Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Saturday, 25 November 2017

kada Tufar Musulmi Ta Wuce Idon Sawu Dr Ibrahim Jalo Jalingo



Duk inda Musulmi yake wajibi ne ya daure ya bi Allah a cikin suturar da yake sanyawa; watau wajibi ne ya tabbatar da cewa wandonsa, ko rigarsa, ko alkebbarsa ba su kasance kasa da idanun sawunsa ba. Wannan shi ne abin da Allah Ya wajabta masa a wannan babin.

Lalle ba daidai ba ne mutum musulmi a bisa zabinsa, da ganin damarsa, saboda kawai neman ado ya je ya biya tela kudi ya dinka masa Zunubi da Bala'I; watau: wandon da ya zarce idon sawunsa, ko rigar da ta zarce idon sawunsa, ko alkebbar da ta zarce idon sawunsa. Lalle wannan Bala'I ne babba cikin wannan Al'ummah Muhammadiyyah.

Imam Malik ya ruwaito Hadithi na 1,631 cikin Muwataa, da Imam Ahmad Hadithi na 11,023 cikin Musnad, da Abu Dawud Hadithi na 4,095 cikin Sunan, da Nasaa'iy Hadithi na 9,633 cikin Sunan, da Ibnu Majah Hadithi na 3,573 cikin Sunan, da Ibnu Hibban Hadithi na 5,447 cikin Sahih, da Dabaraaniy Hadithi na 13,113 cikin Muujam, da Ibnu Abi Shaibah Hadithi na 25,318 cikin Musannaf da isnadi sahihi daga Abu Sa'id Al-Khudriy ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce:-
((ازرة المسلم الى نصف الساق، ولا حرج فيما بينه وبين الكعبين، ما كان أسفل من الكعبين فهو في النار، من جر إزاره بطرا لم ينظر الله اليه)).
Ma'ana: ((Suturar Musulmi zuwa tsakiyar kwabri ne, amma babu laifi cikin abin da ya kasance tsakaninsa da idanun sawu, abin da kuma ya kasance kasa da idanun sawu wannan shi yana cikin Wuta, wanda kuma suturarsa ta ja kasa saboda nuna ado sam Allah ba zai dube shi ba)).

Sayyidina Abubakar Allah Ya kara masa yarda ya kasance Idan ya dan gafala mayafinsa na jan kasa, Sannan nan da nan sai ya daga shi; kamar yadda Imam Ahmad da Baihaqiy suka ruwaito.

Saboda fa'idah ga wasu ayyuka da maganganun Sahabbai game da isbaalin sutura:-
روى الامام النسائي في السنن: ٩٦٢٠ عن ابن عباس رضي الله عنه قال: ((ان الله لا ينظر الى مسبل)).
وروى الدارمي في السنن: ٢٨١٠ عن عبادة بن قرط قال: ((إنكم لتأتون أمورا هي ادق في اعينكم من الشعر كنّا نعدها على عهد رسول الله صلى الله عليه وسلم من الموبقات. فذكر لمحمد يعني ابن سيرين فقال: صدق فارى جر الإزار من ذلك)).
وروى ابن ابي شيبة في المصنف: ٢٥٣٢٤ عن أنس بن مالك قال: ((الإزار الى نصف الساق أو الى الكعبين، لا خير فيما هو أسفل من ذلك)).
وروى ابن ابي شيبة في المصنف: ٢٥٣٢٦ ان عمر دعا بشفرة فرفع ازار رجل عن كعبيه ثم قطع ما كان أسفل من ذلك)).
وروى ابن ابي شيبة في المصنف: ٢٥٣٢٧ عن ابي إسحاق قال: ((رأيت ناسا من اصحاب رسول الله صلى الله عليه وسلم ياتزرون على أنصاف سوقهم؛ فذكر اسامة بن زيد، وابن عمر، وزيد بن أرقم، والبراء بن عازب)).
وروى ابن ابي شيبة في المصنف: ٢٥٣٣١ ان عثمان بن عفان كان إزاره الى نصف ساقيه، قال: فقيل له في ذلك؟ فقال: هذه ازرة حبيبي، يعني النبي صلى الله عليه وسلم)).

Allah Ka tausaya wa wannan Al'ummah Ka cusa mata ganin kyawun abin da duk yake sunna ce ta ManzonKa. Ameen.
Share:

Hadarin Zama Da Mace Daya!!! Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa


Zama da mace daya yana kawo illoli da dama ga magidanci da su mata kansu da kuma
al`umma.
****
ILLOLI GA MAGIDANCI.

1:-Yana rage masa nishadin aure.
2:-Yana kawo tsufa da wuri.
3:-Yana saka maigida cikin damuwa
4:-Yana saka wa mace ta rika daga masa kai, tayi masa yadda taso saboda ta san ba shi da yadda zai yi.
5:-Yana rage masa samun soyayya da tarairaya da kulawa da ya cancanta a matsayinsa na maigida. 
6:-Yakan hana shi tantance so na gaskiya daga bangaren matarsa ko wanin haka.
****
ILLOLI GA SU MATAN.

1:-Yana hana wadansu samun mazajen aure.
2:-Yana dorawa matar gida aiyukan da suka shige misali kamar, kulawa da maigida,  yaran gida da ita ma kanta. 
3:-Yakan hana mace samun isasshen hutu da kuma lokacin kulawa da kanta.
4:-Yana rage wa mace kuzarin nuna soyayya ga maigidanta.
5:-Yana saka matar gida cikin tsoro da fargaba maras yankewa na ko za ai mata kishiya.
6:-Yana haifar da rashin amincewarta ga maigidanta da dauwamar da tuhuma ta har abada.
7:-Yana saka mace cikin shirin yaki da dawainiyar dakon makamai marasa ranar yankewa na nuna kin ayi mata kishiya. 
8:-Yana saka mata yawan zargi ga dukkan matan da suke da alaka da maigidanta ko ma wace iri ce koda ma yar uwa ce ko abokiyar kasuwancinsa. 
9:-Yana kara mata zafin kishi da rashin nutsuwa marasa ranar yankewa.

****
ILLOLIN GA AL`UMMA
1:-Yana haifar da karuwai mata marasa aure.
2:-Yana bunkasa yawan zawarawa acikin al`umma.
3:-Yana dorawa al`umma karin nauyin kulawa da mata iyayen marayu da marayun kansu. 
4:-Yana bunkasa zinace-zinace a cikin
al`umma.
5:-Yana rage tausayi da son bada taimako da agaji daga zukatan al`umma. 
6:-Yana kara saka fargaba da tsoro a zukatan iyaye wadanda suke da `ya`ya mata a gaba. 
7:-Yana bunkasa kasuwar malaman tsibbu da bokaye.

WADAN NAN SU NE KADAN DAGA ILLOLIN ZAMA DA MACE DAYA, 
DA FATAN MAGIDANTA ZASU GANE, 
SU KUMA MATA ZA SU TAIMAKAWA JUNANSU WAJEN TUNAWA MAI GIDA YA QARA AURE.
Share:

Wednesday, 22 November 2017

Hadarin Zama Da Mace Daya !!! Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

Zama da mace daya yana kawo illoli da dama ga magidanci da su mata kansu da kuma
al`umma.
****
ILLOLI GA MAGIDANCI.

1:-Yana rage masa nishadin aure.
2:-Yana kawo tsufa da wuri.
3:-Yana saka maigida cikin damuwa
4:-Yana saka wa mace ta rika daga masa kai, tayi masa yadda taso saboda ta san ba shi da yadda zai yi.
5:-Yana rage masa samun soyayya da tarairaya da kulawa da ya cancanta a matsayinsa na maigida. 
6:-Yakan hana shi tantance so na gaskiya daga bangaren matarsa ko wanin haka.
****
ILLOLI GA SU MATAN.

1:-Yana hana wadansu samun mazajen aure.
2:-Yana dorawa matar gida aiyukan da suka shige misali kamar, kulawa da maigida,  yaran gida da ita ma kanta. 
3:-Yakan hana mace samun isasshen hutu da kuma lokacin kulawa da kanta.
4:-Yana rage wa mace kuzarin nuna soyayya ga maigidanta.
5:-Yana saka matar gida cikin tsoro da fargaba maras yankewa na ko za ai mata kishiya.
6:-Yana haifar da rashin amincewarta ga maigidanta da dauwamar da tuhuma ta har abada.
7:-Yana saka mace cikin shirin yaki da dawainiyar dakon makamai marasa ranar yankewa na nuna kin ayi mata kishiya. 
8:-Yana saka mata yawan zargi ga dukkan matan da suke da alaka da maigidanta ko ma wace iri ce koda ma yar uwa ce ko abokiyar kasuwancinsa. 
9:-Yana kara mata zafin kishi da rashin nutsuwa marasa ranar yankewa.

