Matsalar saurin kawowa (wato rashin dadewa lokacin jima'i) ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Monday, 31 October 2016

Matsalar saurin kawowa (wato rashin dadewa lokacin jima'i)

*MATSALAR SAURIN KAWOWA ( WATO RASHIN DADEWA LOKACIN JIMA'I)*

Rashin sanin hakikanin gaskiyar magana dangane da lokacinda namiji yake iya dauka kafin yayi inzali (wato irin tsawon lokacin) ya kasance abu mai matukar damuwar da yawa daga cikin ma'aurata a wannan zamani. Ya kasance yana saka mazaje da yawa cikin damuwa da rashin walwala sosai gun iyalansu wanda hakan yasa suke ta neman magunguna haukace daga masu bayarda irin wadannan magungunan na gargajiya; ba kadan yake laqumewa mazaje kudi ba. Wannan matsalar tana kasancewa silar son kashe aure ga wasu matan da sunan suje su auri masu daukar tsawon lokaci domin biya musu bukatarsu, wasu matan kuma har yakan zamo silar sabon Allah garesu ta hanyar neman maza a waje wai duk da sunan mazansu basa biya musu bukata. Kuma duk wannan damuwar da wahalolin suna faruwa ne saboda irin  yadda mutane suke karantawa a mujallu, social media, littafai e.t.c cewa maza suna daukar tsawon mintuna talatin (30) zuwa sama suna jima'i kafin suyi inzali( kafin maniyyi ya fito musu) wasu kuma suna jin labarai ko gani ne a irin bidiyoyin batsa da Yahudawa maqiya Allah suke shiryawa.

To dan uwa mai cike da damuwa ganin cewa baka daukar tsawon lokaci yayin saduwa da matarka ko kuma malama mai ganin cewa mijinki baya da lafiya kike damuwa duk ku kwantarda hankulanku wancan bayanin dake a sama na mintuna talatin zuwa sama ba gaskiya bane, bayani zaizo daga baya. Abinda bincike daga masana kwararru a wannan fannin ya tabbatar shine:

1. *Mafi yawan maza suna daukar tsawon mintuna 4 zuwa 5 ne ko kuma 5 zuwa 7*.  Kuma wadannan mazajen lafiyayyu ne daram.

2. Qalilan sosai ne daga cikin maza *suke iya daukar mintuna 12 zuwa sama suna saduwa da matansu bayan shigarsu*.

3. Su kuma wadanda wannan cutar ta saurin kawowa ke damu to *suna kawowa ne irin seconds 15 zuwa  seconds 30 wato dai kasa ga minti 1 kacal bayan sun shigi mace. Wasu ma suna inzali ne tun kafin su shigi matan nasu*. Kuma da zaran sunyi inzali kafin su sake mayarda karfinsu (kafin gabansu ya qara mikewa) wani aiki ne babba.

Sai kuma maganar cewa mazaje suna daukar mintuna 30 zuwa sama ba za'a ce ba'a rasawa ba amma dai mafi yawancin hakan ciwo ne. Sai kuma wadanda suke ji daga masu tallar magunguna, su kuma wadannan suna yi ne dan tallar maganinsu. Wadanda kuma suke kalla a bidiyoyin batsa irin wadanda yahudawa maqiya Allah suke yadawa shi kuma wannan abinda wani fasiqi wanda shi Mai shirya irin wannan batsar ne ya gayawa masu wannan binciken shine *Yadda mutane suke ganin bidiyoyin ba haka abin yake ba. Suna iya daukar watanni suna hada bidiyon. Yace ya kan yiwu shi fasikin wanda ake nunowa yana fasikanci da macen yayi inzali kusan sau biyar ko goma duk a cikin bidiyo guda amma sai su dinga katse wuraren sai subar na karshen kawai. Misali suna iya suzo idan suka fara fasikancin nasu idan yayi inzali sai su tsaya sai kuma wani lokaci idan zasu ci gaba sai su sake dorawa daidai wurinda suka tsaya; kalar kwanciya (position), wurinda suke fasikancin, kalar kaya da komai dai duk iri daya kamar yadda ake hada fim, haka kuma idan ya qara inzali sai su dakatarda daukar sai kuma lokacinda zasu ci gaba hardai sukai tsawon lokacinda suke bukatar kaiwa, sa'annan kuma muna ba jarumman namu kwayoyin kara kuzari*. Kunga kenan indai hakane to suna iya nuna bidiyo mai tsawon awoyi amma shi mai kallon fasikancin sai yaga kamar duk tun lokacinda suka fara fasikancin yine suke bai kawo ba. *Ku kura da kyau wannan fa bincike ne kuma ni na kawo wannan bayanin ne domin wayarda kai tare da kwantarwa da yawa daga cikin yan uwa maza masu ganin cewa kamar basu da lafiya da mata masu ganin cewa mazansu basu da lafiya hankulansu saboda irin yadda suke karantawa ko gani a irin wadannan hanyoyin dake a sama. To kunji yadda suke shirya wannan fasikancin.*

