*ABINDA AKE SO WANDA YAJI KIRAN SALLAH YAYI DAGA LOKACINDA YAJI KIRAN SALLAH HAR I ZUWA IQAMAH*
Assalamu alaikum
Malam dan Allah ina so amin bayani akan yanda ake amsa kiran Sallah
Nagode
وعليكم السلام ورحمة الله.
ﺍﻟﺤﻤﺪ ﻟﻠﻪ ﺭﺏ ﺍﻟﻌﺎﻟﻤﻴﻦ ، ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﺳﻴﺪﻧﺎ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﻋﻠﻰ ﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﺃﺟﻤﻌﻴﻦ، ﻭﺑﺎﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﻮﻓﻴﻖ
_*AMSA:*_
*******
Da farko dai abinda ake son wanda yaji kiran sallah yayi shine: Maimata wato fadin irin abinda duk ladan ya fada. Amma wajenda ladan ke cewa:
*ﺣﻲ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺼﻼﺓ*
*"Hayya alal Salah"*
da
*ﺣﻲ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻔﻼﺡ*
*"Hayya alal falah"*
Anan sai ace
*ﻻ ﺣﻮﻝ ﻭﻻ ﻗﻮﺓ ﺇﻻ ﺑﺎﻟﻠﻪ*
*"La haula wala quwwata illa billah"*
[Bukhari da Muslim 385]
Idan kuma mai kiran sallah ya kammala kiran sallah sai kace:
*"Ashhadu an la'ilaha illallah wahdahu la sharika lahu, wa anna Muhammadan abduhu wa rasuluhu, raditu billahi rabban, wa bi Muhammadin rasulah, wa bil islami dinan"* [Muslim]
Bayan wannan sai mutum yayi wa Annabi sallallahu alaihi wasallam salati:
Daga Jabir (Allah ya yarda dashi) yace: Annabi (sallallahu alaihi wasallam) yace: "Dukkan wanda yace a lokacinda yaji kiran sallah:
*ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺭﺏ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﺪﻋﻮﺓ ﺍﻟﺘﺎﻣﺔ ﻭﺍﻟﺼﻼﺓ ﺍﻟﻘﺎﺋﻤﺔ ﺁﺕ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﺍﻟﻮﺳﻴﻠﺔ ﻭﺍﻟﻔﻀﻴﻠﺔ ﻭﺍﺑﻌﺜﻪ ﻣﻘﺎﻣﺎ ﻣﺤﻤﻮﺩﺍ ﺍﻟﺬﻱ ﻭﻋﺪﺗﻪ*
*"Allahumma Rabba hazihid da'watit tammat wassalatil qaimati, ati Muhammadan waseelata wal fadeelata, wab'athhu maqaman mahmoodal lazi wa'adtahu"*
Cetona ya halatta akansa ranar alqiyamah". [Bukhari, 589]
Wato duk wanda aka gama kiran sallah yayi wannan addu'ar zuwa ga Annabi (sallallahu alaihi wasallam) dake a sama to cetonsa ya halatta a gare shi ranar qiyamah. Allah yasa muna daga cikin wadanda zai ceta.
Sai kuma tsakanin kiran sallah zuwa tada iqamah ana son mutum yayi addu'a saboda ana amsar addu'a a wannan tsakanin. Daga Anas (Allah ya yarda dashi) yace: Annabi (sallallahu alaihi wasallam) yace:
*Haqiqa ba'a mayarda addu'a tsakanin kiran sallah da iqamah, saboda haka kuyi addu'a*. [Tirmizi 212, Abu Dawud 437, Ahmad 12174]
والله أعلم،
***********************************
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
_*Tambayoyin*_ _*Musulunci*_
_*WhatsApp*_ _*Group*_
0 comments:
Post a Comment