****
ILLOLIN GA AL`UMMA
1:-Yana haifar da karuwai mata marasa aure.
2:-Yana bunkasa yawan zawarawa acikin al`umma.
3:-Yana dorawa al`umma karin nauyin kulawa da mata iyayen marayu da marayun kansu. 
4:-Yana bunkasa zinace-zinace a cikin
al`umma.
5:-Yana rage tausayi da son bada taimako da agaji daga zukatan al`umma. 
6:-Yana kara saka fargaba da tsoro a zukatan iyaye wadanda suke da `ya`ya mata a gaba. 
7:-Yana bunkasa kasuwar malaman tsibbu da bokaye.

WADAN NAN SU NE KADAN DAGA ILLOLIN ZAMA DA MACE DAYA, 
DA FATAN MAGIDANTA ZASU GANE, 
SU KUMA MATA ZA SU TAIMAKAWA JUNANSU WAJEN TUNAWA MAI GIDA YA QARA AURE.
Share:

Tuesday, 14 November 2017

ABOKAI KALA HUDU NE - Zauren fiqhu

ABOKAI KALA HUDU NE
*************************
Hakika kowanne mutum da Allah ya bama daukaka ko daraja awani fanni na rayuwa, dole zai samu masoya kala-kala. Kamar yadda kuma zai iya samun Makiya da Mahassada nau'i daban daban.

1. Akwai wanda yake da'awar cewa shi Masoyinka ne. Amma ba zai tashi matsowa jikinka ko kuma nuna maka soyayya ba, sai lokacin da yaga wata nasara ta samu gareka. Amma idan kishiyar nasara (wato Asara) ta samu, ba zaka ganshi ba. Dama ni'imar ce ta kawoshi.

- Wannan ba abokin kirki bane, ba masoyin gaske bane. Kayi hankali dashi.

2. Akwai wanda yana nan tare dakai ko yaushe, amma duk abinda kasa agaba sai ya tayaka kuyi. Ba ya yi maka musu, ko gyara acikin lamarinka koda ya ganka akan kuskure haka zai tayaka kuyi.

- Wannan masoyi ne amma yana da rauni acikin soyayyarsa. Kayi hankali dashi.

3. Akwai wanda yana tare dakai ko yaushe amma idan yaga abin alkhairi tare dakai sai ya binne labarin. Idan kuma yaga mummunan abu tare dakai sai ya watsa ma duniya. Ta wajensa ake samun Miyagun labarai game dakai.

- Wannan Makiri ne, Mahassadi ne. Ka nisanceshi tun kafin yayi maka illa. Idan kuma ba zai yiwu ka nisanceshi ba, to lallai ne ka rika boye masa sirrinka.

4. Akwai masoyin da ko yaushe yana tare dakai azuciyarsa ko kuma afili. (Koda ba ya yi maka zakin kalamai).

Duk lokacin da ya ganka akan alkhairi sai ya taimakeka kuyi. Idan kuma ya ganka akan kuskure sai ya gyara maka koda ranka ba yaso.

- Wannan shine masoyi na gaskiya. Ka rikeshi da kyau domin irinsa suna da wahalar samu.

Hakika Allah yana cewa:

"MASOYA AWANNAN RANAR (WATO ALKIYAMAH) SASHENSU ABOKAN GABA NE GA SASHE. SAI DAI MASU TSORON ALLAH".

Wato aranar Alqiyamah abokai zasu zamanto masu Qin gamuwa da abokansu, saboda tsoron ko zasuyi jayayya dasu agaban Allah.

 Amma wadanda suka gina abotarsu bisa gaskiya da rikon amanar juna da tsoron Allah, sune zasu rabauta.

Zasu zama sanadiyyar samun rahama ga junansu (Kamar yadda hadisai da dama suka tabbatar).

Ya Allah ka hadamu da mutanen kirki masu Qaunarka, kuma wadanda Soyayyarmu dasu zata amfanemu awajenka.

Ka rabamu da miyagun abokai na fili da boye. Ka kiyayemu daga sharrinsu da makircinsu. Ameeen.

Wannan sadaukarwa ce ga dukkan abokai da Masoya.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP -3 07064213990 {08-11-2016} 08-02-1438.
Share:

LABARIN ABU HANIFAH DA WANI KAFIRI- Zauren fiqhu

LABARIN ABU HANIFAH DA WANI KAFIRI
*****************************************
Watarana acikin garin Baghdad akwai wani babban kafiri wanda bai yarda da tauheedi ba, kuma bai yarda da cewa akwai Allah ba.

Har ma ya kirkiri wasu tambayoyinsa na shirme yana ta neman wanda zai amsa masa su. Duk Maluman garin sun kyaleshi basu daukeshi da muhimmanci ba, shi kuma yana ci gaba da bankaurarsa.

Alokacin nan Imam Abu Hanifah (rah) yana yaro Qarami bai fi shekara goma ba. Watarana yazo wucewa sai yaji mutumin nan yana da kurarin cewa wai Musulmai sun kasa amsa tambayoyinsa.

Sai Imam Abu Hanifah ya matsa kusa dashi yace masa "In sha Allahu ni zan amsa tambayoyin naka komai wahalarsu".

Mutumin ya amsa gayyatar, Kuma Jama'a suka cika da mamaki. Ta yaya wannan 'dan Qaramin yaro zai iya jayayya da Kafirin nan wanda manyan Maluma suka kasa ja dashi!

Da ranar Mukabalar tazo sai Jama'ar garin gaba daya suka taru a wani fili a tsakiyar garin Baghdad wanda dama anan ake gabatar da duk wani Muhimmin taro.

Sai shi wannan kafirin ya hau kan tudun dake tsakiyar taro. Sannan ya bude muryarsa ya jefo tambayarsa ta farko zuwa ga Abu Hanifah kamar haka :

"SHIN MENENE ALLAHN NAKU YAKE YI A DAIDAI YANZU?"

Abu Hanifah ya tsaya yayi tunani na 'yan mintuna kadan, sai yace ma mutumin "To ina so kai ka sauko Qasa, ni kuma in hau sama sannan in baka amsarka".

Wannan yaro Qaramin yaro 'dan shekara goma (wato Imam Abu Hanifah) ya hau saman kan tudun sannan yace "Ya Allah kaine shaida gareni agaban duk wadannan Mutanen cewar na shaida lallai yanzun nan kai ka Qaddara saukowar wannan kafiri zuwa Qasa, kuma ka Qaddara cewar Mumini zai hau sama (wato zai daukaka akansa)".

Da Mutane ('yan kallo) suka ji wannan amsar ta fito cikin fasaha daga bakin Abu Hanifah, sai suka fara kabbara "Allahu Akbar!" Allahu Akbar!"

Tun daga nan kafirin nan ya fara ganin Qaskanci. Amma sai ya sake jefowa tambayarsa ta biyu "SHIN MENENE YAKE RAYE KAFIN ALLAHN NAKU?" (Subhanallah).

Imam Abu Hanifah (rah) yayi tunani zuwa wani lokaci sai yace ma kafirin ya Qidaya masa lambobi daga goma zuwa Qasa.

Sai kafirin ya fara "Goma, tara, takwas, bakwai, shida, biyar, hudu, uku, biyu, daya, sufiri"

Sai yaron (wato Imam) yace masa "Shin me ka gani bayan sufiri (wato zero)?". Mutumin yace "Babu komai kafinsa, ni ban sani ba".

Da jin haka sai Imam yayi murmushi yace masa "To gashi nan ka riga ka bama kanka amsa.. Hakika Allah shine rayayye kuma dawwamamme. Babu kowa kuma babu komai kafinsa".

Daga wannan sai waje ya rude da kabbara,  suna Qara jinjina ma Imam Abu Hanifah (rah).

Kafirin nan zuciyarsa ta harzuka, ransa ya baci. Sai ya jefo tambayarsa ta Qarshe "SHIN YANZU WAJEN INA (WACCE KUSURWA) ALLAHN NAKU YAKE KALLO?" (Shin gabas yake kallo ko yamma ko kudu ko Arewa?).

Imam Abu Hanifah bayan yayi tunani zuwa wani lokaci sai yace a kawo masa Fitila (Aci-balbal ko kuma kyandir). Da aka kawo masa sai ya damka wa kafirin nan. Yace masa ya kunna masa.

Bayan kafirin ya kunna kyandir din sai ya tambayi Imam to menene dalikin haka?.

Sai Imam Abu Hanifah yace masa "Shin wanne waje ne wutar hasken kyandir din nan take kallo?"

