniya ce wacce ta bambanta sosai da tamu duniyar. Ta wajen Kamanninta, da yanayinta, da kuma abubuwan da ta Qunsa.
Allah ya halicci Aljanu bisa siffofi nau'i uku kamar yadda Manzon Allah (saww) ya fada acikin wani hadisi.
Acikinsu akwai wadanda suke da Jikinsu shigen irin namu. Sai dai bambancin yanayin Qirar jikin da kuma girman halittar.
Akwai kuma wadanda Allah ya haliccesu ne abisa siffar Karnuka da Macizai. (Wadannan sune wadanda idan suna jikin mutum zai rika yawan mafarkin Karnuka ko Macizai, ko Qadangaru, etc).
Akwai kuma wadanda su acikin dazuzzuka suke yin rayuwarsu. Sai dai basu zama waje guda. Suna yawan tashi ne daga wani wajwn zuwa wani.
Duk wadannan abubuwan da nake fada, sun samo asali ne daga Alqur'ani da Hadisan Manzon Allah (saww) kuma Sahihan labarurruka sun tabbatar da haka.
Acikin nau'i na farko akwai masu yanayin Qirar jikin 'Dan Adam, suna da kai, suna da jiki da Qafafu da hanaye. Sai dai sun bambanta da na Bil Adama.
Misali akwai masu ido 'daya RAK atsakiyar goshinsu. Akwai kuma wadanda idanunsu ya tsage ne daga sama zuwa Qasa. Akwai masu bindi (jela) da komai irin na halittar Birrai (Monkey).
Wani kuma bakinsa ya fara ne tun daga jikin Kunnensa zuwa daya Kunnen. Wani kuma Hakora ne dashi kamar irin na Damisa ko Zaki. Wani kuma bakinsa kamar irin na Kada ne ( Crocodile).
Wasu kuma suna da yanayin halitta irin na Halittun cikin ruwa. Wasu kuma kamar halittun kan tudu suke.
Wato suna da Kofato, Fukafukai, Qaho, da sauransu. (sune wadanda idan sun shiga jikin 'Dan Adam zai rika yawan mafarkin Shanu suna binsa aguje, ko kuma mafarkin faduwa daga tsauni mai nisa).
Allah ya huwace musu su rika chanza launi, ko Siffar jikinsu zuwa ga wata halittar daban.
Shi yasa akan samu wadanda suke rikida su shigo cikin 'yan Adam har arika yin harkokin kasuwanci ko wata hulda dasu ba tare da an ganesu ba.
Musamman alokacin aikin Hajji, da yawa daga cikinsu sukan zo su chudanya da Bil Adama domin gudanar da ibadarsu. (wadannan muminai ne basa chutar da Bil Adama).
Akwai wanda ya ta'ba gaya mun cewa yayi shekaru fiye da hamsin yana harkokin kasuwancinsa anan cikin Birnin Kano. Yana chinikayya da mutane amma babu wanda yasan cewa shi Aljani ne. (wani dan uwansa ne ya shiga jikin wata Baiwar Allah, shine nace masa yazo ya zama shaida akan dan uwan nasa).
Duk wanda ya taba zama acikin tsangayun Karatun Alqur'ani, zai samu labarin wasu irin aljanu Musulmai Muminai. Ana kiransu da suna "TSOMA".
Suna shigowa tsangayu har ana yin karatun Alqur'ani tare dasu. Kuma wani lokacin suna taimakon Mutane da addu'a ko lakanin samun karatu (Wannan ya faru sosai).
Akwai kuma Qananan yaransu sukan zo suyi wasa acikin yaran Bil Adama. Ba tare da wani babba ya ganesu ba.
Akwai kuma wawayen cikinsu wadanda sukan shigo duniyar Bil Adama domin gudanar da ayyukan sabon Allah. Kamar Zina, Sata, Tsafi, harka da bokaye, etc.
Babban abinda ke tsaremu daga sharrin Miyagun cikinsu shine Alqur'ani da Zikirin Allah. Don haka sai mu rike sosai.
Anan zamu tsaya sai wani lokacin kuma zamu sake lekawa cikin duniyar tasu, bisa hasken Alqur'ani da Sunnar Manzon Rahama (saww).
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP 3 (28-11-2015)
Masu kwafar Rubutunmu suna chanza masa launi, Kuji tsoron Allah ku dena. wannan cin amanar ilimi ne. Kuma Allah zai tambayeku.
Share:

