SHIN YA MATSAYIN SADAQA DA AKEYI WAJEN MUTUWA MISALI UKU BAKWAI ARBA'IN
الحمد لله والصلاة والسلام على محمد وعلى آله وصحبه وسلم
AMSA: Malamai sunyi ittifaqi akan cewa sadaqa da nemawa mamaci gafara da hajji duk suna isa zuwa ga mamaci.
Dalili akan addu'a da istigfari shine fadin Allah madaukakin sarki
(والذين جاؤوا من بعدهم يقولون ربنااغفرلنا ولإخواننا الذين سبقون بالإيمان)
Wadanda sukazo abayansu zasu dunga cewa ya ubangijinmu kagafarta mana damu da 'yan'uwanmu dasuka rigayemu da imani.
Manzan Allah sallahu Alaihi wasallam yace: ( kunemawa dan'uwanku gafara, ku roka masa tabbatuwa domin yanzu za'a tambayeshi)
yasake cewa : ( Idan zakuyiwa mamaci sallah ku kyautata addu'a gareshi)
Amma sadaka ya tabbata acikin bukhari daka ubadah bin sabit yardar Allah takara tabbata agareshi, mahaifiyarsa ta rasu baya gari yace: ya manzan Allah mahaifiyata ta rasu bana nan shin innai mata sadaka zata amfaneta, sai manzan Allah yace: eh, sai ubada bin sabit yace: ina shaida maka gonata mai 'ya'yan kayan marmari na badashi sadaka agareta. bukhary (2756).
Amma aikin hajji kuwa Manzan Allah sallalllahu Alaihi wasallam yace: da matar data tambayeshi shin zan iya yiwa mahaifiyata aikin hajji bayan ta mutu? sai yace; shin inda bashine akanta zaki biya mata, sai tace : eh sai Annabi yace bashin Allah shine yafi cancanta abiya.) Bukhary 6699 muslim 1148.
Wadannan dalilai sun nuna sadaqa tana amfanar wanda ya mutu kuma ladanta zai isa gareshi.
Ansamu hadisi mai rauni wanda yake nuna ya halatta cewa idan kaiwa mamaci sallah ladan zaije gareshi, sai dai imamu muslim yace hadisine mai rauni acikin mukaddimar littafinsa ingantacce daka Abdullahi bin mubarak, sannan imamu muslima yace babu sabani akan sadaka.
Amma azumi da sallah amazhabar shafi'iyyah da jamhur din malamai ladansu baya kaiwa ga wanda ya mutu, sai dai idan azumin nawajibine mamaci ya mutu ana binsa to waliyyinsa zai rama masa ko kuma wanda mamacin yaiwa izinin ya rama masa kafin rasuwarasa.
Imamun nawawy acikin tuhfatul muhtaaj yace: " mamaci zai amfana da sadakar da akai masa daka ciki akwai kana iya sayen alqur'ani kakai masallacin daza'a dunga karantasu ko makaranta amtsayin wakafi ga mamacin, ko ka haka rijiya inda ake bukatar ta amatsayin wakafi ga mamaci, koya dasa bishiya zaidunga samun ladanta matukar ana amfana da ita, ko kuma wani yadasa bishiyar amatsayin wakafi ga mamacin.
Amma mafificiyar hanyar da mamaci zai amfana da wani abu dazakai mar shine kayawaita masa addu'ar Allah yagafarta masa, ko ka gina masallatai a inda ake bukatarsu da rayasu da ilmi, ko taimakawa dalibai tahanyar biya musu kudin makaranta ko buga littattafai dansu amfani dasu.
Amma taruwa da'ake bayan kwana uku da mutuwar mamaci a karanta alqur'ani ko adauki dukiyar marayu ayi abunci da sunan sadaka ga mamaci, wannan bidi'ane kuma cin dukiyar marayuce batare da hakki ba, Allah kuma yaharamta cin dukiyar marayu, haka ta arba'in haka ta shekara wadannan duk bidi'o'ine Allah bai saukar dawata hujja akai ba.
Kawai kai kadai kaiwa mamaci addu'a kadauki dukiyarka ta kanka halaliyarka kayi sadaqa da ita da nufin Allah yakai ladan ga mamaci wannan shine zai isa ga mamaci kamar yanda dalilai suka gabata, shima kuma batara mutane akace kaiba, zakayi batare ma dakowa ya sani ba wannan shine sunnah.
والله أعلم،
***********************************
سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا انت أستغفرك وأتوب إليك.
_*Tambayoyin*_ _*Musulunci*_
_*WhatsApp*_ _*Group*_
0 comments:
Post a Comment