Sai kafirin yace "Tana kallon dukkan kuskuwoyi ne. (wato gabas, yamma, kudu, arewa, sama da Qasa) Babu inda bata kallo"

Sai Imamu yace masa "Ai ka riga ka amsa tambayarka. Hakika Hasken Allah ya mamaye ko ina. Yana nan ako ina, babu wajen da babu shi".

Daga nan sai mutane suka rude da kabbarori "Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!!".

Shi kansa wannan kafirin yayi mamakin ilimi da basirar yaron nan. Don haka anan wajen ya furta kalmar Shahada, ya zama Musulmi kuma ya zama Almajirin Imam Abu Hanifah (ra).

Yardar Allah ta tabbata gareka Ya Imam Abu Hanifah. Allah ya saka muku da alkhairi bisa hidimar da kukayi ma addininsa.

Ya Jama'a wadannan fa sune wadanda suka yiwa addinin Allah hidima, suka rairayo mana garin Ilimi, suka dafa mana tuwonsa yanzu muke ci.

Amma abun Mamaki sai kaji mutum ya hura lasifika yana kushesu yana fadin cewa basu iya ba, shi ya fisu iyawa, ko kuma Malaminsa ya fisu.

Su fa sun rayu ne acikin mafiya alkhairin zamanunnuka, a Qalla dai sun riski wadanda suka ga Sahabbai. Kuma duk Mutanen da sukayi zamani dasu sun tabbatar da nagartarsu da gaskiyarsu.

Allah shi bamu albarkar masu albarka. Ameeen.

DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP -1 Juma'ah 11-11-2016 (11-02-1438).
Share:

MAZINACI DA MAZINACIYA IDAN BASU TUBA BA, ZASU HADU DA BALA'O'I GUDA GOMA SHA BIYAR KAMAR HAKA

MAZINACI DA MAZINACIYA IDAN BASU TUBA BA, ZASU HADU DA BALA'O'I GUDA GOMA SHA BIYAR KAMAR HAKA :

⚫ BALA'O'I GUDA BIYAR TUN DAGA NAN DUNIYA :

1. Zubewar Imani (hadisi yace duk mai yin zina bashi da imani alokacin da yake aikatawa).

2. Zubewar Mutuncinsu (su kansu sun san cewa basu acikin lissafin mutanen kirki awajen Allah da bayin Allah).

3. Lalacewar Zuriyyarsu (Duk wanda yayi zina sai anyi da 'Yarsa ko 'Yar Uwarsa ko Qanwarsa).

4. MUMMUNAN TALAUCI : Zina tana haifar musu da mugun talauci. da kuma rashin albarkar duk abinda ya shigo hannunsu.

5. MUMMUNAR JINYA : Jinya acikin zuciyark
Su (bushewar zuciya), ko kuma ajikinsu (Qanjamau, Ciwon sanyi, da sauransu).


⚫ BALA'O'I GUDA BIYAR ACIKIN QABARINSU :

1. Rashin Kyawun Qarko, ko kuma rashin cikawa da Imani (idan ba suyi sa'a sun tuba ba).

2. Tsananin Matsi da duhun Qabari. (saboda rashin kulawarsu da ibada tun aduniya).

3. Rashin samun kyakyawar addu'a daga bayin Allah. (Allah ba zai sanya tausayinsu azukatan al'ummah ba, balle su tunasu, suyi musu addu'a).

4. Za'a nuna musu mummunan mazauninsu acikin Jahannama,  tare da sauran Mazinata.

5. Ci gaba da samun Qaruwar zunubai akansu saboda alhakin 'ya'yan mutane wadanda sukayi lalata dasu, suka gurbata musu rayuwa.


⚫ BALA'O'I GUDA BIYAR ARANAR ALQIYAMAH:

1. Za'a tashesu acikin Qungiyar Manyan Mazinata, akarkashin tutarsu. (SUBHANALLAH).

2. Mummunan ruwa mai Mugun doyi zai rika fita daga cikin al'aurorinsu.

3. Mummunan Hisabi da wulakantuwa agaban dukkan halittun Allah, Mala'iku zasuyi shelar cewa KUN GA WANNAN MAZINACI NE!! (KO KUMA KUN GA WANNAN MAZINACIYA CE!! ).

4. Za'a sanyasu acikin Kwazazzabon Jahannama,  kuma kunamai da macizai zasu rika cizonsu. Ga kuma tsananin bugu daga Mala'ikun Azaba.

5. Allah ba zai dubesu da rahamarsa ba..

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!!!

ZAUREN FIQHU ya rairayo wannan ne daga ingantattun hadisai acikin Littafin AHWALUL QUBOOR na Ibnul Jawzee da Kuma KITABUL KABA'IR na Zahabiy.

Wannan tunatarwa ce. duk wanda yaga dama ya dauki hanyar tuba zuwa ga Ubangijinsa. Allah mai gafara ne, kuma mai karbar tuba ne.

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (07-11-2014).
Share:

IDANUWAN MANZON ALLAH (SAWW) Zauren fiqhu

IDANUWAN MANZON ALLAH (SAWW)
**************************************
Wadannan idanuwa na Manzon Allah (saww), idanuwa ne wadanda darajarsu tafi duniya da lahira da abinda ke cikinsu. Kai har alahirar ma babu abinda ya fisu daraja.

Idanuwa ne wadanda basu ta'ba sa'ba ma Allah ba. Allah ya tsarkakesu ya girmamasu,  Har ma yana yabonsu acikin Alqur'ani mai girma yana cewa:

"MA ZAAGHAL-BASARU WAMA TAGHAA".

Idanuwa ne wadanda suka kalli abinda wani ido bai ta'ba gani ba. Allah Madaukakin Sarki ya shaidar da haka inda yake cewa :

"LAQAD RO'AA MIN AAYATI ROBBIHIL KUBRAA".

"HAKIKA YA GANI DAGA MANYAN AYOYIN UBANGIJINSA".

Kuma akwai hadisai da dama wadanda acikinsu Manzon Allah (saww) yake bamu labarin wasu daga cikin abubuwan da ya gani da wannan idanuwan, wadanda babu wani mahalukin da ya ta'ba gani in banda SHI (SAWW).

SIFFAR IDANUNSA DA GASHIN GIRARSA(SAWW) :
**************************
MASU SIFFANTA SHI (SAWW) irinsu Ameerul-Mu'umineen Sayyiduna Aliy bn Aby Talib, Sayyiduna Abu Huraira, Sayyiduna Hind bn Aby Haala, Sayyidah Ummu Ma'abad Al-Khuza'iyyah (Allah ya kara musu yarda) Sunce:

"MANZON ALLAH (saww) yana da Mayalwatan Idanuwa masu tsananin kyawu. Wajen Farin, Fari Qal yake. Hakanan Qwayar idanunsa baki-Qirin take.

Sannan akwai ratsin-Jaa acikin kwayar idanun. Wanda hakan yana daga alamomin cikar Annabtarsa kamar yadda Annabawan Farko suka gayawa al'ummominsu.

Hafiz Al-Iraaqee ya ruwaito cewa Lokacin da Manzon Allah (saww) Ya hadu da Raahib dinnan alokacin da suka je fatauci tare da Maisara (bawan Nana Khadeeja ra) acikin garin Basra, Farkon shaidar da Raahib din ya fara dubawa ajikin Manzon Allah (saww) ita ce Wannan RATSIN JA na cikin idanunsa.

Daga gani sai ya tabbatar cewa WANNAN SHINE ANNABIN QARSHE (SAWW).

(aduba Sharhin Shama'il na Imamul-Manawy juzu'i na 1, shafi na 55).

Sannan yana da Mayalwacin gashin idanu. Gashin baqi ne, ko yaushe haka zaka ganshi kamar yasa tozali.
Na saman ya Tankwara izuwa sama, sannan na kasan shi kuwa ya tintsira Izuwa Qasa.

Yana da cikakken Gashin girarsa mai kyawu ga Tsawo, kuma ya lankwashe kamar baka.

saboda kwarjininsa da kyawunsa Zaka ga girarsa ta dama data haggu kamar sun hade, amma basu hadu ba. Karan Hancinsa ya dan raba tsakaninsu.

(haka Ibnul Atheer ya fada acikin Nihaya, da kuma Sheikh Yusufun-Nabahany acikin Wasa'ilul-Wusul, Shafi na 73, da kuma Mulla Aliyul-Qary acikin JAM'UL-WASA'IL Juzu'i na 1 shafi na 44.).

YA ALLAH KA QARA MANA SOYAYYAR NAJAMUL-HUDA (SAWW).

Idan an ta'ba Allah yakan yi fushi (saww) sai kaga wata jijiya ta fito atsakanin girarsa (saww).

TOZALINSA MAI ALBARKA (SAWW)
************************************
Sanya tozali yana daga cikin Sunnoninsa (saww). Domin ko sanda aka haife shi (saww), yazo Idanunsa radau da tozali.