Kwazazzabon wutur jahannama

KWAZAZZABON WUTAR JAHANNAMA
****************************************
Hakika Wutar Jahannama tana da kwarurruka da kwazazzabai da dama wadanda Allah ya tanadesu domin azabtarwa ga Kafirai da Fasikai da masu sa'bonsa.
Wasu daga cikin wadannan Kwazazzabai ambatonsu yazo acikin Alqur'ani, wasu kuma acikin hadisai. Wasu kuma ba za'a sansu ba. Sai dai wadanda suka shiga wutar su zasu gansu (Allah shi kiyayemu don karfin ikonsa).
1. WAILUN : Shine wanda ambatonsa yazo awurare da dama cikin Alqur'ani da hadisai.
Abu Sa'eed Alkhudriy (ra) yace Manzon Allah (saww) yace : "WAILUN WANI KWARI NE ACIKIN JAHANNAMA WANDA SAI KAFIRI YAYI SHEKARU ARBA'IN YANA WULWULAWA ACIKINSA KAFIN YA KAI QASANSA".
(Imamu Ahmad ne da Tirmidhiy suka ruwaitoshi).
Acikin wata riwayar ta Tirmidhiy cewa yayi "WANI RAMI NE ATSAKANIN DUWATSU BIYU (NA WUTA). KAFIRI KAFIRI ZAI YI SHEKARU SABA'IN YANA WULWULAWA ACIKINSA KAFIN YA KAI QARSHEN QASANSA".
Ibnu Hibban ma ya ruwaitoshi kuma Imamul Hakim ya ruwaitoshi kuma ya inganta Isnadinsa.
Daga cikin wadanda zasu shiga wannan ramin na "WAILUN" akwai :
- Masu wasa da sallah.
- Masu tauye Mudu ko Sikeli.
- Masu Qin fidda zakkah.
- Masu Qirkirar abu sannan su dangantashi da Allah.
- Masu Qirkirar labarai na Qarya don ayi dariya.
- Masu yin girman kai idan anyi musu Wa'azi.
2. SA'OOD : Shima ambatonsa yazo acikin suratul Mudatthir ayah ta 17.
Abu Sa'eed Alkhudriy (ra) ya karbo daga Manzon Allah (saww) yana cewa: "WANI DUTSE NE NA WUTA ZA'A TILASTASHI (SHI 'DAN WUTA) CEWA SAI YA HAURO SAMANSA. AMMA IDAN YA DORA HANNUNSA AKANSA SAI HANNUN YA NARKE.
IDAN KUMA YA DAUKE HANNUN SAI HANNUN YA DAWO. IDAN YA DORA QAFARSA AKANSA SAI QAFAR TA NARKE. IDAN YA DAUKETA SAI TA DAWO. SAI YAYI SHEKARU SABA'IN YANA HAWANSA KAMAR HAKA".
(Imamu Ahmad da Hakim ne suka ruwaitoshi kuma Hakim ya inganta isnadinsa).
Acikin riwayar Imamut Tirmidhiy kuma cewa yayi "ZAI YI SHEKARU SABA'IN YANA HAUROWA SAMANSA, KUMA ZAI YI KAMAR HAKA (SHEKARU SABA'IN DIN) YANA GANGAROWA.. HAKA ZAI YI HAR ABADA".
3. GAYYU : Ambatonsa yazo acikin Suratu Maryam (as) ayah ta 59.
Abdullahi 'dan Mas'ud (ra) yace "WANI RAMI NE ACIKIN JAHANNAMA WANDA CIKINSA AKE JEFA MASU BIN SHA'AWARSU". (WATO DUK WANDA YAKE BIYE MA SHA'AWA, AWANNAN RAMIN ZA'A JEFASHI IN BAI TUBA BA).
Imam Tabaraniy da Baihaqiy ne suka riwaitoshi.
Acikin wata riwayar daga Imamul Baihaqiy kuma cewa yayi "(GAYYU) WANI KOGI NE MAI TSANANIN ZURFI DA KUMA QAZAMIN DANDANO".
4. MAUBIQ: Acikin fassara ayar nan ta 52 acikin suratul Kahfi, (WA JA'ALNA BAINAHUM MAUBIQA). Sayyiduna Anas bn Malik (ra) yace "(MAUBIQ) WANI KOGI NE NA 'DIWA DA JINI".
(BAIHAQIY NE YA RUWAITO).
5. JUBBIL HUZNI (RAMIN BAQIN CIKI) : Shi kuma acikin hadisi ne ambatonsa yazo. Wato hadisin da Imamul Baihaqiy ya ruwaito daga Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib (ra) shi kuma yaji daga Manzon Allah (saww) yana cewa:
"KU NEMI TSARIN ALLAH DAGA JUBBIL HAZNI".
Sai suka ce "Ya Rasulallahi menene Jubbul Huzni?".
Sai Annabi (saww) yace "WANI KWARI NE ACIKIN JAHANNAMA WANDA ITA KANTA JAHANNAMA A KULLUM TANA NEMAN TSARI DAGA SHARRINSA HAR SAU SABA'IN.
ALLAH YA TANADAR DASHI NE SABODA QARI'AI (WATO MAHADDATAN ALQUR'ANI) MASU YIN RIYA".
(Imamul Baihaqiy ne ya ruwaitoshi da isnadi mai kyau).
An karbo kusan irin wannan hadisin daga Sayyiduna Abu Hurairah (ra) yace Manzon Allah (saww) yace:
"KU NEMI TSARIN ALLAH DAGA RAMIN NAN NA BAKIN CIKI".
Sai suka ce "Ya Ma'aikin Allah shin menene Ramin Bakin ciki?".
Sai yace "WANI RAMI NE ACIKIN JAHANNAMA WANDA ITA JAHANNAMA TAKE NEMAN TSARIN ALLAH DAGA GARESHI KULLUM SAU DARI HUDU".
Sai suka ce "Ya Rasulallahi su waye zasu shiga cikinsa?".
Sai yace "AN TANADAR DASHI NE SABODA QURRA'U (MASU KARATU) WADANDA SUKE YIN RIYA DA AYYUKANSU. KUMA HAKIKA MALAMAN QUR'ANIN DA SUKE ZIYARTAR AZZALUMAN SARAKUNA, SUNA DAGA CIKIN WADANDA ALLAH YAFI QINSU DAGA CIKIN QURRA'U".
Ibnu Maajah da Tirmidhiy ne suka ruwaitoshi).
Acikin riwayar Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (ra) Kuma, cewa yayi an tanadar da wannan ramin ne domin masu yin riya daga cikin al'ummar Annabi Muhammadu (saww).
Ya Allah ka kiyayemu daga wuta da azabar cikinta, Ka kiyayemu daga aikata duk wani abinda zai kusantamu gareta.
Ya Allah ka bamu aljannarka, Ka bamu yardarka, Ka sadamu da Annabinka (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). Aaameeen.
DAGA ZAUREN FIQHU
Share:

Labarin wani dattijo mai hikima

LABARIN WANI DATTIJO MAI HIKIMA
***************************************
Wani Dattijo mai hikima yana zaune agefen kogi yana hutawa, Yana kallon ruwa. Chan sai yaga wata Qatuwar kunama (Scorpion) ruwa ya daukota. Amma bata mutu ba, tana kokarin tseratar da kanta amma ta kasa.
Nan take sai Dattijon nan ya fara neman wani sanda wanda zai tsamo kunamar nan da ita, amma bai samu ba. Don haka sai ya mika hannunsa domin ya daukota. Ita kuwa kunamar ta harbeshi har sai da ya Qwala Eehu!
Da ya gama Eehunsa sai ya sake mika hannunsa domin ya dauko kunamar nan, Ita kuwa ta Qara harbinsa har ma yafi na farko.
Ya sake mika hannunsa kenan a karo na uku, ashe akwai wani saurayi agefensa yana kallon duk abinda ke faruwa. Sai yace: "Haba dattijo!! Mai yasa zaka rika mika hannunka kunar nan tana cizonka. Ina ruwanka da ita! Ka kyaleta mana'.
Shi kuwa Dattijon nan bai kulashi ba, Har sai da ya samu nasarar tsamowa Kunamar nan daga hallaka. Sai ya juya wajen saurayin yace masa :
"Ya kai Saurayi! Ka sani ita kunama babbar dabi'arta shine HARBI DA CIZO DA MUGUNTA. Ni kuwa Musulmi Mumini, Manyan dabi'o'in da Ubangijina ya horeni akansu sune TAUSAYI, HAKURI, JURIYA, TAIMAKON GAJIYAYYU, AFUWA, DA KUMA YAFEWA.
Shin kafi son in bar Dabi'ar kunamar nan ta rinjayi dabi'una, Ko kuwa inyi amfani da tawa dabi'ar don in samu rabo awajen Ubangijin da ya halicci Kunamar nan!!!".
***********
ZAUREN FIQHU :
Hakika da yawa acikin mutane ana samun masu dabi'a irin ta kunamar nan. Ko acikin 'Yan uwanka ko abokanka, Ko iyalanka zaka iya samun masu irin wannan dabi'ar. Kana iyakar kokarinka wajen taimakonsu amma su bassu gani. Kullum sai Mugunta da butulci da Qeta suke shirya maka.
Kayi kokari kayi koyi da dattijon nan mai hikima. Ka tuna da girman Ubangijinka wanda kake yin komai dominsa. Don neman yardarsa. Kar ka bar dabi'ar mugaye ko Mahassada ta rinjayi dabi'arka.
Kyalesu da halinsu kaci gaba da kyautata musu. Ta wannan hanyar Allah zai yi maka maganinsu.. Amma idan ka dauki irin tasu dabi'ar, dakai dasu duk ba zakuyi daraja awajen Allah ba.
Wannan nasihar tazo muku ne daga ZAUREN FIQHU WHATSAPP (3)
Share:

Wanene yakaryata hadisin sihiri

*WANE NE YA KARYATA HADISIN SIHIRI?*

Rubutun: Dr. Mansur Sokoto
12 Shawwal 1438H
5 ga Yuli 2017

*Bismillahir Rahmanir Rahim*

Babu shakka magabata sun yarda da Hadisin Uwar Muminai A'isha (RA) cewa, Labid bayahude ya yi ma Annabi (S) sihiri. Kuma wannan ya yi tasiri a kan sa har yana ganin kamar ya yi wani abu alhalin bai yi shi ba. Ko kuma ya ga kamar ya zo ma iyalansa alhalin bai zo masu ba. Kuma Allah ya yi masa maganin wannan daga baya, ya ba shi lafiya sannan ya nuna masa inda aka rufe sihirin.
Daga cikin malaman da suka ruwaito Hadisin daga uwar Muminai akwai:
*Imam Ahmad a Musnad* (24741, 24804, 24851, 24852 da 25851)
*Imam Al-Bukhari a Sahihinsa* (3268, 5763, 5765, 5766 da 6391)
*Imam Muslim a Sahihinsa* (5667)
*Ibnu Majah a Sunan* (3545)
*Ibnu Hibban a Sahihinsa* (6703 da 6704)
*Abu Ya'la a Musnad nasa* (4757)
*Imam Al-Baihaqi a Dala'il An-Nubuwwa* (3018).

Ban da ta hannun Nana A'isha (R) kuma Hadisin ya zo ta hanyar Sahabi *Zaid bn Arqam (R)* a cikin littafin *Musnad na Imam Ahmad*  (19481) da *Sunan na Nasa'i* (7/103) dss.

