Zuciya tafarkin tsira:Akwai Ma'ajiyar alkhairi, sannan kuma akwai Ma'ajiyar sharri. ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Tuesday, 14 November 2017

Zuciya tafarkin tsira:Akwai Ma'ajiyar alkhairi, sannan kuma akwai Ma'ajiyar sharri.

*ZUCIYA TAFARKIN TSIRA*
**************************
```Zuciya wata ajiyar Allah ce dake cikin jikinka wacce acikinta akayi maka Ma'ajiya guda biyu. Akwai Ma'ajiyar alkhairi, sannan kuma akwai Ma'ajiyar sharri.

Zuciya ita ce tsoka guda 'daya tal wacce lalacewarta yakan janyo maka asarar da babu fanshewa.. Kuma gyaruwarta da nagartarta zai iya janyo maka cin ribar da babu fa'duwa bayanta.

Zuciya ita ce Muhallin da Allah ke kallo acikin jikinka.. Mai yasa ba zaka gyarata ba, kamar irin yadda kake yiwa jikinka kwalliya da gyara kafin ka shiga cikin jama'a?.

Zuciya ita ce Kadara mafi tsada, Mafi daraja, mafi Soyuwa wacce zaka mallaka amatsayinka na Mumini. Idan ka mallaki Zuciyarka ka gama samun dukkan arziki.

Zuciya ita ce Hanyar tafiyarka zuwa ga Allah, Kuma kyawawan ayyukanka sune Motoci da jiragen da zaka hau kayi tafiyar.. Idan hanyarka ta zaka kyakkyawa,to lallai tafiyarka zatayi sauki koda abin hawan naka Qankani ne. Amma idan hanyarka tayi muni, to tafiyarka ba zatayi kyawu ba, koda abin hawan naka mai girma ne.

Tafiya zuwa ga Allah ba da Qafa akeyi ba.. Ana yinta ne da zuciya. Yi kokari ka tsaftace zuciyarka domin samun tafiya mai nisa, mai tsafta, mai sauri..```

_Allah Madaukakin Sarki yace :_

*"RANAR DA DUKIYA KO 'YA'YA BA ZASUYI AMFANI BA. SAI DAI WANDA YAZO MA ALLAH DA LAFIYAYYAR ZUCIYA".*

_Ya Allah! Ya mai juya zukata!! Ka tabbatar da zukatanmu akan addininka._

*DAGA ZAUREN FIQHU (17-02-1439 06-11-2017).*


Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support