Sayyiduna Abdullahi bn  Abbas ya ruwaito cewar Manzon Allah (saww) ya kasance yana shafa tozalin Ithmud acikin Idanunsa kullum da daddare kafin ya kwanta, Sau Uku a idon dama sannan sau uku a idon haggu.

Har ma yana cewa "Kuyi tozali da Ithmud. Domin yana Qara Qarfin idanu, kuma yana tsirar da gashi".

(aduba Sunanut-Tirmidhy, Hadisi na 1757, da Kuma Mustadrak na Imamul-Hakim Hadisi na 8249).

QARFIN IDANUNSA (SAWW)
****************************
MANZON ALLAH (AS) Ya kasance yana gani acikin duhu kamar yadda yake gani acikin haske. Sannan yana ganin abinda ke nesa kamar yadda yake ganin na Kusa.

Idan ya kalli gabas yana iya ganin Mahudar rana, hakanan idan ya kalli yamma yana iya ganin mafadar rana.Kuma Yana iya shaida matafiyin dake nesa tun kafin afara ganin Qurarsa.

An ruwaito cewar Manzon Allah (saww) yana iya Qirga taurari 11 acikin Taurarin nan mafiya nisa na Surayyah.

Mala'ika Jibreelu yakan nado masa Doron Qasar nan gaba dayanta ya, ajiye masa agabansa ya kalli kowanne sashe.

In banda SHI (SAWW) babu wani Annabin da ya ta'ba ganin Mala'ika JIBREELU (AS) abisa Surar da Allah ya halicce shi da ita. Kuma da wannan idanuwan ya kalleshi.

Wannan Idanun nasa masu albarka, dasu ne yaje yaga Aljannah da ni'imomin da suke cikinta, Sannan yaga wuta da Ukubobin da suke cikinta.

Wadannan idanun na Manzon Allah (saww) dasu ne yayi kallo izuwa AJA'IBU (ABUBUWAN MAMAKI) NA MALAKUTUN UBANGIJINSA acikin daren da akayi Isra'i da Mi'iraji dashi (saww).

Yaga dukkan Annabawan Allah (as). Yaga Al'arshu da Kursiyyu da Lauhu da Qalamu da Haudhu da Raf-rafu. Kuma yaga Kogunan haske, Sannan ya ratsa Miliyoyin hijabai duk da wannan idanun.

Yaga Baitul-Ma'amur yaga Mala'iku nau'i-nau'i. Yaga Raf-Rafu da Farshu, har sanda yaga UBANGIJINSA (SWT) alokacin da sukayi Munajati awajen da Ubangijin nasa yaso.

Akwai sa'bani atsakanin Malaman Farko har zuwa yanzu game da maganar Shin Annabi (saww) yaga Allah ne ko bai ganshi ba?.

Nana A'ishah (ra) tace bai ganshi ba. Amma Sayyiduna Abdullahi bn Abbas (Malamin al'ummah) yayin da aka tambayeshi yace : "YA GANSHI! YA GANSHI! YA GANSHI! YA GANSHI! (Yayi ta maimaitawa har sai da ya shiɗe).

Anan zan Tsaya sai mun hadu acikin wani darasin da zamu gabatar a Zauren Fiqhu Whatsapp in sha Allah.

YA Allah kara salati da sallama marasa iyaka abisa Zababben Zababbu (saww).

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (Asalin rubutun na yishi ne aranar 09/APRIL/2013).
Share:

Zuciya tafarkin tsira:Akwai Ma'ajiyar alkhairi, sannan kuma akwai Ma'ajiyar sharri.