Malaman nan duk da suka ruwaito shi babu wanda ya yi suka ga maruwaitansa ko abinda suka ruwaiton. Wadanda ba su ruwaito shi ba ma - kamar Imam Malik, wanda ya takaita Muwaddarsa ga wani rukuni kebantacce na Hadisai - babu wanda ya yi suka gare shi daga cikin su. Amma *_"Mutakallimun"_* yan hauragiya su ne suka soke shi, malaman Sunna kuma ko waiwayarsu ba su yi ba.

Ibnul Qayyim (RH) ya hikaito maganar *Mutakallimun* - wadanda suka hada da Mu'utazila da yan Falsafa masu bin son zuciya da jefa nassi daga Manzon Allah (S) a *Bola*. Suka ce wai, ba su yarda da Hisham bn urwa da ya riwaito shi ba. Ga ta'alikin da Ibnul Qayyim ya yi a kai:

"وهذا الذي قاله هؤلاء مردود عند أهل العلم ؛ فإن هشاماً من أوثق الناس واعلمهم ، ولم يقدح فيه أحد من الأئمة بما يوجب رد حديثه ، فما للمتكلمين وما لهذا الشأن ؟! و قد رواه غير هشام عن عائشة ، وقد اتفق أصحاب الصحيحين على تصحيح هذا الحديث ، ولم يتكلم فيه أحد من أهل الحديث بكلمة واحدة ، و القصة مشهورة عن أهل التفسير و السنن و الحديث و التاريخ و الفقهاء ، وهؤلاء أعلم بأحوال رسول الله و أيامه من المتكلمين.
Ya ce: "Wannan maganar da wadancan suka fada ba abar karba ba ce a wurin masu ilimi. Domin Hisham (Ibn Urwa; wanda ya ruwaito Hadisin) yana daga cikin mafi amincin mutane kuma mafi ilimi a cikin su. Babu kuma wani shugaba a fagen ilimi da ya soke shi da abinda zai sa a mayar da Hadisinsa. To ina ruwan yan hauragiya da wannan lamari! Sannan kuma ba Hisham ne kadai ya ruwaito shi daga A'isha (RA) ba. Shaihunan Hadisi masu littafai biyu ingantattu ma (Bukhari da Muslim) sun hadu a kan inganta wannan Hadisi. Babu kuma wani malamin Hadisi da ya taba furta wata kalma daya ta sukar Hadisin. Ban da wannan kuma, labarin ya shahara a wurin malaman Tafsiri da masu littafan Sunan (Irin su Tirmidhi da Nasa'i dss) da sauran malaman hadisi da na Tarihi da na Fiqihu. Wadannan kuwa sun fi yan hauragiya sanin yanayin Manzon Allah (S) da tarihinsa.
Duba: Bada'i' At-Tafsir (5/407).

*Maganar Ibnu Uyayna* (RH) da ya ce:
"وهذا أشد ما يكون من السحر إذا كان كذا"
Wadda Dr. Gummi yake ganin Allah ya tayar da shi a wannan zamani don ya fassara ta bayan duk daruruwan shekarun da suka gabata ba a fassara ta ba, a wurin malamai masanan Harshen larabci ba jumla mai rikitarwa ba ce. Abinda take nufi: "Wannan shi ne mafi tsananin yanayin da sihiri ke sa mutum, idan ya kai haka".
_*Sufyan ba ya shakkar Hadisin*_ kamar yadda sauran malamai tsararrakinsa da magabatansa da na bayansa - wadanda hankulansu suke daidai da Shari'a - ba su shakkar Hadisin kuma ba su ganin wata aibantawa ga darajar Manzon Allah (S) a cikin sa.
*Allah ya yi mana garkuwa daga bata da bin son zuciya.*
Share:

Matar da jinin al'ada yadaina zuwa mata,yaya hukuncin iddarta zai kasance idan ansaketa

