*ZATON KU ALLAH BAZAI JARABE MU BA?*
*Dr. Isa Ali Pantami*
Akwai abun da 'Dan Adam baya magancewa Kansa balle ya magance maka. Amma maimakon mu duba laifin da muke wa Allah mu gyara, sai mu ce rayuwa ta yi kunci, shugaba wane ya gagara. Eh, kana iya cewa wani lokaci an gagara. Amma ka sani, akwai laifin da mu muke yiwa Allah, matukar kuma bamu gyara ba, ko duk Arzikin Jaziratul Arab za a tara mana, ba za mu fita cikin kuncin da muke ciki ba!
Ai yanzu, kuncin rayuwar ba wai babu kudin bane. Akwai, Albarkar Allah Ya debe. In ko ba mu tuba zuwa ga Allah ba, Allah ba zai dawo da shi ba.
Babu Al'ummar da ta sabawa Allah ta ji dadi a Duniya. Babu ita!
Mutanan Annabi Lut, Luwadi kadai suka yi Allah Ya dirkake su. Ba a Luwadi a yanzu?
Mutanan Annabi Shu'aibu, tauye mudu kadai sukayi, akan wannan Allah Ya halakar da su. Ba a tauye mudu a yanzu?
Mutanan Annabi Saleh, Dabba kadai suka kashe. Akan Taguwa Allah Ya halakar da su. A yau ana kashe mutane, kuma Allah ba zai jarrabe mu ba?
Duk laifin da 'Dai - 'Dai ake wa Allah Ya halakar da mutane, yau duk mun hada muna yin su.
Babu laifin da akai wa Allah a tarihin Duniya da yanzu bama yinsu. Kuma Allah ba zai Jarrabe mu ba?
Har muna zaton Akwai 'Dan Adam da zai cire mu in bamu koma ga Allah ba? Ba za mu duba abun da muke wa Allah mu gyara ba?
A duk Al-Qur'ani, Allah bai bamu tarihin wata al'umma da take yanke jikin mutum a yi sihiri ba. Amma mu a yau muna yi. Bai bamu labarin inda Namiji ke auren Namiji ba, sai dai ace suna luwadi. Amma a yau muna yi. Har a Nigeria anyi irin wannan auren.
Wallahi, ba za mu samu mafita ba har sai mun tuba mun koma ga Allah.
Domin Allah cewa yayi: "Lallai Allah baya canza halin da mutane suke ciki, (wallahi) sai dai in sun canza dakansu." Idan muka canza, Allah zai canza mana.
Kuma ai Al-Qur'ani ya fada mana, Mutanan Fir'auna ai Annabi Musa (as) suka karyata, Allah Ya saukar musu da fari, da bushewar 'ya'yan itatuwa.
Mutanan Saba', suna cikin jin dadi ko abinci ba sa saya, amma da suka kafircewa Ni'imar Allah, sai Ya janye dukkanin falalar da Ya musu na kayan marmari a Lambu. Ya canza musu da ta 'kaya! Allah Ya sanya su cikin 'kuncin rayuwa.
Idan za mu bi dokokin Allah, babu irin Ni'imar da ba zai mana ba. 'Dan Adam baya wa mutane maganin kuncin rayuwa. Wadannan al'amura da muke ciki, na kuncin rayuwa da tawayar tattalin Arziki, suna bukatar muyi wa kanmu wa'azi ne. Mu koma zuwa ga Allah Madaukakin Sarki.
0 comments:
Post a Comment