*ZUCIYA TAFARKIN TSIRA*
**************************
```Zuciya wata ajiyar Allah ce dake cikin jikinka wacce acikinta akayi maka Ma'ajiya guda biyu. Akwai Ma'ajiyar alkhairi, sannan kuma akwai Ma'ajiyar sharri.

Zuciya ita ce tsoka guda 'daya tal wacce lalacewarta yakan janyo maka asarar da babu fanshewa.. Kuma gyaruwarta da nagartarta zai iya janyo maka cin ribar da babu fa'duwa bayanta.

Zuciya ita ce Muhallin da Allah ke kallo acikin jikinka.. Mai yasa ba zaka gyarata ba, kamar irin yadda kake yiwa jikinka kwalliya da gyara kafin ka shiga cikin jama'a?.

Zuciya ita ce Kadara mafi tsada, Mafi daraja, mafi Soyuwa wacce zaka mallaka amatsayinka na Mumini. Idan ka mallaki Zuciyarka ka gama samun dukkan arziki.

Zuciya ita ce Hanyar tafiyarka zuwa ga Allah, Kuma kyawawan ayyukanka sune Motoci da jiragen da zaka hau kayi tafiyar.. Idan hanyarka ta zaka kyakkyawa,to lallai tafiyarka zatayi sauki koda abin hawan naka Qankani ne. Amma idan hanyarka tayi muni, to tafiyarka ba zatayi kyawu ba, koda abin hawan naka mai girma ne.

Tafiya zuwa ga Allah ba da Qafa akeyi ba.. Ana yinta ne da zuciya. Yi kokari ka tsaftace zuciyarka domin samun tafiya mai nisa, mai tsafta, mai sauri..```

_Allah Madaukakin Sarki yace :_

*"RANAR DA DUKIYA KO 'YA'YA BA ZASUYI AMFANI BA. SAI DAI WANDA YAZO MA ALLAH DA LAFIYAYYAR ZUCIYA".*

_Ya Allah! Ya mai juya zukata!! Ka tabbatar da zukatanmu akan addininka._

*DAGA ZAUREN FIQHU (17-02-1439 06-11-2017).*


Share:

Sunday, 12 November 2017

Audio:-Huduba:Lokacin sanyi da hukunce-hukuncen sa??

*HUDUBA HUDUBA :

Mai taken:-

LOKACIN SANYI DA HUKUNCE-HUKUNCEN SHI

Daga:-

IMAM:
*MALAM ANAS ASSALAFY FAGGE*

(DOMIN SAUKO DA WANNAN AUDIO SAIKU SHIGA WANNAN BLUE RUBUTU DAKE KASA)

DOWNLOAD AUDIO NOW


DAGA MASALLACIN JUMA'A NA :
*ABUBAKAR SIDDIQ* DAKE DAN TAMASHE, ZANGO

20/SAFAR/1439 A. H = 10/11/2017

*JIBWIS NIGERIA*

Gadukkan mai son shiga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH* sai ya yi saving wanan number +2348122248585 sannan ya tura da sunanshi da adireshinsa ta what's App. Duk abun da mutum ya turo matukar ba suna ba ne ba za a kula shi ba


Share:

Thursday, 9 November 2017

KUBUTAR MAHAIFA BA SHI NE MANUFAR IDDA BA ! ! | DR JAMILU YUSUF ZAREWA

*KUBUTAR MAHAIFA BA SHI NE MANUFAR IDDA BA ! !*

*Tambaya*

Assalamu alaikum mal dan Allah ga tambaya nan
Nice nai aure na ya rabu da mijina, wato ya bani takardan saki, kafin ya bani wannan takardar,mun samu matsala na bar gidanshi tsawon shekara daya da wata tara,kuma Daman tsawon zaman mu tare shekara bakwai ban taba samun ciki ba,yaya iddata zata kasance ?

*Amsa*
Wa alaikum assalam, Za ta jira tsarki uku, tun da sun taba kawanciyar aure kamar yadda aya ta 228 a Suratul Bakara  ta tabbatar da hakan.
                                                               Hukunce-hukuncen Saki suna farawa ne daga lokacin da aka yi saki, ba daga sanda aka samu hatsaniya ba.                          Allah ya shar'anta idda saboda manufofi da yawa daga ciki akwai: bawa miji damar kome Idan saki daya ne ko biyu, ta yiwu wani daga cikin ma'aurata ya yi nadama, Tare da cewa babban makasudin shi ne tabbatar da kubutar mahaifa, Amma ba shi kadai ba ne.
Allah ne mafi sani

*Amsawa*
*DR Jamilu Yusuf Zarewa*
25/11/2016
Share:

Jinazah Ba Guri Ba Ne Na Gabatar DaHuduba Ko Yi Wa Jama'a Wa'azi Har Kullum :Dr Ibrahim Jalo Jalingo

1. Sunnah ce lokaci zuwa lokaci a sami wani wanda zai fadakar da wadanda suka halarci binne mamaci, amma ba zai dace da Sunnah ba a maida wa'azin tamkar wata lacca, ko a riki yin wa'azin a matsayin wani al'amari raatibi wanda sai an yi shi cikin ko wace jinazah.

2. Akwai hadithai biyu da suka tabbatar da cewa har sau biyu ne Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya yi wa Sahabbai jawabai na wa'azi -ba bisa siffar huduba ba- a inda ake binne wani mamaci. Hadithin farko shi ne wanda Aliyyu Bin Abi Dalib ya ruwaito kamar yadda ya zo cikin Sahihul Bukhariy Hadithi na 1362, da Sahihi Muslim Hadithi na 2647. Hadithi na biyu shi ne wanda Baraa Bin A'azib ya ruwaito kamar yadda ya zo cikin Musnad Ahmad Hadithi na 18534.

3. Kyamatar maida gurin binne mamata wurin yin jawabai masu kama da lacca, da kuma maida hakan al'amari raatibi da ake maimaitawa a duk lokacin da aka zo binne wani mamaci tabbas shi ne yake dacewa da abinda Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya zo da shi, shi ne kuma fahimtar da yawa daga cikin Malamanmu na Sunnah; kamar Sheikh Muhammad Bin Salihil Uthaimeen da wasunsa.
Allah Ya taimake mu Ya dora mu a kan yin daidai har kullum. Ameen.
Share:

Wednesday, 8 November 2017

Maganar Annabi Ta Yi Hannun Riga Da Maganar 'Yan Shi'ah Game Da Aisha Dr Ibrahim Jalo Jalingo


Maganar Manzon Allah mai tsira da amincin Allah game da Matarsa Nana A'isha Allah Ya kara mata yarda ta yi hannun riga da maganar 'yan Shi'ah masu muzanta ta da cin mutuncinta; wannan shi ne ya sa a lokacin da su batattun 'yan Shi'ah suke kafirta ta, suke la'antar ta, a lokacin ne kuma ita Shari'ar Musulunci ta bakin da ba ya karya watau Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ke siffanta ta da cewa ita Ahlul Baiti ce!

Imamul Bukhariy ya ruwaito Hadithi na 2637, da Imamu Muslim hadithin na 2770, da Imam Ahmad Hadithi na 25,664, da Imamul Baihaqiy Hadithi na 20,386 cewa: A lokacin da Jama'ar da  suka yi wa Nana A'isha kazafi da sharrin cewa ta yi zina, sai Manzon Allah mai tsira da amincin Allah:-
((فدعا عليا واسامة حين استلبث الوحي يستامرهما في فراق أهله، فاما اسامة فقال: اهلك ولا نعلم الا خيرا. وقالت بريرة: ان رأيت عليها أمرا اغمصه اكثر من انها جارية حديثة السن تنام عن عجين اَهلها فتاتي الداجن فتأكله. فقال رسول الله صلى الله عليه وسلم: من يعذرنا من رجل بلغني أذاه في اهل بيتي! فوالله ما علمت من اهلي الا خيرا، ولقد ذكروا رجلا ماعلمت عليه الا خيرا)).
Ma'ana: ((Ya kira Aliyyu da Usamah a lokacin da Wahayi ya yi jinkiin zuwa yana mai neman shawararsu game da rabuwa da iyalinsa; amma shi Usamah sai ya ce: iyalinka ce ita, kuma ba mu san wani abu ba in banda alheri. Bareerah kuwa sai ta ce: babu wani abu na nakasa da nake gani tare da ita in banda kasancewarta wata yarinya mai karancin shekaru wacce take barci ta bar kullun garin gurasa har awakin gida su rika zuwa suna cin sa. Sai Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce: Wane ne zai gamsar da mu har mu karbi uzurin mutumin nan da labarin cutarwarsa ga Ahlu baitina ya zo mini! Wallahi ni ban san wani abu ba game da iyalina in banda alheri. Tabbas sun ambaci wani mutum ni dai babu abin da na sani game shi in ba alheri)).

Allah Ya taimake mu har kullum. Ameen.

Share:

SANYA HAKORIN MAKKA A MA'AUNIN SHARIA?? Dr.jamilu yusuf zarewa

*SANYA HAKORIN MAKKA A MA'AUNIN SHARIA ?*


*Tambaya*


Assalamu Alaikum Dr, dafatar ka tashi lafiya
Alagafarta malam ina neman karin bayani game da Hauren makka da alhazzai suke sakawa akan cewa shima yana haddasa lum'a a lokacin da mutum ya zo kuskurar baki ruwa ba za su taba ainihin Hauren da Allah ya halicci mutum da shi ba?


*Amsa*
Wa alaikum assalam,

a zahiri sanya Haure bayan aikin hajji ba matsala ba ne ta fuskar Lam'a tun da kurkure baki sunna ne a wajan da yawa daga  malamai, wannan yasa rashin shafar ruwan ga hakori daya ba zai yi tasiri ba.

Amma zai iya zama matsala saboda yana iya janyo riya, tun da galibi wanda zai sanya yana yi ne saboda yaje hajji ko dan ace masa Alhaji, hakan ya sa barinsa shi ne ya fi.

Idan ya kasance an yi hauren ne da zinare to haramun ne namiji ya sanya saboda Annabi S.A.W. ya ce: (An haramta zinare ga mazajen Al'umata, amma an halatta ga matayansu)

Allah ne mafi sani.

*Dr, Jamilu Zarewa*

1/11/2017

Ga dukkan mai son shiga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH* sai ya yi saving wannan number +2348122248585  sannan ya tura da sunansa da adireshinsa ta whatApp. Duk abun da mutum ya turo matukar ba suna ba ne ba za a kula shi ba.
Share:

Tuesday, 7 November 2017

Yaduwar bin bokaye!!?

```YADUWAR BIN BOKAYE```
~~~~~~~~~~~~~~~~


_Godiya ta tabbata ga Allah, kuma tsira da amincin Allah su tabbata ga manzon Allah da mutanen gidansa, da sahabbansa da duk wanda ya bi tafarkinsa._
.
.
_Bayan haka wani abun takaici dake faruwa shine yadda zaka ga da yawa daga cikin matayen arewacin Nigeria sun jefa kansu a cikin mummunar hallaka ta sanadiyyar bakin kishi akan kishiya. Wasu mata saboda tsabar bin bokaye da 'yan duba da 'yan bori har su kansu ma sun zama matsafa qarfi da yaji, wasu kuma sun zama mazinata, suna zuwa suna zina da bokaye domin samun biyan miyagun bukatunsu._

_Akwai wasu Qawaye masu bin bokaye da faɗa ya tashi a tsakaninsu, suna yiwa juna gori sai wata tace ma ɗayar, ai yaron da kike goye dashi kema kin san ba ɗan mijinki ba ne, ɗan gidan boka wane ne. Haka dai suka rika tona ma juna asiri._

_Wasu kuma sun talauce su lalace, duk abun hannunsu ya qare saboda bin bokaye, wasu kuma addinin na su da imaninsu ma duk sun lalata, sun fi imani da maganar bokaye fiye da maganar Ubangijin su._

_Amma sai naga mafi yawan masu tofa albarkacin sunfi alaqanta abun da jahilci, ko duhun kai, alhali kuma gaskiya abun ba haka bane_

_A yanzu zaka tarar da mafiya yawan masu bin bokaye din nan, mataye ne wayayyu, 'yan boko masu aji, waɗanda ake ganin kamar kansu yaji gishiri. Kuma zaka tarar mafiya yawansu suna zuwa Islamiyyan ballantana ace basu san haramcin abun bane._

_Kuma matsalar tafi aukuwa a tsananin matayen Attajirai, 'yan siyasa da masu mulki, da sauran masu hannu da shuni. Amma yawancin matan talakawa suna fama da abin da zasu ci, koda suna son bin bokaye basu da bayarwa._

_Irin wannan harkar ta bokanci da tsafe-tsafe ta shigo har cikin kafofin sadarwa na yanar gizo wato (social media) kamar su whatsapp da Facebook. Yanzu haka akwai groups da pages da suke tallata wani abu wai shi *(Goron Tula)* wai wani abu ne wanda idan mace tayi amfani da shi, mijinta zai rikice wajen kaunarta har sai ya rabu da dukkan matansa, wai har kyautuka zai rika yi mata don dolensa!.._

_Dasu turaren jan hankali maza, da na korar kishiya da dai sauran su. Kuma matan dake wannan Sana'a r kullum sai kara yawa sukayi, kuma basu 6oye ma kowa abin da sukayi.._

_Abinda muke so mata su gane shine: bokanci ko harka da boka, ko amfani da kayan bokanci, duk haramun ne, kum hukuncin masu yinsa shine kafirci._

_Idan kikaje wajen boka kuma kika gaskatashi kin kafirce kenan, kuma ba zaki gane cewa ke kafira bace sai lokacin mutuwarki (sanda bubu lokacin tuba)_.

_Idan kika je lahira babu imani, to fa babu wata alfarmar da zaki samu a wajen Allah. Babu ceto gare ki, babu fita daga wuta, babu shiga Aljannah, babu shan ruwan Alkausara._

_kuma maganin mallakar miji ba zai mallaka miki tsarkakakkiyar soyayyarsa ba, kuma ba zai janyo miki samun soyayyar Allah ba, balle cikawa da imani._

_Duk wulakanci ko bambancin da kike gani agidan mijinki, to kiyi hakuri kiyi addu'a shine mafita, Allah ne yake juya al'amura ba boka ko malamin duba ba._

_Imaninki shine babban jarinki Aduniya da lahira, idan kika rasashi kin afka cikin talaucin da ba zaki sake yin arziki ba. Har abada. Allah ya tsare mana imaninmu._
=
=
Allah Ta'ala yasa mudace.
=
=
```DAN UWANKU HAR KULLUM ```:
IBrahim Abubakar Hamza