*_Tambaya ta (333)_*
:
_Matar da *Jinin-Al'ada* yadena zuwa mata, yaya hukuncin *Iddarta* zai kasance idan ansaketa??_
:
*_Amsa:_*
:
_Dangane da abinda yashafi *Iddar Matar da'aka saketa* alhali kuma *Jinin-Al'ada* yadena zuwa mata, dafarko dai Matan da *Jinin-Al'ada* baya zuwa musu sun kasune *Nau'i-Nau'i,* kuma kowanne *Nau'i* daga cikinsu akwai irin hukuncin da ya keɓanta dashi, *Misali:*_
:
_*→(1)-Idan* ya kasance Matar da aka saketa batayin *Jinin-Al'ada* sakamakon yawan Shekarunta saboda tsufa datayi, kokuma saboda *Ƙan-Ƙantar shekarunta* saboda kasancewarta *Yarinyace ƙarama* wacce batama fara *Jinin-Al'adar* ba,  to Iddar irin waɗannan Matan idan aka Sakesu zasuyi lissafine da watanni uku kamar yadda *Aʟʟαн(ﷻ)* Yafaɗa:_
:
*"واللائي يئسن من المحيض من نسائكم إن ارتبتم فعدتهن ثلاثة أشهر، واللائي لم يحضن"*
*_MA'ANA:_*
*_Waɗanda suka ɗebe tsammani da zuwan Haila (saboda tsufa) daga cikin Matayenku, idan kuna kokwanto, zasuyi Iddane tsawon watanni uku, hakanan (hukuncinsu daidai yake da) waɗannan da basayin al'ada (saboda ƙuruciyarsu)_*
:
_*→(2)-Idan* ya kasance Mace batayin *Jinin-Al'adane* sakamakon *Shayar da Jariri datakeyi* kamar yadda akan samu Mata dayawa waɗanda basa *Jinin-Al'ada* alokacin dasuke *Shayarwa,* to irin wannan Matar idan aka Saketa dolene tajira har zuwa lokacin da *Jinin-Al'da zai zomata* koda kuwa hakan zaikaita zuwaga lokacin da zata yaye Jaririn datake *Shayarwar,* wato Shekaru biyu kenan, kokuma idan tanaso *Jinin yazo mata* da wuri to saita bayar da *Jaririn* nata wata Matar ta Shayar dashi, kokuma tayi amfani da wani magani wanda zai janyo mata al'adarta alokacin datake *Shayarwar*, amma da *Sharaɗin* yakasance anada tabbas kokuma zato mafi rinjane akan cewa maganin yadace da Jikinta bazai cutar da'itaba,_
:
_*→(3)-Idan* ya kasance *Matar da'aka Saketa* Asali dafarko tanayin *Jinin-Al'ada* amma daga baya sai yadena zuwa sakamakon wani *Sababi* wanda ba tsufaba, to itadai wannan Mata ɗayane daga cikin biyu, kodai yakasance tasan *Sababin da yahana Jinin zuwa* kokuma yazamana batasan *Sababin ba,* idan ya kasance batasan *Sababin da yahana Jinin zuwaba* itadai kawai taga tadena ganin jini, to anan ansamu maganganun *Malamai* guda biyu akai, wasu daga cikin *Malamai* sukace zatayi tajirane harsai randa tayi jini uku, koda kuwa hakan zaikaita ga daukan adadin Shekaru masu yawa tofa dolene sai tajira, kokuma idan jinin baizo mataba har takai shekarun tsufa na debe tsammanin zuwan jini, to shikenan yanzu sai tayi Idda da watanni uku kenan amatsayinta na tsohuwa, to amma Saidai kuma akwai Malaman da suka tafi akan cewa wannan maganace mai rauni, domin akwai cutuwa ta bangaren ita Matar, tunda bazai yiwu tayi aureba tun tana da kuruciyarta harsai ta tsufa,_
:
_Magana tabiyu kuma itace, wasu daga cikin Malamai  sukace Iddar irin wannan Mata zata zaunane har tsawon *Shekara guda Cur,* watanni 9 amatsayin mafi galibin tsawon lokacin da mai ciki takeyi kafin ta haihu, Saikuma watanni 3 amatsayin Idda idan anhada yazama watanni 12 kenan, amma idan yazamana Mace tasan *Sababi ko Dalilin da yahana zuwan Jinin,* kamar dalili na rashin lafiya, ko Shayarwa, kokuma ya kasance itace tasha wani magani dan Jinin yaɗauke, ko wani abu makamancin haka, to irin wannan Matar idan aka saketa zata jirane har zuwa lokacin da Jini uku zai zomata, idan kuma Jinin bai zoba to itama zatayi Iddane na tsawon *Shekara ɗaya,* amma idan yakasance Mace zatayi *Iddane na tsawon Shekara ɗaya,* Misali tayi watanni *7, ko 8, kokuma 9,* kawai saitaga *Jinin-Al'ada yazomata,* to yanzufa lissafinta yarushe, danhaka dolene tasake jiran zuwan *jini na 2, da na 3,* idan baizoba har tasakeyin wata *Shekarar shikenan,* amma idan *jini na 2 yazo* koda kuwa tayi *watanni 9* da zuwan na farko, to anan ma lissafinta yasake rushewa, danhaka dole sai tasake jiran *Jini na 3 yazo* sannan tagama idda, idan kuma *jini na 3n* baizoba har tasakeyin wata *Shekarar* shikenan tagama Iddah,_
:
_To amma Idan ya kasance *Mace Mijinta mutuwa yayi* bawai sakinta akayiba, to anan zatayi Iddane irin *Iddar Mutuwa* wato *Takaba,* itakuma Iddar Mutuwa hukuncinta yasha *Bam-Bam* da Idda irin ta Sakin aure, domin dukkanin waɗancan *Nau'ikan Matan* da aka ambaci yadda hukuncin Iddarsu take, to idan ya kasance Mijinsu Mutuwa yayi to dukkansu yanayin Iddarsu zata kasance iri ɗayace, wato watanni huɗu da kwana goma adadin kwanaki *(130)* kenan, da Matar datake *Jinin-Al'ada,* da wacce batayi, da Tsohuwa, da wacce batama fara *Jinin-Al'adarba saboda Ƙuruciya,* da mai *Jinin-Istahara* wacce ita kullum acikin Jini take, dukkansu hukuncinsu ɗayane, mai ciki ce kaɗai akace iddarta shine tahaife abindake cikinta,_
:
*_※(шαʟʟαнυ- тα'αʟα α'αʟαмυ)※_*

*_ωαηαη sнιηε gωαяgωαdoη ɗαη αвιηdα ιʟιмιη мυ dαкυмα вιηcιкεηмυ үαкαι zυωα gαяεsнι, dαηнαкα ιdαη αηgα ωαηι кυsкυяε αcιкιη αвιηdα мυкα яυвυтα тo αηα'ιүα ғαɗαкαя dαмυ мυgүαяα, тαяεdα кαωo нυננα мαι ƙαяғι:_*
:
*_Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:_*
                 *_↓↓↓_*
:
*"المغني لإبن قدامة" (8/87)*
:
*مواهب الجليل" (3/404)*
:
*"التاج والإكليل" (4/143)*
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
              *Daga Zaυren*
             *Fιƙ-нυl-Iвadaт*
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
              *_→AMSAWA←_*
           *Mυѕтαρнα Uѕмαи*
              *08032531505*
*_""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""""_*
_*Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾*_
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat/
Share:

Hukuncin qasru 10

*HUKUNCIN SALLAR QASRU-10!!!???*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Taken Lekca........
.
*SALLAR QASRU!!!!??*
.
Wannan shine bayani na goma****
.
.
Cigaba***
.
.
_Ibnul Usaimeen acikin Littafinsa ASHSHARHUL MUNTI' mujallad na hudu shafina 505, yakawo maganar Ibn taimiya inda yace duk mutuminda ya cika sallah ahalin tafiya toh ya aikata makaruhi***_
.
_kenan da wannan zamu gane cewa makaruhine ga matafiyi yakiyin qasru yadinga cika sallah***_
 .
_Sannan kuma kan malamai ya hadu akan cewa idan matafiyi yabi mazaunin gida sallah toh shima matafiyin yazama dole yacika sallah, koda kuwa raka,a daya yasamu a wannan jam,in da yabi***_
.
_kenan zamu gane kuskurene abinda wasu mutane sukeyi idan suna ahalin tafiya wai sesuzo subi jam,i abayan limami mazaunin gida, idan anyi raka,a biyu wai sesu zauna sujira limamin idan yagama yayi sallama suma sesuyi toh wannan babu shakka kuskurene***_
.
_haka kuma wasu yanda sukeyi shine suna tsayawane bazasu shiga cikin jam'inba harse wannan limamin yagaka raka'a biyu sannan sesu shiga akarasa ragowar biyun dasu sesuyi sallama tareda liman, toh wannan shima kuskurene, inhar matafiyi yabi mazaunin gida jam,i toh yazama dole akan wannan matafiyin yacika sallah****_
.
_amma babu laifi shi matafiyin yazama limami ga mazaunan gida, idan yagama raka,a biyunshi yayi sallama sai sukuma sumike suciko ragowar raka,a biyun***_
 .
_Abdulqaheer Al baghdadi acikin littafinshi *AKHDA'UL MUSALLIN* wato kura kuran masallata, yakawo maganarda wasu mutane sukeyi cewa wai dan mutum ya hada tsakanin salloli biyu asanda yake doron tafiya kokuma yana yin qasru sesuce wai yacika lalaci da ragontaka, toh baghdadi yatabbatarda wannan maganar tasu amatsayin kuskure, wanda shima baghdadi yanada fahimtar cewa yin qasru wajibine ga matafiyi, wanda munyi wannan bayanin abaya, toh amma shima baghdadi ya kuskurantarda wayanda suke cewa idan tafiya ta sabon Allah ce wai baza,ayi qasruba, harma yakafa hujjah da waccan bayanin na Ibn qayyum wanda yake cikin ZADUL MA,AD mujallad nafarko shafina 461***_
.
_Sannan kuma qasru ba,ayi mata niyya, wato bazakayi niyyar qasru ta daban ba, Aa niyya zakayi kawai kamar yanda kasaba yin sallah, wannan yake nuna babu laifi idan kafara sallah danufin zakayi qasru sekuma daga baya kana cikin yin sallar sai kachanza shawara kawai kabar qasrun kacika sallah, wannan babu laifi insha Allahu, sedai kamar yanda muka fada abaya, makaruhine ga matafiyi ya cika sallah***_
.
_sekuma jam'in sallah asanda ake doron tafiya, wannan shima yasamo asali asunnar Annani muhammad alokacinda mutum yake cikin tafiya beriga yakai inda zashiba kuma yana ganin cewa lokacin wata sallah zai sameshi bekai inda zashiba toh babu kaifi ya janyo wata sallah kokuma ya jinkirta wata***_
.
_misali kana tsakar tafiya sai lokacin azahar yayi toh babu laifi kahada sallar azahar da la,asar kayisu awannan lokacin sekawai kacigaba da tafiyarka, haka kuma inkaso kana iya jinkirta azahar din se lokacin la,asar yayi sai kayisu tare, hakama ana hada tsakanin magriba da isha'i***_
.
_Toh wani yayi tambaya gameda mutuminda yake tafiya acikin jirgin ruwa shin yaya zeyi sallah?? Toh Albani acikin Sifatus Salah yayi bayani wannan inda yakawo hadisai akan hakan, daga ciki akwai wanda manzon Allah yace wanda yake cikin kwale kwale zeyi sallah atsaye matukar baya jin tsoron nutsewa****kenan idan kanajin tsoron zaka fadi toh sai kayi sallar azaune karika yun nuni, wato (IMA'I)***_
.
_Wani kuma yayi tambaya gameda mata da miji wayanda suke zaune awata kasa suna karatu shin suma qasru zasuyitayi har sudawo?? Eh babu shakka qasru zasuyitayi koda shekaru nawa zasuy acan**aduba tafsirin Qurdubi mujallad na biyar fassarar ayata 101 cikin suratun nisa'i***_
.
_Yan kasuwa wayanda suke tafiya ta kasuwanci zuwa wasu kasashen waje shin suma qasrun zasuyi?? Eh suma qasru zasuyi harse sun dawo***_
.
_Matarda mijinta yake zaune awani gari daban, ita kuma tana wani gari daban toh shin idan taje wajen mijinta awancan garinda yake shin qasru zatayi?? Eh kwarai kuwa qasru zatayi harse tadawo***_
 .
