Hukuncin ci ko sha da mantuwa alhali mutum yana azumin nafila ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Tuesday, 8 November 2016

Hukuncin ci ko sha da mantuwa alhali mutum yana azumin nafila

*HUKUNCIN CI KO SHA DA MANTUWA ALHALI MUTUM YANA AZUMIN NAFILA*

Mai azumin nafila ko da gangan yaci abinci ko ya sha abin sha ko yayi jima'i da matarsa to bai da laifi kuma ba zai rama azumin ba. Saboda Annabi (s.a.w.) yana cewa: "Mai azumin nafila sarkin kansa ne, in ya ga dama ya ci gaba da azumi, in ya ga dama kuma ya karya" Albani ya ingantarda shi a sahihul-jami'i hadisi mai lamba ta: 3854.

Haka kuma idan yaci ko ya sha ko yayi jima'i da matarsa da mantuwa alhali yana azumin nafila to yana da zabi guda biyu:

1. In yaga dama yaci gaba da azuminsa saboda duk wanda yaci abinci ko yasha abinsha cikin mantuwa, ko cikin kuskure, ko kuma aka tilasta masa, to babu kaffara ko ramuko akansa. Saboda Sahihin hadisin da Abu Huraira (r.a) ya ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w) yana cewa:
"DUK WANDA YA MANTA CEWA YANA AZUMI, HAR YACI ABINCI KO YASHA WANI ABU, TO
YACI GABA DA AZUMINSA. HAKIKA ALLAH NE YA CIYAR DASHI KUMA YA SHAYAR DASHI"
(Jama'ar Maruwaitan hadisi ne suka ruwaito
shi).

Haka kuma Ibnu Maajah da Hakim daga Abdullahi bn Abbas (r.a) daga Manzon Allah (s.a.w) yana cewa:
"ALLAH YA DAUKE MA AL'UMMATA LAIFIN DA SUKAYI CIKIN KUSKURE, DA MANTUWA, DA KUMA ABINDA AKA TILASTA SU AKANSA".

Anan koda kuwa na farillah to zai ci gaba da azuminsa kawai Allah ne ya ciyar ko ya shayar dashi.

2. Ko kuma idan yaga dama sai yaci gaba da cin abincinsa wato ya karya azumin gaba daya saboda shine sarkin kansa kamar yadda hadisi yazo a sama. Anan ana nufin mai azumin nafila kenan, banda mai azumin farillah.

Wallahu a'alam

Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support