*YA MUTUM ZAYYI RAMUWAR SALLAR DA YA MANTA BAYAN LOKACIN WATA YA SHIGO??*
Aslamu alaikum warahamatull lahi taala wabara katuhu malan ya mutum zaiyi ramuwar sallah wadda baiyi bah a baya
الحمد لله والصلاة والسلام على محمد وآله وصحبه وسلم.
AMSA:Dafarko kafin mu amsa tambayar zamuyi wani bayani dazai bada haske akan ramuwar sallar da mutum yamanta ko kuma takubuce masa baiyiba.
Hukuncin jeranta sallolin dasuka riga suka wuce mutum bai yiba.
Malaman mazahabobi guda uku Abu hanifa, Ahmad, Malik. suntafi akan wajabcin jeranta sallolin da suka wuce, yayin ramasu, dalili akan haka shine manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ya rama wasu sallar data wuce masa ajere alokacin yakin kandaq.
Imamul bukhari ya ruwaito hadisi(641) da muslim(631). daka jabir dan Abdullahi manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ya rama sallar la'asar data wuce baiyi taba aranar yakin kandaq, bayan rana tafadi, sannan sai yayi magriba bayan ya rama la'asar,
haka kuma bukhary ya ruwaito (631) Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace ( kuyi sallah kamar yadda kukaga inayi. Almugny(2/336).
Idan mutum ya manta jerantawar wajan ramuwa shin jerantawar tafadi akansa?
Na'am idan mutum ya manta jeranta salloli wajan ramasu jerantawar tafadi akansa, saboda fadin manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace:(Allah madaukakin sarki yadaukewa al'ummata abunda suka aikata bisa kuskure bada niyyah ba, dakuma abunda suka aikata bisa mantuwa da kuma abunda aka tursasau akai) Ibnu majah (2043) Albany ya ingantashi acikin sahihu ibnu majah (1662) kuma wannan itace mazhabar limamai biyu Abu hanifa da Ahmad Allah yai musu rahama.fat hul qadeer(1/424). da Almugny (2/340).
Duk wanda yamanta sallah har lokacin wata ya shigo,yana da halaye guda uku
1-ya tuna sallar data wuce masa kafin ya shiga wacce lokacin tane, awannan lokacin wajibine yafara yin wacce ta wuce kafin yin wacce lokacin tane.
2-Ya tuna ana binsa sallar data kubuce masa bayan ya kammala wacce take alokacin ta, to sallar dayayi wacce take alokacin ta tayi, sai yarama wacce ake binsa abayanta, saboda yana da uzurin rashin jerantawa da mantuwa
3-Ya tuna ana binsa sallar data wuce akansa yana cikin yin wacce lokacinta yake, awannan hali zai cika wacce lokacinta yake nan saita zamto masa amatsayin nafila, sannan sai yayi wacce ake binsa, sai yasake wacce take alokacinta saboda kiyaye jerantawa, wannan itace mazhabar imamu Ahmad Rahimahullah Almugny (340-2/336).
itace maganar Abdullahi bin umar Yardar Allah takara tabbata agaresu.
Imamu malik ya ruwaito acikin muwaddah, daka nafi'u cewa Abdullahi dan umar yana cewa: wanda ya manta sallah bai tuna ana binsa sallah ba saida yana cikin bin liman a wata sallar, idan liman yayi sallama, sai yayi sallar data wuce masa yasake wacce yayi tare da liman.
Shaikul islam ibnu taimiyyah Rahimahullahu yace:( Duk lokacin da mutum ya tuna ana binsa wata sallah yana cikin yin wata zai kasance kamar baifara yin wacce take alokacinta ba, Amma dazai tuna ana binsa sallah bayan yagama wacce take alokacinta, to wacce yayi alokacinta ta isar masa awajan mafiya yawan malamai kamar Abu hanifah, da shafi'i da Ahmad.)Fatawal kubra (1/112).
Cewa da akayi zai cika wacce yake alokacinta mustahabbine ba wajibiba da zai yanke wacce yake alokacinta, yayi wacce ake binsa sannan yayi wacce take alokacinta hakan ya isar masa.
Wasu malaman suntafi akan cewa zai karasa wacce yake alokacinta bazai sake maimaita taba, sannan sai yayi wacce ake binsa, wannan shine mazhabar imamul shafi'i, kamar yanda yazo Acikin Al majmu'u (3/70).
kuma shine zabin uthaimeen rahimahullah, kamar yanda yazo acikin fatawarsa(12/221). Maganar farko ita tafi daidai.
Idan mun fahimci yanda ake rama sallar data kubucewa mutum da mantuwa ko wani dalili karbabbe ashari'a, to ga yanda zai rama din kuma shine muka dan fadada bayani asama.
والله أعلم،
***********************************
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
_*Tambayoyin*_ _*Musulunci*_
_*WhatsApp*_ _*Group*_