_Matafi wanda yariga yadawo gida amma akwai wata sallarda ta riskeshi ahanya beyiba toh tunda yariga yadawo gida yaya zerama sallar??? Yanda zerama shine: Idan sanda yadawo gida lokacin wannan sallar be fitaba, toh zeramatane cikakkiya wato raka,a hudu, amma idan lokacinta yariga yafita toh zeramata qasru zeyi raka,a biyu kenan***_
.
_misali sallar azaharce ko la,asar kokuma duka biyun suka riskeka ahanya baka samu damar yinsuba har kazo gida, toh idan sanda ka iso gidan rana tafadi, toh zaka ramasu qasrune raka,a bibbiyu, amma idan rana bata riga tafadiba sanda kazo gida toh zakayisu cikakkune domin lokacinsu yananan bai fitaba, haka kuma idan isha,ice tasameka ahanya, toh inhar kazo gida alfijir bai fitoba toh zaka ramatane cikakkiya, amma idan sanda ka iso gida alfijir yariga ya bayyana toh zaka ramata qasrune, dukda cewa anfiso kayi sallar acikin lokacinta koda kana cikin motane kawai karika nuni kayi sallar ahaka karka bari lokacinta yafita wannan shine abinda yafi dacewa***_
.
_Wayanda suke ahalin tafiya shin ya halasta suhadu suyi jam,in sallarsu qasru?? Eh kwarai kuwa ya halasta suyi qasru***_
.
_yaya matafiyi zeyi sallar juma,a?? Toh shi matafiyi sallar juma,a ba wajibi bane akanshi, inyaso yana iyayin sallarshi shikadai a masaukinshi seyayi raka,a biyu kawai kamar yanda yasaba, amma dai idan yafita yaje masallaci yabi jam,i toh hakan yafi insha Allahu***_
.
_mutuminda yakeyin qasru seya shigo masallaci yatarar ana jam,i yaya zeyi tunda su masu jam,in cika sallah sukeyi?? Abinda zeyi shine yakoma can baya seyayi sallarshi shikadai***_
.
_Dalubi wanda yake karatu awata kasar waje kuma yana kwashe shekaru awaccan kasar shin yaya zeyi qasrunshi??wannan bayanin munyishi abaya mukace qasru zetayi awaccan kasar koda shekara dubu zeyi, kawai yaita qasru harse yadawo***_
.
.
_Alhamdulillahi anan mukazo karshen wannan lekcar, amadadin abokan aikina wayanda suke kai gwauro sukai mari wajen ganin wannan aiki yatafi kamar yanda kuke gani***_
.
.
_Almajirinku kamar kullun_
.
```Jameel Alhassan Haruna Kabo```
_(Abu khausar)_
 .
_nake mana fatan Alheri wassalamu,alaikum***_
.
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
https:/t/m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka  Wanatubu ilaika
Share:

Hukuncin qasru 9

*HUKUNCIN SALLAR QASRU-9!!!???*
.
.
*DAGA ZAUREN*
.
*KITABU WAS SUNNAH*
.
.
*ﻣﺠﻠﺲ ﺍﻟﺘﻌﻠﻴﻢ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ*
📓📔
Watsaps
08036222795
08136182627
.
.
Taken Lekca........
.
*SALLAR QASRU!!!!??*
.
Wannan shine bayani na tara****
.
Cigaba***
.
.
_Ibn Qayyum acikin Zadul ma,ad mujallad na uku shafina 561, yace: Manzon Allah (s.a.w) har yabar duniya baicema Al,umarsa idan kunyi kwanaki kaza agarinda kukaje kudena yin qasru ba, kuma baice sekun kai nisa kaza sannan zakuyi qasruba****_
.
_Toh Alhamdulillahi yanzu dai mungamada batun kwanakinda akeyi ana qasru, munce babu adadi harse kadawo kawai, sannan mungamada irin tafiyarda ake mata qasru nanma munce kowacce irin tafiya anayin qasru koda tafiyar ta sabon Allah ce****_
.
_Toh inda rigimar take yanzu shine, shin yaushe ake fara yin qasrun kuma yaushe ake denawa???_
.
_Munkawo muku sabanin malamai abaya inda wasu sukace tun kana gida zaka fara qasru dazarar kayi shirin tafiya, wasu kuma sukace Aa bazaka fara qasruba harse kafara tafiyar kawuce gonakin garinku, wasu kuma sukace sai ka wuce gidajen garinku, wasu kuma sukace sekaci kimanin mil uku, wasu kuma sukace buridi hudu, wasuma sukace Aa saika isa wancan garin kuma bazaka faraba sai dare yayi***_
.
_Toh wannan matsalar a gaskiya nidai bansan abinda zance akantaba, sedai zanyi tauqifi kawai wato bazance komaiba saboda maganganun babu na yarwa aciki kuma babu wacce tadace adauketa dari bisa dari, amma bari innemi agaji da wata maganar Albani acikin Adabu Zifaf, Albani yace idan aka samu irin wannan sabanin toh kawai kai kakoma kaida zuciyarka kayi tunani kaga tsakaninka da Allah wacce maganar kafi gamsuwa da ita?? Toh duk wacce zuciyarka tafi natsuwa da ita toh kai awajenka da wannan zakayi aiki***_
.