Share:

Audio:-Hakkin mata akan mazajensu - Dr.Abdullahi Usman g/kaya





HAKKIN MATA AKAN MAZAJENSU



Tare da:-

DR ABDALLAH USMAN G/KAYA


DOMIN SAUKO DA WANNAN AUDIO SAIKU SHIGA WANNAN BLUE RUBUTU DAKE KASA.


Ayi saurare lafiya.
Share:

Audio:-Adaidaita sahu 1-4 by Sheikh Muhammad adam albani Zaria (Rahimahullah)

MUHADARA MUHADARA

Mau taken:-
ADAIDAITA SAHU

Daga:-
Sheikh Muhammad adam albani Zaria (Rahimahullah)

DOMIN SAUKO DA WANNAN AUDIO SAIKU SHIGA WANNAN BLUE RUBUTU DAKE KASA.

001 Adaidaita sahu

Download now

002 Adaidaita sahu

Download now

003 Adaidaita sahu

Download now

004 Adaidaita sahu

Download now

Ayi saurare lafiya

Kucigaba da kasancewa da wannan shafin.
Share:

Menene Hukuncin lika Ayatul Kursiyyu Abango da Nufin neman kariya?

*Tambaya ta (219)*

*Menene Hukuncin lika Ayatul Kursiyyu Abango da Nufin neman kariya?*

الحمد لله واحد القهار.

*AMSA:*Lika Ayatul kursiyyu ko qananun alluna ajikin gida ko mota ko shago, ko makaranta ko wajan kasuwa, akwai barna mai yawa acikin hakan, bisa Abunda shari'a ta hana.

@ - Mafi Rinjaye Ana likawa ne dan Ado da gayu, wanda bango ana sanya masa launuka na fenti hakan saiya zama sababi na wulaqanta Alqur'ani.
Wannan yana daka cikin juyar da Alqur'ani daka manufar saukar dashi, daka shiriya da wa'azi kyakkyawa dakuma Ibada da tilawarsa dasauransu..

Alqur'ani Ba'a Saukar dashi danyiwa bango Ado dashi ba, an Saukar dashi dan shiriya ga Mutane, dakuma Bayani.

2- Wasu Suna likawa ne dan Neman tabarruki, Wannan Bidi'ane Tabarruki Mai kyau shine bauta da karanta Alqur'anin, Bawai likashi ajikin bango ko juyashi zuwa jikin Alluna masu Ado ba.

Sannan Yin hakan yasabawa Abunda Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yake akai, da khalifofinsa shiryayyu Allah yakara yarda dasu, dukkan Alkhairi yana cikin binsu, bawai wajan Saba musu ba,

Tarihi yanuna wannan dabi'a taliqa karamin Allo mai dauke da ayatul kursiyyu ko wani Bangare na Alqur'ani ajikin gida ko mota ko kasuwa, ba'a fara yinsa ba sai bayan shudewar  Nagartattun Musulmi sai lokacinda Musulmai suka zama masu rauni a'aqida da ilmi dariko da Addininsu.

Haka nan Lika irin wannan alluna dauke da Alqur'ani hanyace dazatakai Mutum ga shirka, domin Wasu suna qudurta cewa wadannan kananun Alluna da'ake likawa akasuwa ko mota ko gida kariyane ga gidan ko motar daka Wani Sharri, qudurce wannan kuma Shirkane.

Mai bada kariya na Hakika shine Allah, daka cikin dalilan da zaisa kuma yabawa Mutum kariya shine tilawar Alqur'ani ka yin zikirori wadanda Sukazo acikin hadisai Ingantattu, bawai likashi abangon gida ko mota ba.

Adunqule dai bai halatta rubuta ayar Alqur'ani abangon gida ko sanya karamin Allo ajikin mota ko shago ba, koda abangon masallacine bai halatta ba, bidi'ane.

Sanyawa kuma tareda qudurce bayar da wata kariya ga Mutum wannan kam Shirkane.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك نشهد أن لا إله إلا أنت نستغفرك ونتوب إليك.

🖊 *Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai*
*+2347033406106.*
*+2348140925493.*
Share:

Menene hukuncin mutumin da yake take wandonsa, shin ya halatta a bi shi salla?

*TAMBAYA DA AMSA DAGA SHEIKH MUHAMMAD BELLO AHMAD AL-ADAMAWIY, RAHIMAHULLAH*

*001*

*TAMBAYA*
Assalamu alaikum, Mene ne hukuncin mutumin da yake take wandonsa, shin ya halatta a bi shi salla?

*AMSA*
Take wanda a Musulunci haramun ne domin hadisai masu yawa sun zo suna hani akan haka, kuma ba lallai sai wando ba.

Manzon Allah, sallallahu 'alaihi wa sallama, ya ce:

 *"مَا أَسْفَلَ مِنْ الْكَعْبَيْنِ مِنْ الْإِزَارِ فَفِي النَّارِ"* رواه البخاري (5787).

Duk abun da ya wuce idon sawu (na tufafi), to yana wuta. Bukhari ne ya ruwaito hadisi na 5787.

Malamai suka ce tun da har Allah Ta'ala Ya yi barazana da wuta, to wannan ya nuna babban laifi ne.

Dangane da batun bin shi salla matukar babu najasa a jikin tufan shi za a bi shi salla, domin laifin mai laifi bai hana a karɓa sallansa matukar ya yi ta yanda shari'a ta koyar kamar yadda Abdullahi Bn Umar ya yi salla a bayan Hajjaj Bn Yusuf al-Thaqafee.

Wallahu A'alam.

✍🏼Tattarawa:
*_Umar Shehu Zaria_*
Share:

Sunday, 5 November 2017

JAN HANKALI:- Idan kana aikata abubuwa 3 imaninka zai karu

JAN HANKALI

IDAN KANA AIKATA ABUBUWA UKU IMANINKA ZAI KARU:

1- Tilawal Al-Qur'ani.
2- Kiyamul-laili.
3- Azkhar.

ZAKA FUSKANCI MATSALA A KABARINKA IDAN KA MUTU DA ABU UKU:

1- Hakkin Wani
2- Dabi'ar Annamimanci
3- Hassada

ABUBUWA UKU SUNA KAUDA FUSHIN ALLAH AKAN BAWANSA:

1- Istigfari.
2- Tausayawa waninka
3- Sadaka

IDAN ALLAH YA BAKA ABU UKU TO KA GODEWA ALLAH:

1- Lafiya
2- Wadata
3- Basira

KADA KA YARDA KA AURI MACE MAI DABI'O'I GUDA UKU:

1- Mai yawan fushi.
2- Maras sirri
3- Marar tsafta (Kazamiya)

KA YI KOKARI KA GINA RAYUWARKA AKAN ABU UKU:

1- Son Allah da Manzonsa.
2- Gaskiya da Rikon Amana.
3- Hakuri da Jarrabawa a Rayuwa

ABUBUWA UKU KA ROKI ALLAH (S.W.T) YA TSARE KA DA AIKATA SU:

1- Yanke Zumunta.
2- Zagin Sahabbai.
3- Mutuwa da hakkin wani

MUTANE UKU KADA KA SAURARI MAGANARSU:

1- Makaryaci
2- Magulmaci
3- Malami mai kwadayi da son zuciya

MUTUM UKU KADA KA YARDA SU DINGA KUSANTARKA:
1- Munafiki
2- Mazinaci
3- Maras kunya

ABUBUWA UKU BA A SON JINKIRTA SU IDAN LOKACIN SU YA ZO:

1- Sallah
2- Aure
3- Jana'iza

ABUBUWA UKU RIKO DA SU YANA SAMAR DA RABO A LAHIRA:

1- Kokarin ibada
2- Kula da Nafila
3- Amfani da Halal a Rayuwa

ABUBUWA UKU SUNA HANA MUTUM TANADIN LAHIRA:

1- Dogon Buri.
2- Rashin karanta Alkur'ani
3- Nisantar sauraron Wa'azi.

