Shin zaka iya tsinewa azzalumin shugaba ~ Duniyarfatawa.com™

вarĸarĸυ da zυwa ĸυcι gaвa da ĸaѕancewa da wannan ѕнaғιn doмιn cιgaвa da ѕaмυn ιnganтaттυn ғaтawa a cιĸιn vιdeo/aυdιo ĸo rυвυтυ daga мalυмa daвan-daвan na aнlυѕ-ѕυnnaн мυngode

Recent Post

Thursday 20 October 2016

Shin zaka iya tsinewa azzalumin shugaba

SHIN ZAKA IYA TSINEWA AZZALUMIN SHUGABA.

الحمد لله رب العالمين ولا عدوان إلا على الظالمين، والصلاة والسلام على محمد وعلى آله وصحبه وسلم.

AMSA:La'anta tana nufin Allah yakori mutum daka rahmarsa, da nesantashi dashi, yana daka cikin la'anta zagi da cin mutunci da muguwar addu'a ga mutum.

Tsinuwa tana faruwane ta fuska biyu:
1-Mutum ya la'anci kafirai da masu sabo a dunkule, kamar mutum yace Allah yatsinewa kafirai, Allah yatsinewa mazinata, Allah yatsinewa barayi da fasikai, da azzalumai, irin wannan la'anta ta halatta, ibnu muflih yace: acikin adabul shari'a la'antar kafirai gaba daya ya halatta (1/203).

2-Tsinuwar takasance ka ayyana wani jinsi wajan la'antar taka, kamar kace Allah yatsinewa kafiri wane ko Allah yatsinewa wane ko Wane maiyin kaza Allah yatsine mar, wannan nau'i na tsinuwa shima kashi biyu ne

1-Yakasance ansamu nassi dayake nuni da la'antarsa kamar shaidan, ko kuma nassi ya tabbatar da cewa ya mutu akan kafirci, kamar fir'auna da Abu lahab, da abu jahal, la'antar wadannan ya halatta.
Ibnu muflih, yace: acikin adabul shari'a (1/214). ya halatta tsinewa kafirai wadanda nassi yatabbatar da la'antar su, babu laifi wajan kin tsine musu.

2-Tsinewa wanda nassi baizo akan la'antar saba, tahanyar ayyana shi shi kadai da sunansa kamar mai saida giya, da wanda yake la'antar iyayen sa, dawanda yake yanka ga wanin Allah, Wannan shikuma malamai sunyi sabani wajan halacci ko haramcin hakan, da maganganu guda uku.

1-Sukace bai halatta ayyana wani mai sabo ko kafiri shi kadai, ka tsinemar ba takowanne hali.
2-Sukace ya halatta akan kafiri amma banda musulmi mai sabo,
3-Sukace: yahalatta kai tsaye.
Adabul shari'a na ibnu muflih,(1/303).

Wadanda sukace ya halatta la'antar kafiri shi kadai sunkafa hujja da dalilai kamar haka.
1-Daka Abdullahi dan Umar yaji manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam idan yadago daka ruku'un sallar sa ta raka'ar karshe ta asuba yana cewa:Allah katsinewa wane da wane bayan yace Allah yaji mai gode masa, sai Allah yasaukar da yah
(ليس لك من الأمر شيء أو يتوب عليهم أو يعذبهم فإنهم ظالمون،)
Baka da wani al'amari na komi akansu, ko Allah yakarbi tubansu ko yai musu azaba lallaisu azzalumai ne, da wannan aya wasu malamai sukace bai halatta la'antar mutum shi kadai ba koda kafirine saboda da wannan aya ta sauka sai manzan Allah yadaina ambaton su daya bayan daya saidai a jam'i, saboda idan Allah yakaddara zai shiryu agaba kuma katsine mar to ka zalunceshi.

2-Daka umar wani mutum yakasance azamanin manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ana masa lakabi da "Himaar" yanasa manzan Allah dariya, Annabi yanai masa bulala idan yasa giya sai wata rana akazo dashi yasha giya za ai masa bulala,sai wani daka cikin sahabbai yace: Allah ya tsinemar saboda yawan shan giya dayake anaimar bulala, sai manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace:(kada ku la'ance shi Na rantse da Allah ba'abunda nasani akansa face yanasan Allah da manzan sa.) Bukhary(6780)

Shaikul islam ibnu taimiyyah acikin majmu'ul fatwa (6/511)
Yace: la'anta ta halatta kai tsaye ga wanda Allah damanzan sa suka la'anta, amma la'antar wani ka ayyana shi ta halatta ne kadai ga wanda ya mutu kafiri, amma la'antar fasiki maisabo ka ayyana shi bata halatta ba, saboda hanin da manzan Allah yayi na la'antar Abdullahi bin himar, duk da cewa Manzan Allah yala'anci masu shan giya da mai taimakawa wajen kasuwancin ta adunkule, tare dacewa la'antar mai sabo ka ayyanashi akwai sabanin malamai.

Shaeik uthaimeen Rahimahullah acikin qaulul mufeed (1/226) yace:

Banbaci tsakanin la'antar masu sabo adunkule dakuma la'antar wani ka ayyana shi, nafarko la'antar wani ka ayyana shi anhana, nabiyu la'antar masu sabo adunkule ya halatta, idan kaga mai taimakawa barna bazakace Allah yatsine maka mabarnaci ba, a'a sai dai kace Allah yatsinewa mabarnata, dalili akan haka shine lokacin da manzan Allah yake tsinewa wasu mushirikai acikin qunuti, yana ambatarsu da sunayensu, Allah ya hana shi hakan da fadinsa madaukakin sarki
(ليس لك من الأمر شي ء أو يتوب عليهم أو يعذبهم فإنهم ظالمون)
Baka da wani al'amari na komai akansu kodai Allah yakarbi tubansu ko kuma yai musu azaba hakika su azzalumaine. Bukhary
Wallahu A'alam.

Saboda haka la'antar shugaba koda azzalumine kuma koda fasikine haramunne ba koyarwar musulunci bace, koda kafirine matukar bai hanaku yin addinin kuba tsinemar da zaginsa dayi masa muguwar addu'a haramunne, kamar yana hanaku azumi ko sallah ko wata ibada ko yada addininku, saboda hadisai dasukai hani da hakan.

Ankarbo daka Abu umamah daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam yace: ( kada ku zagi shugabanni, ku roka musu shiriya da gyaruwa awajan Allah domin gyaruwarsu gyaruwarkuce.)

Kuma tsinuwa da aibantawa ba al'adar mutumin kirki bace wanda yakebin koyarwar Annabinsa sallallahu Alaihi wasallam, saboda hadisi ya inganta manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam yace: ba'asan musulmin kirki da tsinuwaba, ko sakin harshe yaita maganganu bakai bagindai, ko zancen banza,

Muna rokon Allah madaukakin sarki yatabbatar da dugadugnmu akan abunda yakeso kuma yayarda dashi.

Wallahu A'alamu.

سبحانك اللهم وبحمدك أشهد أن لا إله إلا أنت أستغفرك وأتوب إليك.

*TAMBAYOYIN MUSULUNCI*
*WhatsApp Group*

Share:

0 comments:

Post a Comment

Archive

Unordered List

Support