_Toh ni awajen nafi natsuwa da wayanda sukace bazaka fara qasruba har sekabar gidanka kafara tafiya koda bakayi nisaba indai kafito kabaro gida toh yahalasta kafara qasru ni nafi natsuwa da wannan maganar saboda Hadisin Anas dan Malik dayace Suda Annabi muhammad zasuyi tafiya amma sai Annabin yaimsu sallar azahar raka,a hudu sanda suke gida, amma bayan sun fito sekuma yaimusu la,asar raka,a biyu a Zulhulaifah, saboda haka wannan itace fahimtata ni, dazarar kabaro gida ka kama hanya toh kawai ya halasta kayi qasru, na zabi wannan fahimtar ne saboda dacewarta da wannan hadisin, amma bawai na yanke hukunci bane na kore fahimtar sauran malaman***_
.
_fahimtar wayanda sukace kana iya fara qasru tun kana gida dazarar kayi shirin tafiya itama wannan tanada karfi saboda dacewarta da zahirin waccan ayar idan aka fassarar kalmar *DARABTUM* da ma,anar *(AZAMTUM)* toh amma cewa saika wuce gonaki ko kawuce gidaje ko saikaci wani zango kokuma saika kwana daya, toh wayannan maganganun Ibn Taimiya yace basuda asali a qur,ani da sunnah, sedai ansamu wasu daga cikin malamai sunyi aiki da hakan, *ALLAHU TA,ALA A'ALAM* nikam bansaniba gadai bakin kokarina nayi sekuma anemi manyan malamai sukara mana bayani***_
.
_sekuma cewa idan tafiya ba me nisa bace ba,ayin qasru itama wannan ibn taimiya yace batada asali sannan kuma ta sabama zahirin ayar Alqur,ani, amma nakaranta fatwar wasu malamai wacce take cikin ALJAMI,I LI AHKAMUL QUR,AN sukace kawai duk tafiyarda a Al,adar garinku inkayita za,a ce kayi tafiya toh ya halasta kayi qasru, duk tafiyarda baza,ace kaje unguwaba sedai ace kayi tafiya toh sukace ya halasta kayi qasru, toh babu shakka wannan maganar tanada karfi amma sedai kuma tasabama zahirin wancan hadisin na sayyadina Umar wanda yayi qasru a zulhulaifah aka tambayeshi seyace nayi kamar yanda naga Annabi yayi***_
..
_Saboda haka abinda yafi dacewa awannan maganar itama shine kawai tauqifi, dan haka semuce kawai duk sanda kayi tafiya toh dazarar kaji kai azuciyar kanatsu cewa wannan tafiyarda kayi kaji cewa kanatsu akan eh lallai yakamata kayi qasru toh kawai kayi qasrunka, kaga kenan anbar kofar abude cewa duk sanda kayi tafiya koda gajerace wato koda unguwa kaje, inhar kaji azuciyarka kanatsu cewa wannan yar tafiyar da kayi kaji aranka cewa yakamata kayi qasru toh kawai kayi kayanka koda kuwa unguwace kaje wacce ba mai nisaba, wannan shine abinda yafi dacewa da waccan maganar ta Ibn Qudama, Allahu ta,ala A,alam***_
.
_Toh sekuma batu gemada lokacinda mutum zaidena qasru wanda shima wannan anyi sabani, wasu malamai sukace bazaka bar yin qasruba harse kazo gida nafarko agarinku, wato wajenda kafara kenan afahimtar wayanda suke ganin bazaka fara yin qasruba saika wuce gida nakarshe agarinku***_
.
_wasu kuma sukace zakabar yin qasrune dazarar kazo gona tafarkon shiga garinku, ga masu fahimtar ana farawa daga gona ta karshe***_
.
_wayansu kuma sukace bazaka dena yin qasruba harse kashiga gidanka, wasu kuma sukace zakabar yin qasru ne dazarar kafara hangen gidajen garinku***_
..
_Toh wannan matsalar itama sedai muyi tauqifi kawai tunda kakaf malaman basuda aya basuda hadisi kawai gwajin fahimta sukayi, toh dan haka semuce kawai kaduba wacce zuciyarka tafi natsuwa sai kayi aiki da ita ammadai aji tsoron Allah****_
.
_Amma ni nafi natsuwada fahimtar wayanda sukace zaka dena yin qasrune dazarar kashigo garinku, saboda wannan shine fahimtar sayyadina Aliyu kamar yanda bukhari yakawo acikin littafinshi a babin qasru, kenan sai muce koda ace kadawo daga tafiyar gaka ga garinku kana hango gidajen garin amma baka shigaba toh ya halasta kayi qasru insha Allahu***_
.
_*ALLAHU TA'ALA A'ALA WA A'ALAM* haza huwa ma indi wabillahit taufeeq***_
.
.
_zamu dakata anan sekuma fitowa tagaba wacce muke fatan tazama ta karshe da ikon Allah***_
.
.
.
_Almajirinku kamar kullun_
.
```Jameel Alhassan Haruna Kabo```
_(Abu khausar)_
 .
.
.
.
Zaku iya samun shafinmu na facebook tawannan hanyar
https:/t/m.facebook.com/Kitabu-Wassunah-1522000298067561/
.
ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.

Subhanak Allahumma wabi hamdika nash hadu anla ila ha illah anta nastagfiruka  Wanatubu ilaika
Share:

Archive

Unordered List

Support