MUTANE UKU SUNA SAMUN TAIMAKON ALLAH:

1- Mutumin da yake Neman aure Don ya kare mutuncin kansa
2- Mutumin da ya tafi jihadi, Domin daukaka kalmar Allah.
3- Bawa wanda aka dora masa fansar kansa.

ABUBUWA UKU NASA ZUCIYA TA GURBACE:
1- Rashin yarda da kaddara.
2- Aibata bayin Allah na kwarai
3- Wulakanta Iyaye

Ya Allah ka tsare mu daga sharrin Shaidan, ka shiryar da mu kan hanya madaidaiciya, amin.
MATA 10 WAINDA ALLAH YA
TSINE MUSU: -
ﺍﻟﻮﺍﺷﻤﺎﺕ
ﻭﺍﻟﻤﺴﺘﻮﺷﻤﺎﺕ
1. Mata masu
tsaga
fuskokinsu. -
ﺍﻟﻨﺎﻣﺼﺎﺕ
ﻭﺍﻟﻤﺘﻨﺼﻤﺎﺕ
2. Mata masu
aske gashin
gira. -
ﺍﻟﻤﺘﻔﻠﺠﺎﺕ
3. Mata masu
kankare hakori
(wushirya). -
ﺍﻟﻮﺍﺻﻠﺔ
ﻭﺍﻟﻤﺴﺘﻮﺻﻠﺔ
4. Mai 'karin
gashi da wadda
ake karamata
gashin. -
ﺍﻟﺘﻲ ﺳﺨﻂ ﻋﻠﻴﻬﺎ
ﺯﻭﺟﻬﺎ
5.Matar da
mijinta yayi
fushi da ita. -
ﺍﻟﻤﺘﺸﺒﻬﺎﺕ ﺑﺎﻟﺮﺟﺎﻝ
6. Mata masu
shigar maza. -
ﺯﻭﺍﺭﺍﺕ ﺍﻟﻘﺒﻮﺭ
7. Mata masu
yawan
ziyartar
kabur-bura
(makabarta).
- ﺍﻟﻨﺎﺋﺤﺎﺕ
8. Mata masu
kururuwa akan
mamaci. -
ﺍﻟﻤﺤﻠﻞ ﻟﻪ
9. Mata masu
auren kashe
wuta. -
ﻛﺎﺳﻴﺎﺕ ﻋﺎﺭﻳﺎﺕ
ﻣﺘﺒﺮﺟﺎﺕ
10. Mata masu
bayyana
tsiraicinsu.
Kada ku manta TSINUWA itace
nisanta daga
rahamar Allah!
ﻗﺎﻝ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : " ﻳﺎ
ﻣﻌﺸﺮ ﺍﻟﻨﺴﺎﺀ
ﺗﺼﺪﻗﻦﻭﺃﻛﺜﺮﻥ ﻣﻦ
ﺍﻹﺳﺘﻐﻔﺎﺭﻓﺈﻧﻲ
ﺭﺃﻳﺘﻜﻦ ﺃﻛﺜﺮ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﻨﺎﺭ " ﺭﻭﺍﻩ ﻣﺴﻠﻢ
Manzon Allah (SAW)
ya ce: 'Yaku
taron mata! ku
yi sadaqa,
kuma ku yawaita neman
gafara.
(Istigfari)
domin lallai
ninagan ku
mafiya yawanku
'yanwuta
ne."Allah yakaremu. Send it to ur family n frndx

Assalamu alaikum. Manzon Allah (S.A.W) yace:kuyi kokarin danne abubuwa uku:

(1) fushi (2) Sha'awa (3) Maganganunku.

Ku himmatu danyin abubuwa 2:
(1) Ayyukan Alkhairi (2) Abokai nagari.

Kuci moriyar abubuwa 2:
(1) Lokaci (2) Karfi.

Ku nemi abubuwa 3:
(1) Gafaran Allah (2) ilmi (3) Hikima.

YA ALLAH KABAMU IKON KIYAYEWA.

Ba'a gajiya da aikin alkhairi. Daure turawa 'yan uwa musulmi domin samun lada.

Share:

Saturday, 4 November 2017

AKWAI GADO GA DAN DA MACE TA SHAYAR DA IYAYEN SHI ?

*_AKWAI GADO GA DAN DA MACE TA SHAYAR DA IYAYEN SHI ?_*


*_Tambaya_*

Assalamu alaikum malamaina don Allah ga wata tambaya kamar haka : idan aka haifi yaro sai daga baya aka samu cewa da babanshi da mamarshi duk mace guda ta shayar dasu to wai wannan yaron yana da gadansu koko?


*_Amsa_*
Wa'alaykumussalam.

 A na gado da takaba a auren da a ka gano rashin ingancinsa, kuma a na danganta yaro ga mahaifinsa. [AL-MUGNY; 8/590]

Wallahu A'alam.

*_MALAM: NURUDDEEN MUHAMMAD (MUJAHEED)_*

25/10/2017

Ga dukkan mai son shiga *ZAUREN FIQHUS SUNNAH* sai ya yi saving wannan number +2348122248585  sannan ya tura da sunansa da adireshinsa ta whatApp. Duk abun da mutum ya turo matukar ba suna ba ne ba za a kula shi ba.

Share:

Friday, 3 November 2017

FALALAR KARANTA WASU SURORI LOKACIN KWANCIYA BARCI?!

*FALALAR KARANTA WASU SURORI LOKACIN KWANCIYA BARCI*


*1-Karanta AYATUL KURSIYYU*

Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Idan kazo kwanciya a shimfidarka to ka karanta AYATUL KURSIYYU,Wato*
*﴿اللّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ﴾ bazaka gushe ba kana tare da mai kariya daga Allah,Kuma shaidan bazai kusance ka ba har sai ka wayi gari)*
@صحيح البخاري-رقم (3275).

*2-Karanta QUL YÃ AYYUHAL KAFITUN*

Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Idan kazo kwanciya shimfidarka acikin dare,to ka karanta QUL YA AYYUHAL KAFIRUN,"قُلْ يَا أيُّهَا الْكَافِرُونَ"sannan sai ka kwanta barci alokacin da ka gama karantata,Domin ita kubutace daga Shirka)*
@حسنه الألباني في صحيح الجامع -رقم :(292).


*3-Karanta QUL HUWALLAHU da FALAQI da NASI*

Daga Nana A'isha رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا,tana cewa,Manzon Allah ﷺ ya kasance,idan yazo kwanciya a shimfidarsa a kowane dare,yana hada tafikan hannuwansa,Sannan sai yayi tofi acikinsu,
sai ya karanta,QULHUWA FALAQI da NASI)*
﴿قُلْ هُوَ اللَّهُ أَحَدٌ﴾وَ﴿قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ﴾وَ﴿ قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ النَّاسِ ﴾،
*Sannan sai ya shafi abinda ya sauwaqa daga jikinasa,yana farawane daga shafar kai,da abinda yayi saura na jikinsa,yana yin haka har sau ukku)*
@صحيح البخاري-رقم : (5017)


*4-Karanta suratul ISRA'I da ZUMAR*

Daga Nana A'isha رَضِيَ اللَّهُ عَنْهَا,tace,Manzon Allah ﷺ ya kasance baya kwanciya barci har sai ya karanta *SURATUL ISRA'I da SURATUL ZUMAR*.
@صححه الألباني في صحيح الترمذي -رقم:(2920)

*5-Karanta Suratul MULK wato TABARA*


 Manzon Allah ﷺ yana cewa;-
*(Lallai akwai wata Sura ta Alqurani mai ayoyi guda Talatin,tana neman ceton bawa har sai an gafarta masa,itace Suratul TABARA.....)*

Daga Abdillahi bn Mas'ud R.A yana cewa;-
"Wanda ya karanta Suratul TABARA
{تباركَ الذي بيدِه الملكُ}
A kowane dare,Allah zai kare shi da ita daga Azabar Qabari,Mun kasance a lokacin Manzon Allah ﷺ muna kiranra mai tseratarwa.....".
@صحيح الترغيب 1475 صحيح ابن ماجه 3068 صحيح الترمذي 2891 صحيح أبي داود 1400 الألباني

Manzon Allah ﷺ ya kasance yana karanta Suratul TABARA  da Suratul
SAJADA,akowane dare"
@صحيح الجامع  ٤/٢٥٥ الألباني
*6-Karanta Ayoyi guda biyu na karshen Suratul BAQARA*

Manzon Allah ﷺ yana cewa;-

*(Dukkan wanda ya karanta ayoyi guda biyu na karshen suratul BAQARA a kowane dare ta isar masa)*
@البخاري مع الفتح، ٩/ ٩٤، برقم ٤٠٠٨، ومسلم،١/ ٥٥٤، برقم ٨٠٧، والآيتان من سورة البقرة، ٢٨٥-٢٨٦.

