Ka/ki kiyaye raka'o'i 12 domin samun gida a aljannah ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Friday 28 October 2016

Ka/ki kiyaye raka'o'i 12 domin samun gida a aljannah

KA/KI KIYAYE RAKA'O'I 12 DOMIN SAMUN GIDA A ALJANNAH..

Assalamu alaikum malam dan allah ina son ayimin bayanin yadda nafilolin da ake yi kafin sallah da kuma bayan sallah suke da kuma falalarsu wslm?

Amsa:

الحمد لله

Malaman fiqhu sunyi bayanin cewa sallolin nafila na rana a asirce ake yinsu, su kuma sallolin nafila na dare a bayyane ake yinsu. Amma sallar bayan maghrib (ba'ad maghrib) da kuma raka'atanil fajr kana iyayi a bayyane ko a asirce. Hujja kuwa itace; Hadisin da Ibn Majah da Tirmizi suka ruwaito daga Abdullahi Dan Mas'ud (Allah ya yarda dashi) yace yaji abinda Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yake karantawa a sallar bayan Maghrib da kuma nafilar sallar al-fijr. Kenan wannan ya nuna manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yana yi a bayyane shi yasa har Dan Mas'ud yaji abinda yake karantawa.

Haka kuma akwai hadisi wanda Uwar muminai A'isha (Radiyallahu anha) ta ruwaito cewa Annabi (sallallahu alaihi wasallam) ya kasance yana karanta Fatiha ne kadai acikin raka'atanil fajr, kuma yana yinta ne a asirce.

Saboda haka dai su sallolin Ba'ad maghrib wato sallar bayan maghrib da kuma raka'atanil fajr kana iya yinsu a bayyane ko asirce, kuma yana da kyau ma ka rinka yi kana canzawa; yau kayi asirce gobe kayi a bayyane.

Sai kuma dangane da fafalarsu; to kowace daga cikin sallolin nafilolin tana da nata falala wadda ita kadai take da ita kuma. Amma kuma akwai hadisi wanda ya nuna mana falalarsu a jimlace. Imam Muslim ya ruwaito hadisi daga Ummu Habeebah (Allah ya yarda da ita), matar Annabi (sallallahu alaihi wasallam) tace:  Naji manzon Allah (sallallahu alaihi wasallam), yace: " Ba wani Musulmi wanda zai kiyaye yin raka'o'i 12 na nafila kowace rana, bayan yayi na farillah face Allah bai gina masa gida a aljannah ba"...

A wata ruwayar hadisin kuma wanda Tirmizi (415) ya ruwaito daga ita din Ummu Habeebah(Allah ya yarda da ita) tace: Manzon Allah (sallallahu alaihi wasallam) yace: " Duk wanda ya kiyaye yin raka'o'i goma sha biyu (12) a dare da rana, to za'a gina masa gida a cikin Aljannah: raka'a hudu kafin zuhr da kuma raka'a biyu bayanta, raka 2 bayan maghrib da kuma raka'a biyu bayan Isha'i sai kuma raka'a biyu kafin sallar subhi" Sheikh Albani ya ingantarda hadisin a cikin Saheeh Sunan at- Tirmizi.

Saboda haka dan uwa ko yar uwa da fatan zamu kiyaye yin wadannan sallolin nafilolin domin samun gida a Aljannah. Allah yasa muna cikin wadanda zasu tsinci kansu a aljannah Firdaus.

Wallahu a'alam

سبحانك اللهم وبحمد ك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.

Tambayoyin Musulunci
WhatsApp group
+2348164884055
+2347068043652

Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support