*RAYUWARMU A YAU KENAN*
Ko ka taba karanta _*English Version*_ na irin wannan labari, ka dan daure karanta wannan akwai wani dan qarin bayani a ciki....
Wata rana wata malamar Lissafi (Mathematics Teacher) ta shigo aji sai ta rubuta wannan rubutun dake a qasa akan allo..
_*9×1=7*_
_*9×2=18*_
_*9×3=27*_
_*9×4=36*_
_*9×5=45*_
_*9×6=54*_
_*9×7=63*_
_*9×8=72*_
_*9×9=81*_
_*9×10=90*_
Bayan ta kammala rubutunta, koda ta juyo ta kalli dalibanta tuni aji ya kacame da dariya suna nuna mata hannu akan allo saboda wancan kuskuren da tayi na farkon wanda ta sanya _*9×1=7*_ a maimakon _*9×1=9*_ wanda yake shine daidai.
Sai malamar tayi murmushi tana mai gaya musu cewa:
_*" Ai dama nayi haka ne da gangan ( a sane ) saboda inason ku koyi darasi daga wannan kuskuren nawa"*_
Wannan zai zamo darasi gareku kusan cewa haka mutane ke biye daku. Yanzu ku duba ba tare da duba da irin wahalar da nake yi daku ba wajen koya muku wannan lissafi har kuka iya, ban taba yi muku kuskure ba sa'annan kuma a wannan rubutun kadai na rubuta amsoshi guda tara *_9*_ gaba dayansu daidai, sa'annan kuma baku yi la'akari da cewa wadannan amsoshin guda tara gaba dayansu sunfi waccan amsar ta farko wuya ba kuma duka nayi su daidai amma a cikinku ba wanda ya jinjina min sai wannan kuskuren shi kawai kuka gani kuma kuke dariya da tuhumata akansa.
Lallai ina mai qara jaddada muku ku sani wannan babban qalubale ne zuwa gare ku, haka rayuwar take.......
Mutane ba zasu taba gode ko jinjina maka ba a duk dimbin miliyoyin ayukan alkhairi da kayi, amma kuma zasu saka maka ido tare da zargin/tuhuma akan kuskure qwaya daya kacal da kayi. _*AMMA FA KADA KU KARAYA SABODA WANNAN*_
_*SABODA HAKA A KULLUM IDAN KA MIQE ZUWA AIKATA ALKHAIRI TO KA KAUDA KAI DAGA DARIYA, ZARGI DA KUMA TUHUMAR MUTANE. KADA KA NEMI GODIYA, JINJINAWA KO SAKAYYAR MUTANE. KAWAI DUK ABINDA ZAKA YI TO KAYI DAN ALLAH. KUMA KA NEMI TSARI DA GAFARA DAGA GARE SHI SABODA SHI YANA GANIN DAIDANKA KUMA YANA GANIN KUSKURENKA.*_
_*Idan kuma kace kana jiran godiya da sakayya daga mutane babu shakka za ka sha mamaki kuma idan aikin lada ne kake yi zaka rasa ladar, kaga ka tashi a tutar babu kenan.*_
_*YA ALLAH KA QARA KYAUTATA MANA NIYYOYINMU*_
_*YA ALLAH KA KARBI AYUKANMU NA ALKHAIRI KA YAFE MANA KURA-KURANMU*_
*Tambayoyin*_ _*Musulunci*_
_*WhatsApp*_ _*Group*_
0 comments:
Post a Comment