*﴿آمَنَ الرَّسُولُ بِمَا أُنْزِلَ إِلَيْهِ مِنْ رَبِّهِ وَالْمُؤْمِنُونَ كُلٌّ آمَنَ بِاللَّهِ وَمَلائِكَتِهِ وَكُتُبِهِ وَرُسُلِهِ لا نُفَرِّقُ بَيْنَ أَحَدٍ مِنْ رُسُلِهِ وَقَالُوا سَمِعْنَا وَأَطَعْنَا غُفْرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيْكَ الْمَصِيرُ*

*لا يُكَلِّفُ اللَّهُ نَفْسًا إِلا وُسْعَهَا لَهَا مَا كَسَبَتْ وَعَلَيْهَا مَا اكْتَسَبَتْ رَبَّنَا لا تُؤَاخِذْنَا إِنْ نَسِينَا أَوْ أَخْطَأْنَا رَبَّنَا وَلا تَحْمِلْ عَلَيْنَا إِصْرًا كَمَا حَمَلْتَهُ عَلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِنَا رَبَّنَا وَلا تُحَمِّلْنَا مَا لا طَاقَةَ لَنَا بِهِ وَاعْفُ عَنَّا وَاغْفِرْ لَنَا وَارْحَمْنَا أَنْتَ مَوْلانَا فَانْصُرْنَا عَلَى الْقَوْمِ الْكَافِرِينَ﴾*.


Allah ne mafi sani



*Allah ka bamu ikon da Manzon Allah ﷺ a dukkan rayuwa baki daya*.
Share:

MENENE HUKUNCIN WANDA YAYI SALLAH ALHALI YASAN YANA CIKIN JANABA??

*MENENE HUKUNCIN WANDA YAYI SALLAH ALHALI YASAN YANA CIKIN JANABA??*

الحمد لله رب العالمين.

Amsa: Abune sananne awajan musulmi cewa tsarkin  hadasi babba ko karami, wajibine, kuma sharadine na ingancin sallah, duk wanda yai sallah bashi da tsarki da gangan koda mantuwa sallarsa batacciyace bataiba, saiya sake, idan daganganci yayi hakika ya aikata babban laifi cikin manyan laifuka dakuma zunubi mai girma.

Shaikul islam ibnu taimiyyah rahimahullah yace:

"Musulmi kada yayi sallah a inda ba alkibla bane, kada yayi sallah batare da alwala ko ruku'u ko sujjada ba, wanda ya aikata haka yacancanci zargi da uquba,
Min hajussunnah (5/204).

Hakika gargadi mai tsanani yazo gawanda ya aikata haka;

Hadisi daga Abdullahi dan mas'ud yardar Allah takara tabbata agareshi daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam yace: (Anyi Umarni ayiwa wani bawa daka cikin bayin Allah bulala dari acikin kabarinsa, bai gusheba yana tambayar dalilin bulalar dakuma rokon asassauta masa harsaida ya rage saura bulala daya, sai aka karasa masa dayar, aka cika kabarinsa da wuta, lokacin da'aka dauke masa azabar bayan yafarfado sai yace kusanar dani sabo dame akaimin bulala? sai akace dashi kayi sallah ne sau daya batare da tsarki ba, kawuce tawajan azzalumi kuma baka taimakeshiba) Addahawi yaruwaitoshi acikin mushkilil Ãàsaar Albani ya hassanashi acikin silsila saheeha (2774).

Malamai sunyi ittifaqi akan duk wanda yai sallah batare da tsarki ba yana mai halatta hakan, ko saboda isgili, hakika yakafirta, za'a nemi yatuba, idan bai tubaba za'a kasheshi.

Amma idan mutum yai sallah batare da alwala kawai dan wulakanta sallah, bai halatta hakan ba kuma ba izgili yakeba,  Imamu Ahmad yatafi akan cewa mutum yakafirta, jamhurdin malamai kuma sukace: bai kafirta ba, saidai abunda yayi babban laifine cikin manyan laifuka.

Imamun nawawi rahimahulla yace:

Idan mutum yasan yanada hadasi kuma yasan sallah batsarki haramunne, abunda yayi laifine babba cikin manyana laifuka, baya kafirta awajanmu, saidai idan yahalatta sallah batsarki ne, Abu hanifa yace yakafirta saboda izgilinsa.

Abunda yake wajibi akan wanda yai sallah babu tsarki shine yatuba, yayi istigfari, yakuma kuduri niyyar bazai sake aikata hakan ba, sannan saiya sake sallar daya sallata batare da alwala ba, Allah madaukakin sarki yana karbar tuban wanda yatuba yakoma gareshi.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.

Tambayoyin musukunci
Watsapp group
Share:

Thursday, 2 November 2017

Audio:- Muhimmancin Sada Zumunci A Musulunci Sheikh Jabir Sani Maihula

KHUDUBAR JUMU'A (7-2-1439AH / 27-10-2017) Daga Masallachin Sultan Muh'd Sa'ad Abubakar III dake Tanki Guiwa Lowcost Sokoto.

Mai Taken: MUHIMMANCIN SADA ZUMUNCI A MUSULUNCI

Tare da: Sheikh Jabir Sani Maihula (Hapizahullah)

Download Audio Now
Share:

Video:-Maganin Ciwon Suga Da Hawan Jini By Dr.Abdullahi Usman Umar g/kaya Kano

Zaku Saurari Da Kuma kallo Fatawa Daga  ml Abdullahi Usman Umar Dake Jahar Kano State, Zakuji Yadda Yake Bayani Game Da Magungunnah Na Gargajiya.
Wa’yanda Sunka Hada Da Magance Ciwon Suga da Hawan jini Da Saurab Makamantan Su.
Haka Kuma Zaku Karu Da Wannan Fatawa Tashi Ta Fannin Abubuwa Dake Cike Da lora A Wannan Zamani Da Muke ciki Domin Malamin Allah Ya Bashi Basira Fiye Da Tinanin Jama’a.
Sai kuyi Download Ku kallah Ku saurari Malamin.
Watch After Download:-
Share:

Video:Wacece Mijinta Yafi ( Tare Da Mata ) - Sheikh Jafar Mahamud adam (Rahimahullah)



Allah jiqan malam da rahama allaha ka tsinewa dukkan masu hannu a wajen kisan malam ya Allab ka wargaza tanadinsu allah hadasu da masifa da bala i daga duniyarsu har lahira.
ya na daya ne daga cikin mafiya
shahara da kuma fitattun
Malaman Musulunci kuma
Jagorori a kan shiriya da miliyoyin al’ummar Musulmin Najeriya –
Musamman Arewacinta –
da kuma yammacin Afirika
su ka gani a farkon karni
na 15 bayan Hijrar Manzon
Allah (sallallahu ‘alaihi wa
alihi wa sallam) daga
Makkah zuwa Madina.
Ranar Juma’a 25 ga watan
Rabi’ul Awwal, 1428 A.H.
(13 April 2007, C.E.), wasu
‘yan ta’adda da kuma
bindiga dadin da har
yanzu ba a san ko su waye
ba, sun yiwa Malam Ja’afar
Kisan gilla lokacin da ya ke
jagorantar jama’a a sallar
Asuba a masallacin
Juma’arsa da ke unguwar
dorayi a birnin Kano,
Najeriya.
Hakikanin gaskiya, Malam
Ja’afar zai dade a zukatan
dukkanin Musulmi a
matsayin wata alama ta
masu riko da madarar
karantarwar addinin
Musulunci bisa
madaidaicin ra’ayi adalci
da kuma basira.
Don haka, bukatar samar
da website da sunansa ba
za ta misaltu ba. Wannan
website zai tattara tare da
yada gagaruman ayyukan
Shaikh Ja’afar ta dukkanin
hanyoyi, abun da mutane
da yawa a ko’ina cikin
kasa ke yunwar samu,
musamman saboda
Shehin malamin wata
alama ce ta malaman da
su ke kira zuwa ga akidar
Ahlus Sunnah wal Jama’ah.
Wannan website zai
taimaka wajen yada
ayyukan Shaikh Ja’afar na
alkhairi da taimakon
al’umma tare da bayar da
hadin kai don yada
kyawawan ayyuka da
ciyar da su gaba ta hanyar
tallafawa ilimi da harkokin
zamantakewa.
FATAN ZA’ACI GABA DA KASANCEWA TARE DAMU
Share:

Archive

Unordered List

Support