To wasu daga cikin masu rubuce-rubuce akan wannan matsalar wadanda mafi yawancinsu masu tallar magunguna ne suna amfani da irin wannan bayanin ne ba tare da sanin hakikanin gaskiyar lamarin ba domin tallar hajojinsu. Wasu ma sun sani kawai dai dan su tallata kayansu ne ta yadda mutum zai ga lallai baida lafiya bari ya siya maganinsu.

Saboda haka dan uwa mai ganin tamkar baka da lafiya ko wadda take ganin mijinta baya da lafiya har take kokarin rabuwa dashi ko neman wani a waje saboda irin wancan bayanin na karya to ku kwantarda hankalinku karya ne. Haka kuma wanda ma yake fama da wannan rashin lafiyar wato saurin inzali din (rashin dadewa ana saduwa) wato baya iya daukar ko minti daya kacal yana saduwa da iyalinsa to sai ya garzaya asibiti ko wajen masu islamic medicine akwai magunguna kuma suna dan tasiri sa'annan kuma ga wasu 'yan hanyoyi masu taimakawa sosai ga masu wannan rashin lafiyar, harda ma wadanda ke irin mintuna 2 ko 3 haka to duk wannan bincike ya nuna zasu samu ci gaba su haura hakan idan suna bin wadannan hanyoyin. Ga hanyoyin kamar haka:

1. Mutum ya yawaita motsa jiki (exercise)

2. Cin lafiyayyen abinci mai gina jiki da qara lafiyar jiki da kuma yawan cin 'ya'yan itatuwa (Kawai dai aje asibiti domin samun gamsasshen bayani)

3. Yin wasa da gaba a fitarda maniyyi aqallah awa daya kafin fara jima'i da matarka ( *A lura wannan bincike ne a kimiyyance to kuma munsan cewa a musulunce yin wasa da gaba har a fitarda maniyyi haramunne. To amma mafita itace sai ka saka matarka tai maka wannan aikin aqallah awa daya kafin ku fara kaga zaka iya sanyata tai maka bayan kayi inzalin sai ku shiga wanka tare ta yadda dai zaku iya bata lokaci har ayi awar kuna tare kafin fara jima'in, kaga wannan ma duk karin soyayya ne*)

4. Matarka ta dinga yi maka wasa da azzakarinka har sai kaji ka kusan kawowa sai ta dakata, sai gabanka ya tafi kwantawa sai kuma taci gaba ku yawaita yin haka, shima masana sunce yana taimakawa sosai wajen qara tsawon lokaci yayin saduwa.

5 Ku dinga yin wasa sosai da matarka gabanin ka shigeta ta yadda koda kayi  saurin inzalin to ita matar zata iya samun biyan bukatarta daga wadannan wasannin.

6. Haka kuma akwai irin taimakawar da ita macen zata dinga yi yayin saduwar. Kamar lokacinda kuke jima'i idan kaji ka kusa kawowa sai ka cire ita matar tayi sauri ta dan matse kan azzakarinka ta yadda sha'awarka zata dan gushe. Haka kuma kasancewar matarka a samanka shima wannan yana taimakawa sosai. (Wannan dai idan mai fama da rashin lafiyar yaje asibiti duk zai samu cikakken bayani)

To da yardar Allah masana wannan fannin sunce idan mai fama da wannan rashin lafiyar yana yin haka zai samu canji sosai. Haka kuma wadanda suke yin irin mintuna 2 ko 3 haka suma idan suna bin wadannan matakan to lokacinsu zai karu sosai kamar zuwa 4 zuwa 5 haka. Allah ya kara mana lafiya da abinda lafiya ke bukata.

+2348164884055.
+2347068043652.

*��Tambayoyin Musulunci��*
           *WhatsApp Group*

Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support